AZIZA DA AZIMA 61-70

“Nima zan bi ka bikin” tashi yayi yana fadin
“Ba zaki bini ɗin ba, ba fushi kikeyi dani ba ana neman sati uku baki min magana”
“To kayi hakuri na daina fushin amma zan bi ka”
“To naji, saiki shirya, mutanen gidan nan ma zasuje, idan kika je ma zaki ga wata mai kama dake”
“Mai kama dani kuma!? Ni babu wani mai kama dani a duniya! ni ni daya ce”
“To naji amma ki dai shirya da wuri,dan inaso ace karfe shidda da rabi mun bar gidan nan” murna ta hauyi tana tsalle zataje yawo, watakila ma daga can ta samu kafar guduwa ta gudu ta huta da ala’ƙaƙai, sai da safe ta masa zata fice ya dakatar da ita, yace
“Kina son makaranta?” tabe baki tayi ta girgiza kai, ƙura mata ido yayi yana hango gaskiyarta yace
“Kwanaki na tambayeki kin sauke al’kur’ni kika ce min a’a shima nace zaki ci gaba kince bakiso,ke baki san ilmi shine mutum ba?”
Azima a ranta ta ce
“Humm! Wani karatu ni da ko sallah bane yi” amma a fili da shike tana murnan barin gidan ya sakata fadin
“Idan muka dawo daga kaduna na yarda zanyi makarantar” ta faɗa tana murmushi”
“Kinyi alkawari?”
“E nayi” ta faɗa tana ficewa.
da murnanta ta hau saukowa tana zuwa dai-dai step din tsakiya taji an fisgota an shige daki da ita aka wurgata ta fadi kasa, tana daga kai ta ga su Sumy da Sady ,hade rai Azima tayi tana shirin magana sady tace
“Inyeee yar banza miye a hannunki? Kinje ya gama kwalularki sai ya baki me?” ta faɗa tana sa hannu ta fizgi wayar daga hannun Azima, tashi tsaye Azima tayi, sumy tasa hannu ta yaye mata mayafi ta jefar,Azima ta duƙar da kai,maganar Al’mazeen ne ya faɗo mata da yake cewa shi a rayuwarsa baya son rigima, sannan yadda yasa doka su daina shiga tsabgar Azima haka itama Aziman yace ta daina shiga tsabgarsu idan kuma maganar aiki ne to yanzu ma shi zata dinga yimawa tinda dama shike biyan duk ma’aikatan gidan, tunowa da haka ya sakata fadin
“Kunga bani shiga hidimarku tunda Hamma Mazeen bai son rigima,ku bani wayata!?” Azima ta faɗa tana cije baki gami da miƙa hannu, Sady ce take ƙurewa dalleliyar wayar kallo tace
“Inyeee! waya mai tsada wa yar aiki! yar aikin ma ƙidahuma!? To wlh ba zan bayar ba fasawa zanyi sai dai duk abunda zai faru ya faru” da sauri Azima tace
“Karki fara wannan kuskuren dan na…..” maganarta ne ya tsaya cak sakamakon rutsa wayar da Sady tayi da bango, saurin zuwa daukar wayar Azima tayi jikinta na b’ari alaman b’acin rai, tana daukar wayar ta ga ya ragargaje, bata gama saita b’acin ranta ba taji an jawo wuyar rigarta, waigowa tayi ta ware blue eye dinta a kan Sady, Sady na ganin ido a rine tayi saurin sakin wuyar Azima taja da baya,ihu Azima ta sa ta haɗa hannuwanta biyu ta ɗagasu sama ta tayar da guguwa ya dauki Sady ta dinga bugata da bango, ihu Sady keyi yayinda Azima ta wurga wani bakin abu a kofar shiga daki wanda duk ihu da kacaniyar da za ayi a dakin babu mai ji, nan ta haɗa da sumy ta dinga cin uwarsu,kuka suke suna bata hakuri tare da gaya mata basu san cewa ita ba mutum bace tayi hakuri, Azima da ta kara yin sama da Sady ta buga mata kai a silin fuskar Sady duk jini ta ce
“Shin zaki iya maida min wayata ta koma yadda take? Na sha gaya muku karku tunzurani ku ga asalin wacece ni amma kun kasa fahimta! An gaya muku ko wane yake mutum! Balle kuce zaku takasa son ranku!” cikin kuka Sumy tace
“Dan Allah Anty Azima kiyi mana rai! Ni wlh yau din nan bana kwanan gidan nan,gobe da sassafe kuma katsina nayi,wlh har ta auren Hamma Mazeen din ma nikam na yafe” Sady ma mai kwasar baƙar wuya tace itama ta yafe, sakinsu Azima tayi suka zubo a kasa sharab kamar an watso kaya, suna faduwa suka hau tattaren kayansu, a daren suka fice ba tare da kowa ya sani ba sai mai gadi da kuma driver da suka ce masa ya kaisu gidan wata kawarsu, Azima sai da ta gargaɗesu da cewa wlh idan suka sake suka gaya ma wani abunda ya faru sai ta maida Sady kunkuru ta maida Sumy gwaɗo, jin haka yasa sukace bakinsu ƙanin kafarsu.
