AZIZA DA AZIMA 61-70

“Duk yadda kikayi dai-dai ne mom”
“Ka dauketa ka kaita daki! Sultana ke kuma ki zauna da ita, bari naje na sanar da cewa auren biyu ne” mom ta fada tana hawa sama, shi kuwa Nawaz ya dauki Aziza ya kwantar da ita a daki sannan ya fice yana neman layin Al’mazeen dan ya shaida masa har da shima za a daurawa aure.
A cikin ƙanƙanin lokaci mom tayi sanarwan auren Nawaz da Aziza wanda mutane sun sha mamaki, amma da shike ance ba a mamaki da ikon Allah sai kowa ya bi lamarin da fatan alkairi.
Sadda Nawaz ke gayawa Al’mazeen akan cewa zai auri Aziza ba karamin mamaki Al’mazeen ya yi ba, har yaushe Nawaz ya fara soyayya da Aziza da har ta kaisu ga maganar aure nan da sati daya? Sannan Nawaz baya son auren yarinya kamar yadda baya son auren babba sosai ,ya tabbata idan Nawaz ne zai iya cewa Aziza tayi masa yarinta, haka dai ya share maganar yana fadin shima ga shi ya kamu da son Azima,yana so ya ba wa Nawaz labarin Azima amma sai yaji kamar an riƙi bakinsa, dan haka ya share maganar gabadaya yana tambayar Nawaz dame-dame zasu shirya da bikin tunda aure yazo a bazata, nan Nawaz ke gaya masa babu wani abunda za ayi wanda ya wuce daurin aure daga shi shikenan, dan harta sultana tace babu abinda zatayi da an daura aure kawai a kaita,babu yadda khalil baiyi da ita ba ko da walima ayi nan ma tace ta yafe, ya fahimci rigima ce kawai take ji da shi amma da ta shigo hannunsa zai sauke mata shi.
@@@@@
Da misalin karfe tara hamma mazeen ya kira Hadiza a waya yace ta kirawo masa Azima, Hadiza ta amsa da to sannan taje kiran Azima wacce yanzu dakinta daban ita daya, a lokacin tana kwance a gado ta zama macijiya, Hadiza kuwa tana zuwa ta sako kai ta tura kofa, wani burki tayi turuss! Ganin abunda ko a mafarki bata taba gani ba, shirgiɗeɗen maciji blue sai sheƙi yakeyi, wani mahaukacin ihu Hadiza ta sake tana zubewa a kasa sumammiya, da sauri Azima ta waigo nan tayi saurin komawa mutum ta yo kan Hadiza.
Da gudu su Maman Hanan suka fito har da Al’mazeen wanda ya sauko daga part dinsa, dakin Azima suka nufa inda suka ji ihu ya fito, suna shiga suka samu Hadiza a baje Azima na tsaye a kanta, suna shigowa ta duƙar da kai kasa.
“Me kika mata!” cewar Maman Beenah hankali tashe, Sumy wacce ta jima da dawowa dai-dai ta ce
“Ba mamaki itama an shaƙeta ne! Duk yadda akayi wannan yarinya ta taba zaman prison” Al’mazeen cikin fushi ya kalli Sumy yace
“Ban ce duk wanda yake son kansa da zaman lafiya a gidan nan ba ya daina shiga hidimarta!!?” shuru sukayi ya kalli Azima ya ce
“Me kika mata?”
“Ban mata komai ba,nima daga kewaye nake naji ihu na fito da sauri sai na ganta a sume,idan kuma baku yarda ba idan ta farfaɗo ku tambayeta” Al’mazeen ya kalli Sady yace
“Kawo ruwa a yayyafa mata”
“Me?”
“Nace kawo ruwa a yayyafa mata!” ya faɗa a tsawance Sady ta fice tana yatsine fuska, ruwan ta kawo aka yayyafawa Hadiza a firgice ta farka da karatun ayatul’kursiyyu a bakinta! Nan aka hau tambayarta menene, cikin fitar hayyaci Hadiza ke fadin maciji! maciji!
