AZIZA DA AZIMA 61-70

A lokacin da Almazeen suka fara dambatuwa da Banju, a lokacin Aziza na kwance a jikin Nawaz, lokaci daya kamar an zabureta haka ta miƙe, cikin hanzari Nawaz ya fizgota ya maidata jikinsa ya matseta dan ya tuno da maganar Baffa da yake cewa idan Aziza ta subuce za a iya rasata shiyasa ya kara matseta sosai a jikinsa, ihu Aziza ta saka jin fatar jikinta na sabulewa, saurin ture Nawaz tayi ta koma gefe tana ƙanƙame jikinta, fuskarta ne ta ji yana b’anb’arewa, hannu biyu tasa tana tare fuskarta tare da ihu, ganin halin da take ciki yasa Nawaz saurin tashi zai zo gareta, nan yabga masifa, daga ƙugunta abunda ya yi sama ta zama macijiya fara sol sai kyalli take yi, sak irin wanda yake gani a mafarkinsa, hannu ta miƙa masa cikin azaba tana fadin
“Help me plss! ka taimakeni Hamma Nawaz!” ta faɗa siffar jikinta na ƙasa na haurawa zata zama macijiyar gabadaya, da saurin Nawaz ya rintse ido yaje ya rungumeta ƙaƙam! Yana rungumarta ta tsaya a haka, a lokacin da Banju zai fita a jikin Azima itama Aziza taci azaba dan nan suka hau gwada karfi da Nawaz, hakika shima ya jikata, dan kuwa sadda abun zai fita gani ya yi wani farin abu shi ba dutse ba shi ba tsuntsu ba ya fice ta goshin Aziza, yana fita numfashinta ya tsaya cak yayinda ta koma mutum, haka Nawaz ya zauna riƙe da ita a jikinsa, gab’ob’insa na masa ciwo sosai, har asuba.
????????????????????
Sanyin asuba ne ya fara farkar da Almazeen wanda da kyar yake iya buɗe ido sabida nauyin da suka masa, ya jima a haka kafin da layi ya tashi ya janyo kayansa ya saka, ya rufawa Azima jikinta, ya koma ya kwanta a gefenta yana sauke huci mai zafi.
Baffa suna idar da sallar asuba Arɗo yace su je a duba yaran nan.
Mom aka kira dan da ita za aje Hajja ta ƙi fitowa ƙememe.
Suna zuwa gidan Hajja zata shiga da saurin Baffa ya dakatar da ita ya hanata shiga, yace tana shiga Banju zai iya kasheta dan shi yanzu duk wanda ya samu zai kashe ne” Baffa ne ya fara shiga cike da yarda da kansa sabida ya yi imani da Allah ya yi riƙo da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam,duk wanda ya yi riƙo dasu baya da fargaba a kan kowa, yana shiga kuwa Banju dake neman hanyar guduwa a gidan tun daren jiya ya kasa sabida Baffa ya ɗaure ko ina da ina, suna ido huɗu Baffa ya daga takwabi, Banju yace
“Magaji a gwabza idan ba tsoro! karka kasheni sai mun gwabza!” Baffa ya yi murmushi yace idan ka so haka”
“Zan so! amma ka ajiye takwabi” Baffa ya ce
“Ba daga yanzu zamu fara ba, kafin nan ga wannan” Baffa na faɗi ya wurgawa Banju wani igiya nan ya daure Banju ya fito da shi, yana fitowa da shi ita kam mom bata iya daga ido ta kalli Banju ba, dan tace mugun ji da mugun gani Allah ya rabamu dasu, Baffa na cewa zata iya shiga da sauri ta wuce shi kuma ya wuce da Banju, mom na shiga ta samesu a yashe, Azima ta jijjiga sannan ta taba Almazeen wanda jikinsa ke rawa alaman ciwo jikinsa zafi raɗauu kamar wuta, na Azima ma akwai zafi amma na Almazeen ya fi nata, babu wani taimako da zata iya masa, amma zata iya taimakawa Azima, dan haka ta fito ta haɗa ƙirare ta tafasa ruwan zafi, kafin ruwan ya gama sai ga jikan Ardo Sanda ya kawo wasu magunguna yace Baffa yace idan su Hamma Almazeen da Azima zasuyi wanka a zuba musu shi a ruwan wankan suyi wanka da shi, wannan kuma su sha, sannan a ba wa Hamma Mazeen wannan,wannan kuma a ba wa Azima” mom ta karba tana masa sannunsa da aika.
