AZIZA DA AZIMA 61-70

Goma da rabi Al’mazeen suka iso, a lokacin gidan ya fara cika da mutane yan biki, yana shiga ciki ya yi parking din motarsa bugun zuciyar Azima ya tsananta,kallonta ya yi ya ce
“Menene?” girgiza masa kai tayi alaman babu komai
“To fito” suna fitowa Nawaz shima na fitowa daga part dinsa zai shiga wajan mom ta kirasa ya hangi amininsa, da sauri yazo suka rungumi juna ya kara yi masa jaje, bai ma lura da Azima dake maqale kanta na mugun juyawa ba ga jiri ga zufa, har sun fara tafiya Al’mazeen ya waigo ya ce
“Azima?” da sauri Nawaz ya juyo ya kalleta tana sanye da black shadow a idonta, fuskar a bude amma tayi rolling din veil mai rufe rabin fuska,ƙura mata ido Nawaz yayi, ya kalli Al’mazeen yace
“Who is she?”
“I will tell u later, now let’s go inside, Azima muje ko?” jinjina kai tayi tana gaishe da Nawaz ya amsa ba yabo ba fallasa suka shiga, suna shiga aka hau yiwa Nawaz tsiya ango ango aure ba shiri a lokaci guda mun zata sai mun buga mata gangan gauro ashe yanzu kuwa wa Almazeenu zamu buga mawa, cewar tsofaffi, su dai dariya sukayi suna hawa sama Azima na kan binsu a baya, dakin mom suka shiga da sallama mom ta amsa tana yiwa Almazeen oyoyo gaisheta yayi ta amsa cikin kulawa tana fadin
“Ka ga ikon Allah ko? Abokinka zaiyi aure ,da ina shirin takura muku ashe Allah ya riga da yayi ikonsa, yanzu ma kai zan takura ma wa, naso ace a tare zakuyi aure wlh!”
“Mom ba komai ai,komai lokaci ne nima ranata tana zuwa in sha Allah”
“Amma dai ba da wannan Alishan ba ko?” Nawaz ya fada yana hararan Mazeen
“To wai ina ruwanka?mom ki masa magana”
“E kuma gaskiya ne ina ruwanka kai zaka zauna masa da ita ne” mom ta fada tana daga kai ta kalli Azima dake tsaye a bakin kofa kanta a duke jikinta na rawa
“Wacece kuma?”
“Amm umm e mom tare muka zo da ita, inasu Sultana?”
“Ayya sannu da zuwa ɗiyata” Mom ta fada tana kurawa Azima ido ganin wani sirhitaccen kamanni da takeyi da Aziza, duƙawa har kasa Azima tayi ta ce
“Ina kwana mom? Mun sameku lafiya?” hakan da tayi ba karamin dadi Almazeen yaji ba, Mom ji tayi muryan ma irin na Aziza amma sai dai Aziza ta fita sanyin murya sosai,
“Alhamdulillah! Ga shi kin zo su Sultana sun tafi gidan lalle da gyaran jiki, amma zo na nuna miki dakin sultana sai ki zauna ki jira su, ko kina so a kaiki gidan lallen kema a miki?”
“A’a ban taba yi ba ma a rayuwata, zan jira su ɗin kawai” mom tayi murmushi ta kama hannun Azima caraf idonta ya sauka akan zoben hannun Azima iri daya sak da na Aziza,kuma Aziza tace sadda aka haifesu kakansu Arɗo shi ya ba wa Hajjarsu ta saka mu shi a hannu, daurewa Mom tayi ta ce ya sunanki?
“AZIMA!”
“Ma sha Allah Azima suna mai dadi, Azima wa?”
“AZIMA BANJU!!” ba iyakar Mom ba harta Nawaz wanda yake kokonta sai da ya waigo a firgice, da kyar Mom ta iya riƙe kanta tana murmushin yaƙe ta rungumo Azima ta kaita dakin sultana sannan ta koma daki ta samu Almazeen na tambayar Nawaz meke damunsa, Mom Na shigowa Nawaz ya mike yana fadin
“Wlh ita ce mom, yar uwar Aziza ce, Allah Alhamdulillahi³!” Mom da Nawaz suke faɗi, Al’mazeen da kansa ya shiga duhu yace
“Dan Allah Mom ku min bayani ku fiddani a duhu, dama Aziza tana da yar uwa ne?” mom tace
“Dole zamu maka bayani amma kafin nan a ina kasan Azima ina ka sameta?” bai boye musu ba aiki takeyi agidansa a cam ma ya sameta dan tun bayanan su Maman Hanan suka gaya masa an dauke sabuwar mai aiki, har izuwa sadda ya dawo da shakuwar da ta shiga tsakaninsu.
