AZIZA DA AZIMA 61-70

“Abunda ya kawo mu ba mai tsanani bane Kuɗaɗe kawai zaka bamu sannan mu yiwa wannan yarinyar fyaɗe mu kama gabanmu” zare ido Al’mazeen ya yi jin sunce zasu yiwa Azima fyaɗe hakuri ya hau basu amma da shike zuciyarsu ta riga da ta bushe da rashin imani sukace babu abunda ya damesu, Al’mazeen yace
Su fadi kudin da zai fanshi Azima,nan suka masa wani zunzurutun kudi wanda idan ya basu ya kwashe kudin acct dinsa kaff kai har ma da gidan da suke ciki a yanzu, zufa ce ta hau wankewa Al’mazeen jiki yace musu baya da wa innan kuɗaɗen a gida, sannan kudinsa na acct bai kai wannan ba sukace karya yake yi,idan babu kudin a gida to ya musu transfer (kai b’arawo da karfin hali yake wlh).
“Ko da yana da shi ba zai bayar ba!” Azima ta faɗa jikinta na rawa sabida bakinciki izuwa yanzu yaci ace kaff ta sare b’ayin nan amma fitowar Al’mazeen ya dakatar mata da komai.
“Ai kuwa idan bai bayar ba lahira zatayi baƙo, ke kuma zamu yaga-yaga dake! idan kuma kinci musu ya kuma fadin cewa ba shi da kudin da muka tambaya ya gani, dan ko biyar ba zamu rage ba” shuru Al’mazeen ya yi zuwa can suka ce yana bata musu lokaci akwai gidan da zasuje
Almazeen yace
“Wlh kudina na acct bai kai haka ba,kuyi hakuri na baku kuɗin duka amma bai kai yadda kuke bukata ba”
“Amma lallai ka raina mana hankali, a wannan babban gidan naka zakace baka da kudin da muka tambaya ashe kuwa baka son rayiwarka da ta wannan yarinyar!”
“Ku kashesa!” ogan b’arayin ya faɗa, daga Al’mazeen akayi aka saita masa bindiga ganin haka yasa da sauri Azima ta rintse ido hannunta ya kama da wuta ta ciki, saurin saketa wanda suka riketa sukayi sakamakon wani bala’in zafi a tafin hannunsu, rintse ido Al’mazeen yayi yana kalman shahada, ji yayi karan an saki kunnamar bindiga, kafin bullet din ya shigo jikinsa Azima ce ta fara shigewa jikinsa bullet din ya shigeta a baya, saurin buɗe ido Mazeen ya yi ga Azima a jikinsa da Alama bullet din jikinta ya shiga!
“Azimaaaaa!!” Mazeen ya faɗi hankalinsa tashe da sauri tasa hannu ta shafi fuskarsa nan ya kafe, sannan ta juya ta watsawa su Maman Hanan wani baƙin hayaki nan suma suka kafe sannan ta juyo tana kwashe gashin fuskarta ta nannaɗe ta waro blue eye dinta, dan idan bata ci ubansu ba hankalinta ba zai kwanta ba,bakinciki zai iya sawa ma ta sari kanta ta mutu.
Su kuwa b’arayi tsayuwa kallon bala’i da ikon Allah suka yi, wani gurnani Azima tayi ta juya nan ta zama macijiya.
Karyan iskanci nan suka saka ihu, ta ce
“Kamar yadda baku da imani haka nima ban da shi, nawa kam har ya fi naku! RUWA BIYU! AZIMA! AZIMA BANJU MACIJIYA! NI MACIJIYA CE!” tana faɗi ta hau binsu da sara, sai da ta saresu kaff sannan ta naɗesu kaff dinsu da jelarta ta sulale ta jasu suka bar gidan, b’acewa tayi ta kaisu jeji ta watsar dasu sannan ta koma gidan, nan ta samu mai gadi a sume an harbesa a kafa shima,bata yi ta kansa ba ta koma ciki ta samu har yanzu suna nan a daskare hannu tasa ta shafe jinin dake wajan tass sannan ta watsawa su Maman Hanan wani bakin hayakin nan ta sakesu, Al’mazeen kuwa kara shigewa jikinsa tayi ta shafo fuskarsa nan shima abun ya sakesa a firgici ya riƙo Azima wacce ke sulalewa a jikinsa yayi saurin haɗeta da kirjinsa yana ambatar sunanta, dago kai yayi bai ga kowa ba yaga wayam
To meya samesa sai kace wanda komai na jikinsa ya tsaya na wucin gadi.