Mom da kanta ta taimakawa Azima tanuna mata yadda zatayi wankan tsarki, sannan tayiwa mata wanka haka,ita dai Azima wani iri take jin kanta, riƙota mom tayi suka shiga bukkar har yanzu Almazeen ya kasa motsi koda da yatsarsa daya ne, taimakawa Almazeen mom tayo shima ya yi wanka ya yi sallah a zaune ya sha magungunan da Baffa ya bada a ba shi daga nan ya hau bacci,itama Azima maganin ta sha ta hau bacci, haka ma Aziza wanda aka aika aka ba wa Nawaz yasha ita ma ya bata ta sha duk suka buge suka hau bacci.
Can wajan dandalin yanki Baffa yaje ya daure Banju, ko kaɗan Banju baida kyawun halitta gani, ga girma katam da shi tamkar basamude ga baƙi fiye da misali, kai babu ta yadda za a sunfanta zubin halittan Banju.
Bayan Baffa ya daure Banju yasa maga isar da sakon yankin kwana a kan ya rubuta wasika yayi aike sauran yankuna ana gayyatar su izuwa kallon fafatawa a tsakanin aljani Banju da Baffa bisa umarnin gayyatar sarkin yankin kwana wato sarki chubaɗo, kamar irinsu yankin ja’i da yankin tudu da yankin ja’o da yankin gangare, da yankin shani, da dai sauran yankuna.
Sadda wasika ta iskesu sun sha mamaki, kai wannan ai babban fafatawa ne a tsakanin Magaji bawa da Maciji Banju, wanda ya yi b’arna da ta’adi a yankin kwana, wanda ya kashe shahararrun masu kama macizai irinsu jarman macizai dasu Innu maciji, da iro mai maganin macizai da dai sauransu, hakika duk yankuna sun amince zasu zo ganin wannan fafatawar tsakanin mutum da aljan,duk da wannan ba sabon abu bane a wajan Garkuwan Kwana Magaji Bawa Arɗo.
Mom ce ta cewa Baffa dan Allah ya taimaka ya raba Aziza da Bahula ta koma asalin cikakkiyar mutun ɗinta ta huta gaba daya, Baffa ya yi murmushi ya ce wannan ba wata matsala ba ce, suka je gidan har zuwa yanzu suna bacci, goshin Aziza Baffa ya riƙe ya rintse ido, attishawa Aziza tayi sannan ta fara hamma, wani farin abu ne ya fito ta bakinta, a hankali farin abun ya koma kamar farin hayaki haka, daga nan abun ya zama mutum wanda ake mata kallon dishi-dishi, Baffa ne kawai yake iya ganinta dan kuwa mom ba ganinta take yi ba, kallon Baffa Bahula tayi tana girgiza kai hawaye na zuba a idonta dan tasan Baffa kashe mata Yayanta Banju zaiyi dan tasan ko a wasa Yayanta Banju ba zai haɗa karfinsa da kwatan karfin da Magaji ke da shi ba,kawai dai a mugunta ne baya da lamba ta biyu, dukar da kai Baffa yayi, daga haka Bahula ta b’ace, muryan mom Baffa yaji tana magana
“Baban Aziza? Yanzu shikenan sun warke babu wata matsala ko?”
“In sha Allahu, sun warke, amma wanda ba yanzu zaiji sauki ba wanda shi ba mu san a ya zai farka ba shine Almazeenu, amma harta Azima zata farka lafiya lau,kuma idan ta farka za a gaya mata gaskiyar abunda ya faru kar a boye mata duk da abun da suka faru zata iya gani duk da ta kasance a sume amma zata iya gani kamar mutum mai bacci yana mafarki sabida sun rayu a jiki daya da Banju,jikin ma kuma nata ne, zata tuna komai kuma zata gane komai shiyasa za a gaya mata sabida rashim gaya mata zai iya haifar mata da wani matsala, mom ta gya ɗa kai tana mai tausayawa Almazeen.
????????????????
Basu suka farka ba sai lokacin sallar azahar, wani ɗauuuu!! Aziza taji a kunnenta da ta farka, zata fadi da saurin Nawaz ya riƙeta, wanda shima yanzu baya jin komai ciwon jikin nasa ya tafi
“Kina lafiya?” Aziza ta gya ɗa kai tana gyara tsayuwarta, zuwa can ta ce
“Azima? yar uwata?” ta faɗa zata fice da sauri Nawaz ya rikota yace suyi sallah kafin su tafi, sallan kuwa suka gabatar shi ya jasu sannan suka fita sukayi gidan da Almzeen da Azima suke, mom ma tana gidan tana kula da Almazeen wanda a zaune ma ya ƙara gabatar da sallah, Azima kuwa tunda ta farka har tayi sallah karo na farko a rayuwarta, bata furta ko da uffan bane kallo kawai take bin mutane da shi abubuwa suna dawo mata kamar a mafarki haka take tariyowa, tana zaune a kan sallayar kaba su Nawaz da Aziza suka shigo da sallama, Aziza tana ganin Azima a kan sallaya tasa kukan farinciki tana fadin