AZIZA DA AZIMA 61-70

“To ba damuwa hakan ma yayi Allah ya iya mana” Baffa ya amsa da amin, mom ta kira Nawaz da Almazeen tace musu su bi Baffa, Malam Yunusa kuma da kanin mahaifinsu Nawaz Alhaji Karami suna tare dasu sarki chubado da mai unguwa ori sai hira sukeyi ana shan damemmen fura da nono, gwanin sha’awa.
@@@@@
Gidan suka je, duk da gidan kara ne amma yadda aka shirya gidan ya burge Almazeen, tarko Baffa ya saka a ciki da waje ta yadda ko Banju ya fice a jikin Azima ba iya guduwa zaiyi ba.
Sannan Baffa ya ba wa su Almazeen da Nawaz wasu maganguna da rubutu yace su sha, ya basu na kariya da na sha da na wanka da na gogawa dana murzawa dana ɗorawa duka babu wanda bai basu ba, daga nan sukayi wani gida gaba kaɗan da na inda aka ba wa Almazeen, Baffa yace
“Nawazu, kai ma a nan zaka zauna ka riƙe Aziza, dan a lokacin da abun da ke jikinta zai fita zata iya shiga wani hali, zata iya fita hayyacinta, idan kuma ta subuce zamu iya rasata na har abada dan babu abunda Banju ba zai yi ba” Nawaz yace
“In sha Allah hakan ma ba zata faru ba Baffa, hakuri da gaskiya sune a sama, zamuyi nasara a kan Banju bi’izinillahi ta’ala!” Baffa ya yi murmushi na jin dadin samun sirkai kamarsu Nawaz da Almazeen, haka shi ma wannan gidan ma ya saka matakan tsaro.
Wunin ranar kuwa Baffa bai zauna ba shiri yayi sosai ya koma asalin Garkuwa Magaji Bawansa kyakkyawa fari dogon bafulatani mai dogon hanci da halin girma da cikar zati da haiba.
Da daddare mom ita ce tayiwa Azima da Aziza komai,ita da Maman Beenah suka raka Azima da Aziza, Almazeen wani irin kunya yakeji, hajja kuwa ta kasa fitowa a bukka tana zaune tana tasbihi ga Allah, tana roƙon mai duka da ya fidda mata yaranta lafiya, hakika ita kam ta ga jarabta.
Bayan an mikawa Almazeen Azima wacce take da ita da babu za a iya cewa duk daya, sannan aka wuce aka kai wa Nawaz Aziza duk da shi ba wani abu bane zai wakana a tsakaninsu.
Ko da su Mom suka koma itama ba kwanciya tayi ba, alwala tayi ta zauna ta fuskanci gabas, Maman Beenah kuwa gadon kara ta haye tayi kwanciyarta dan tace bacci takeji.
Baffa ma uban gayya bai ga ta zama ba balle ya rintsa dan kuwa a tsaye yake kyam.
????????????????????
*AL-MAZEEEN DA BANJU AZIMA.*
A bukka kuwa Almazeen zama ya yi ya kurawa Azima ido yana kallonta, shi bai ma san ta ina zai fara ba, ya kwashi kusan mintuna talatin yana kallonta daga bisani ya tashi ya ɗauro alwala ya yi sallah raka’a biyu, ya ciro wayarsa ya yi karatun alkur’ani mai girma ya daga hannunsa sama yana adduoi sannan ya shafa ya miƙe a hankali ya fara rage kayan jikinsa, wani magani da Baffa ya basa yace ya shafa a jikinsa idan zai taba Azima, maganin ya shafa a hannunsa da dukkkan jikinsa, yana tabata sai da ta girgiza,kwantar da ita yayi, Banju dake jikinta yana kallon abunda ke faruwa ɗauresa kawai Baffa yayi, wani gurnani ya fara nan ya hau buge-buge, Almazeen da iyakacin karfinsa ya fizgi kayan dake jikin Azima, nan dambe ya kacame duk da banju yana daure amma ba shi ya hanasa kokarin yunkurin kashe Almazeen ba shima Almazeen yaci albarkacin daure Banju da Baffa yayi amma duk da haka yanaji a jikinsa, duk kalman da yazo bakin almazeen indai na salati ne yin shi yake yi