Su Maman Hanan kuwa masu fitsari a jiki da masu kashi duk sunyi, Hadiza kuwa cewa tayi wlh yau gidansu zata tafi dan daren nan babu abunda ta gani sai bala’i ido da ido, Al’mazeen na daukar Azima suka fito gabadaya nan ya iske mai gadi a kwance shima da harbi a kafa, kwashesu yayi duk ya kaisu asibiti a lokacin da ya fito ana kiran sallan assalatu.
Bayan sun isa asibitinsa duk yan gidan aka hau basu taimakon gaggawa shi kuwa ya wuce cikin emergency da Azima, shi da kansa ya hau mata aikin cire mata bullet din da ya shiga bayanta,duk abunda yakeyi tanajinsa sarai har ya gama yi mata komai, allura ya dauko zai mata tayi saurin riƙe hannunsa tana girgiza masa kai, da sauri ya hau kiran sunanta,murya can kasa tace
“Hamma karka a yi mini allura zai cutar dani, jikina bana allura bane karka mini dan Allah” hawaye Al’mazeen ya goge yana gya ɗa kai alaman ba zai mata ba, duba agogo ya yi ya ga bakwai dan haka ya wuce masallaci dake cikin asibitin ya yi sallah sannan ya koma ya duba lafiyar kowa ya ga kowa lafiya harta mai gadi an cire masa bullet yana zaune, sai a lokacin yaji ya samu natsuwa ya kira jami’an tsaro ya shaida musu duk abunda ya faru, bayan ya gama musu bayani ya tuno da ashe ya bar wayarsa a gida dan da wayar asibiti ya kira jami’an tsaron kasancewar akwai wa inda ya sani a ciki, wayar wata nurse ya karba ya saka lambar Nawaz ya hau kira, sai da ya masa kira uku kafin nawaz ya daga Al’mazeen ya ce
“Dude ni ne”
“Kai Dude jiya muna magana kace zaka kirani baka kirani ba ni kuwa nata kiranka baka daga ba,ina fata dai komai lafiya?”
“E to da sauki dai” nan Al’mazeen ya ba wa Nawaz labarin abunda ya faru, hankali tashe Nawaz yace gashi nan tahowa Kano, Al’mazeen ya ce
“Noo! Wlh karka zo don’t worry we are safe now alhamdulillah! and Karka gayawa Mom am sure hankalinta zai tashi but still zan taho jibin In sha Allah dan na saka jami’an tsaro a lamarin,pls karka damu ina lafiya”
“Pls take care of urself” daga haka sukayi sallama.
Sai wajan karfe hudu kafin suka gama watsatstsakewa sannan suka ɗunguma sukayi gida har lokacin yan sanda suna zagaye da gidan,nan maƙota aka hau yiwa su Al’mazeen jaje ana yin Allah ya kiyaye gaba, nan police suka ba wa Al’mazeen rahoton sun san b’arayin sun jima suna aikata b’arna amma yanzu sun nemesu sun rasa amma zasu ci gaba zurfafa bincike, godiya Mazeen ya musu sannan yace yana da bukatar matakan tsaro a gidansa, nan D.P.O. ya shaida masa babu komai, sannan ya kamo Azima wacce ke zaune a mota ya fito da ita suka shiga ciki, dakinta ya kaita ya kwantar da ita ya kalleta yace
“Meyasa kika tare min harbi?”
“Nima ban san meyasa nayi hakan ba, amma naji a jikina ba zan iya bari a harbeka ka mutu ba” shuru Mazeen ya yi sannan ya tashi ya fita.
Sai dare tukunna su Maman Hanan da Maman beenah suka hau neman su Sumy da Sady, ko da aka kira wayarsu cewa sukayi sun jima a katsina, nan aka basu labarin abunda ya faru Sady tace
Ashe da rabon ba zamu ga masifa biyu ba,munga daya kun ga daya,maganar auren Almazeen kuwa sun yafe Allah zai bamu wani kar muzo mu bamuci kudi ba mu mutu a banza sai anjima anty suka kashe wayarsu.
Bayan kwana biyu Azima ta warware sai shirin tafiya kaduna akeyi gobe, har yanzu kuma ba a samu wani rahoto ba dangane da b’arayin, su Almazeen zasu tafi gobe shida Azima, su Hajiya Lawiza kuma sai ana gobe daurin aure zasu je.
Da washe gari kamar yadda Mazeen ya cewa Azima ta shirya akan lokaci hakan ce kuwa ta kasance karfe takwas suka kama hanyar kaduna, gaban Azima sai bugawa yakeyi.
Itama Aziza yau da bugun zuciya ta farka dan bata san da maganar aurenta da Nawaz ba duk wannan hidima sai a daren jiya, tun tara suka tafi gidan gyaran jiki da lalle dan idan basuyi yau ba gobe Sultana tace ba fita zatayi ba,kuma mom tace dole ayi walima a goben tunda jibi ne daurin aure jumma’a kenan.