Bayan sun tafi Azima ta dau wayarta ta sa hannu ta shafe kayanta ta koma yadda take kamar ba abunda ya same shi tayi hanyar dakinta ta kwanta tana murmushi tana kallon wayar wajan kusan sha biyu da yan mintoci,bayan ta gama daddannawa ta ajiye ta lumshe ido alaman bacci yazo sai taji wayar na ƙara,dubawa tayi tana hararan wayar, to waye kuma a wannan lokacin? Ta tambayi kanta, dagawa tayi kamar yadda Al’mazeen ya nuna mata tasa a kunne, da masifa ta fara tarban wanda yake kan layi
“Dalla waye! A wannan lokacin! Baka iya hakura ka kira gobe ne! Ko baka san yau na karbi wayar bane? Idan Hamma Mazeen ya sani ai sai ya kwace! Idan kuma ya kwace ko ma waye kai Allah ko a ina kake sai na maidaka burgu!” dariyan Al’mazeen taji ta zare ido tace
“Hamma Mazeen? Dama kai ne? Bakayi bacci ba? Ina dai ba wani abu kakeso ba?” ajiyar zuciya ya sauke mai karfi ya ce
“Na kasa baccin ne shine nace bari na kiraki muyi hira”
“Oh to inajinka” hira suka hau yi ko wannensu ya saki baki,Al’mazeen yana son gayawa Azima yana sonta amma sanin ba ko da wani lokaci take saiti ba zata iya tsince masa notinan kai ta damka masa a tafin hannunsa, shiyasa ya yi shuru suka ci gaba da hira har wajan biyun dare, harbi suka ji ya fara tashi a gidan, Al’mazeen yace
“Ƙaran miye haka? Subhanallahi! ba dai b’arayi ba! Azima karki fito!”
“A’a Hamma mazeen kai karka sauƙo”
“Azima nace miki karki……”
“Na ce maka ka tsaya ko!” ta faɗa a tsawance tana ajiye wayar ta fito, fitowarta ya yi dai-dai da balla kofar parlor da sukayi suka shigo dik da kofar security door ne, suna shigowa da Azima suka fara karo duk sun rufe fuska suna riƙe da bindigogi, Azima suka cafka suna tambayarta ina mai gidan tace baya nan, ogansu ne ya bada umarni a shiga lungu da saƙo na gidan a fito da duk mutanen gidan har da ma’aikata, nan kuwa aka hau fito da ma’aikata sannan aka sauko dasu Maman Hanan da Beenah da Maman Beenah,Hanan da Hanif duk aka fiddo dasu,bindiga aka ɗorawa Maman Hanan a goshi ana tambayarta ina Al’mazeen kafin Maman Hanan tayi magana Azima ta kuma faɗin baya nan da karfi babu alamun tsoro a tattare da ita, Al’mazeen kuwa yana aikin dambe da kofar dakinsa wanda ya kasa buɗewa, Maman Hanan jin bindiga yasata fadin
Ai part din Al’mazeen na saman nasu dan haka yana can sama, nan ogan b’arayin yace su hau su duba,dama wa inda suka hau daga farko basu lura da dayar step din ba, wani ke fadin yau zasu cika aljihunsu da kudi a wannan gidan, Azima tace
“Idan baka cika aljihunka da kudi ba,ni na maka alkawari zan cika maka cikinka da gubar dafin maciji!”
“Kai wannan yarinya bata da kunya! Waike bakinki baya shuru ne zan fasa kanki da bindiga fa!” cewar wani daga cikin b’arayin, ogansu yace ku kyaleta mun san irinsu ai, bari mu karbi abunda ya kawo mu daga nan mu rabata da baki har abada muyi mata fyaɗe muyi gaba, wani kallo Azima ta musu tana shirin magana taga an fito da Al’mazeen ana jansa, ranta ne ya b’aci ganin yadda suke fizgar shi kamar kaza.
Gaban ogan aka kawosa ya dago ido yaga ahalin gidansa a zube a kasa an kewayesu da bindiga Azima kuma ana riƙe da ita.
“Dan Allah karku yiwa kowa komai plss” Al’mazeen ya faɗa hankalinsa a tashe
Wani dariyar mugunta ogansu ya sake ya ce