“Maciji!!” Sumy Sady da Hanan da Beenah suka rungumi juna suna ihu,harta su Maman Hanan da Maman Beenah bayan Al’mazeen suka koma jikinsu na kyarma suna tambayar Hadiza ina macijin, yayinda Azima take kallonsu ɗaya bayan ɗaya ta cikin gashin kanta da ta sauko dashi ya rufe mata fuska, Al’mazeen yace maciji dai a dakin nan?”
“E wlh nagani! Katon maciji! Ruwan ganye! Babba ya cike wannan gadon! Na ganshi a kan gadon nan! Wlh na gani! Maciji! Babba maciji!” duk a ruɗe Hadiza ke magana,jin abunda take fadi yasa suka maida maganar ta ta shirme ba mamaki tayi gamo ne,su sumy suka hau tsaki
“Hanan je ki kirawo Talatu ta zo ta kai Hadiza daki,kafin nan bari nayi mata alluran bacci” ya fada yana ficewa, su ma su Maman Hanan duk ficewar sukayi.
Ba jimawa Al’mazeen ya sauko da allura a hannunsa ya zo ya yiwa Hadiza sannan ya ce Talatu ta kaita daki ta kwantar da ita,bayan sun fita Al’mazeen ya kalli Azima wacce kanta ke duƙe yace
“Zan sha shayi, za a iya haɗawa a kawo min?” ya tambayeta yana mai ƙura mata ido, gya ɗa masa kai kawai tayi sannan ya fice ita kuma ta nufi kitchen dan haɗa masa.
Bayan su Sumy da Sady sun koma daki Sumy ke fadin
“Duk lokacin da na kalli wancan jakar yarinya ‘yar fulanin can ji nake kamar na kashe shegiya! har yanzu ban manta da kaini kofar lahira da tayi ba” Sady tace
“Mu jawo shegiya yau mu ci ubanta a dakin nan kawai” Sumy ta ce
“Haka za ayi” fitowa sukayi nan suka hangi Azima da tray a hannunta tana hawa part din Al’mazeen, Sady tace
“Kalli Matsiyaciya, mu jira ta dawo mu ja banza muci uwarta!” nan suka tsaya suna jiran saukowar Azima.
Da sallama ta tura kofar parlorn a lokacin Al’mazeen suna waya da Nawaz, tana ajiyewa ta tashi ta juya zata fita da sauri Al’mazeen ya ce
“Azima tsaya!”
Nawaz ya ce
“Azima? Azima kuma? Al’mazeen wace Azima?”
????????????????????
MOMYN AHLAN✍????
[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????
????✨ *AZIMA DA AZIZA*????✨
(???? _Macizai ne_????)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*????????
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)_
_Follow me on wattpad,@Fateemah’0_
????????????????????
*PAID.*
????️=6️⃣3️⃣↪️6️⃣4️⃣
“Amm Nawaz ina zuwa zan kiraka” Al’mazeen na faɗi ya ajiye wayar, da kallo Nawaz ya bi wayarsa da shi yana fadin
“Azima irin sunan yar uwar Aziza ce fa? anywhere mutane nawa ne masu suna iri daya” daga wannan tunanin ya ajiye wan can a gefe.
“Azima pls ki tsaya ki saurareni! Fushin ya isa haka kiyi hakuri dan Allah! Har tsawon wani lokaci zaki dauka kina fushi dani?”
ƙin magana tayi yace
“To shikenan idan ba zaki min magana ba, ga wayar ki karba,babban aminina Nawaz zaiyi aure shi da kanwarsa yau saura kwana shidda bikin,ni kuma zan tafi nan da kwana uku kafin nan gobe zanyi kwana biyu a asibiti dan akwai mutum bakwai da zan yiwa aiki, ki karbi wayar dan na dinga jin lafiyarki, sannan idan na dawo jibi ba lallai bane mu samu magana da juna ba, dan ba da wuri zan dawo gida ba, da washe garin kuma da wuri zan kama hanyar kaduna” saurin karban wayar tayi tana fadin