“ALLAH KENAN MAI YIN YADDA YA SO, HAKURINKA BAYA FADI KASA BANZA! ALLAH YA TAKAITA MANA WAHALA” cewar Mom tana jinjina kai, zama sukayi nan Mom ta hau warwarewa Al’mazeen komai bata kara ba bata rage ba, Al’mazeen ya zare ido yace
“Kenan mom *AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE? SANNAN YAN BIYU NE?* mom ta gya ɗa kai,
“Kenan Azima ba Azima bace Banju ne?” mom ta ƙara jinjina kai
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!” mom ta kara da cewa
“Wannan shine dalilin da yasa auren Nawaz da Aziza ya tashi babu shiri dan yin jahadi ya taimaki Aziza” jinjina kai Al’mazeen yayi ya ce
“Idan har Aminina zaiyi wannan aikin ladan ba tare da ya faɗa soyayya ba ina ga ni da na fara son Azima? Sannan ta taimakeni da badin sanadinta ba da yanzu b’arayi sun kasheni!” nan ya bai wa mom labari mom ta hau salati tana sanar da ubangiji, sannan ya kara da cewa
“Ta taimakeni! Ta ceci rayuwata yayinda ta saka nata a hatsari! mom ina son Azima! Ina so kuma jibi nima a ɗaura min aure da ita amma karta sani, kamar yadda Banju shaiɗanin aljani ne zai iya kashemu idan har yasan da hakan, sannan ya kamata a gayawa Aziza kar ta dawo gidan nan dan karsu haɗu da Azima har sai bayan an daura aure” Mom tace
“Hakan ma wata shawara ce mai kyau,idan yaso aka daura auren da washe gari ranar sai mu shirya tafiya yola,ko kuma da an daura kawai mu wuce tinda Aziza tace cikin daci suke, sai ku shirya mota mai ƙarƙo da zai iya kaimu zamu tafi da Malam Yunusa da ƙanin mahaifinku da kuma Hajiya Lawiza ko kuma Hajiya luba”
“E hakan ma yayi mom” cewar nawaz, na suka gama tsara abunda zasuyi.
An gama yiwa Aziza lalle tana zaune,ita kuwa Sultana ana wanke mata nata, gajiya da zaman Aziza tayi ta ɗan jinginu tana lumshe ido, tana lumshe ido wa zata gani? Azima ta hanga wani ajiyar zuciya ta sauke da jan numfashi ta buɗe ido tace
” *AZIMAA!?”* sultana tace
“Azima kuma? Ina kika ganta?”
“Wlh na ganta Anty Sulty ina rintse ido na ganta,ina zuwa bari na sake dubawa” rintse ido tayi ta shafo tafin hannunta nan ta hangi Azima kwance a gadon sultana, a hankali ta buɗe ido tace
“Azima a gida kuma a dakinki a gadonki?” sultana zatayi magana wayarta ya yi kara, tana dubawa ta ga mom saurin dauka tayi tasa a kunne tayi sallama mom tace saurareni da kyau Sultana” nan mom tayiwa sultana bayanin komai sannan tace
Idan sun gama su biya gidan kawarta Hajiya Biba su ajiye Aziza sannan su su dawo, yanzu sultana ki yiwa Aziza bayanin komai yadda na miki, mom na gama fadi ta ajiye waya,sultana ido bude ta kai bakinta saitin kunnen Aziza tayi mata bayani dalla-dalla,itama Azizan ido a waje ta kalli Sultana, sultana ta jinjina mata kai.
Basu gama ba sai gaf magriba dan haka ko da suka tashi suka biya suka ajiye Aziza a gidan Hajiya Biba su kuma suka wuce gida.
Ko da suka isa Sultana bata nunawa Azima komai ba tayi maraba da ita ta hau janta a jiki.
Nan sanarwan aure ya koma na mutum uku.
Da washe gari walima Mom ta ba wa Azima haɗaddiyar dogon riga wanda yasha stone, a jiya ne ma da dare tasa aka nemo mata kasancewar ba ayi shiri da ita ba, bata tayi ta saka Azima ta karba ta mata godiya, kasancewar a gidan za ayi walimar a tare kusa da juna Mom ta zaunar da sultana da Azima,itama Aziza ana can anayin nata a gidan kawar mom, sadda aka fara wa’azi dodon kunnenta kamar zai tarwatse ji take har fatarta ƙuna yakeyi dan da karfi Malama Rasheedat Hassan Usman ke fadin Allah yace Annabi Yace.
Duk wanda yazo ya tambaya wannan itace amaryan Nawaz din sai mom tace a’a ta Al’mazeen ce, lokacin dasu Maman Hanan suka iso kamar su mutu da bakin ciki dan tun a jiya labari ya iskesu nan suka dinga tsinewa Almazeen da Azima, har suna cewa dama ya sane ya ƙi fada musu zaiyi aure.