,Banju bai gama sarewa ba sai da ya ga Almazeen ya yiwa Azima kaff da kayan jikinta, yunkurin komawa maciji Banju yayi amma kafin ya fara hakan tuni Almazeen ya karanto adduar saduwa ya fara kokarin shiga jikin Azima, wani sarawa kansa yayi tare da wani wawan jiri dake shirin watsa shi waje daurewa yayi ya riƙe kokaran gadon karan gam jikinsa na kyarma, nan Azima ta fara canzawa tana zama wata halitta daban mai matukar ban tsoro da firgitarwa, kokarin zare jikinsa yayi dan dama bai shigeta sosai ba, tunowa da maganar Baffa na cewa kar ya kuskura ya kyale Azima har sai ta yi attisha sau uku dan duk hanyar da Banju zai bi dan ya ga ya hana Almazeen kusantar Azima zaiyi, daga karshe kuma zai kashesa ya kuma guduwa, tunowa da haka yasa Almazeen ya dage da iyakacin karfinsa sakamakon b’ari da jikinsa ke yi ya shige Azima gabadaya, wani ihuu Azima ta saka da karfi wanda sai da ya karaɗe gefe da kewayen inda suke, ta shaƙo wuyan Almazeen wanda shi kadai yasan abunda yakeji kamar ana zare ransa haka yakeji tsananin azaba dan harta fatarsa ji yakeyi kamar ana soya masa shi, sake damƙar kafaɗun Almazeen Azima tayi ta dage ta saki wani attishawa mai karfin gaske dan kuwa an karya makarin Banju tunda Almazeen ya afka cikinta, tana yin attishawa na ɗaya tayi na biyu, na ukun ne nan wani guɗa ya hau tashi, tana attishawar Banju wanda ya yi tsalle ya fice ta baki da hancin Azima, ƙauuuuu! Azima taji yayinda ta wani firgita tana jan wani numfashi da iskar duniya,da nauyin kai ta hau ware ido da kyar jin idon kamar an liƙe mata su, tana ji tamkar yau ne uwarta ta haifeta, tana gama buɗe ido mutum ta hanga a saman kanta, Almazeen wanda yake gaff da sumewa yana ganin ta bude ido a hankali ya sauke bakinsa saitin kunnenta cikin mayuwacin hali da kyar ya furta
“Alhamdulillah! Wlcm back my dear wife, am so happy, u are back! i promise that i wouldn’t let any harm attack u, i will sacrifice my life to u, cox I luv u, am really luv u, i fell in luv with u Azima! pls don’t leave me alone” Almazeen na faɗi ya hau kokarin zare jikinsa daga na Azima, a lokacin Azima taji wani mugun raɗaɗi ta kasanta hakan ne yasa taja wani numfashin mai cike da azaba, a tare suka suma.
Banju dake tsaye yana
kallon Almazeen wanda yake son kashesa dan ya lashi takwabin sai ya kashe Almazeen, amma inaaa ya kasa kusantar almazeen balle ya kashesa kasancewar Almzeen mutum ne mai riƙo da ibada baya sanya.
????????????????
*NAWAZ DA AZIZA.*
Sadda aka raka Aziza tsayuwa tayi a bakin bukkar taki karasowa, Nawaz na zaune yana danna wayarsa da tun shigowarsu garin babu network ko ɗigo, ɗaga ido ya yi ya kalleta ya ga jikinta sai rawa yakeyi, da alama tsorata tayi, a hankali ya tashi yaje gabanta bata ma sani ba tayi zurfi a tunani, ji tayi an kama hannunta, a firgice ta dago idonta ya haɗe da na Nawaz, ganin duk ta taburce yasa Nawaz rausaya kai yace
“Ya haka? Jaruma a waje, matsoraciya a gabana?” ya faɗa yana matsota sosai, ja da baya tayi tana shirin ficewa yasa hannu ya jata ta shige jikinsa,
“Haba jaruma, karki bani kunya mana” mutsu-mutsu ta hau yi tana son kwace jikinta, yasa hannunsa duka biyu ya kewayeta ta kasa kwacewa ya ce
“Ko za a watsar dani ne?” nan ma bata masa magana ba, ya ce
“Idan baki min magana ba, zan cinye bakinki” mamaki ne ya kama Aziza, oh dama haka Nawaz yake? take tambayar kanta, bata gama yankewa ba sai da taji ya dauketa ya ajiyeta a saman gadon kara yana shirin kwanciya a kanta tayi saurin miƙewa zunbur tana fadin
“Sorry Hamma” murmushi ya yi a boye, ya ce
“To matso kusa dani, kin san Baffa yace na rikeki da kyau dan haka matso” ya faɗa yana ware mata hannu alaman ta shigo cikin jikinsa, ganin yadda ya sauya fuska ba alaman wasa yasa ta matso a hankali ta shige jikinsa ta kifa kanta a ƙirjinsa, yasa hannu ya rungumeta da kyau yana son fassara me zuciyarsa takeji game da Aziza.