BA JINI NA BA CE Page 51 to 60 (The End)

Sai da yai addu a sosai kafin ya fara hak’a ramin da tayi, yayi mamakin yadda ta iya hak’a rami mai uban zurfi haka, yajima yana hak’a dan har ya fara tunanin babu abin da ta binne kafin yaji hannunsa ya caki wani abu mai mugun tsini da sauri ya janye hannun saiga jini yana bin hannun nasa wanda jini ya fara bi ga wani mugun radadi da ya zuyarci har kwakwalwar sa, mamakin hakan yasa kashi saurin lek’a ramin haba da sauri ya janye kansa yana sauke wani irin wahalallen numfashi sabo da wani fitinannen wari daya daki hancin sa, sai dai abinda ya gani yasa shi saurin komawa tare da dauke numfashi dan tabbas wannan masifar zai iya masa illah.
Mikewa yayi ya koma d’akin sa hankali a tashe ya d’auko hanglob jikinsa har wani rawa rawa yake sosai yazo ya hau fito da abin bakinsa d’auke da addu’a, yanzu kam rawa jikinsa ya kama sosai saboda tsabar mamaki.
Kan mujiya ne jikinsa duk wasu irin manyan allurai sai kuma wata ‘yar k’aramar benu da aka sa wata katuwar allura aka caki daidai zuciyar ta sai numfashi take fitar wa da k’yar ga wasu irin curin layu masu yawa suma a saman wata tsuntsu da baisan ko ta mecece ba itama daga gani ajikace take tama kusa mutuwa.
Idanunsa da sukayi wani fitinannen ja ya runtse da mugun k’arfi ya zauna dab’as a wajen cikin ciyayin gun ya dafe kansa da yake mugun sara masa da k’arfi yace “innalillahi wainnailahi raji’un Maryam ko Ammey zata kashe?”
Dan shi abinda ransa ya bashi kenan na ganin wannan masifar alluran dake jikin tsuntsayen da suke da rai ya fara zarewa kafin ya cire na jikin mujiyar gaban sa na wani irin mugun fad’uwa hankalin sa a masifar tashe bai ma yarda da kona kayan kai tsaye ba sai da yayi musu fitsari kafin yasa fetur ya Kone.
Tunda taga Ammey ta fara shiri tace itafa sai gobe zata dawo dan gajiyan hanya bai gama sakinta ba sosai Abdul jabbar da yake ta binta da kallo yasaki murmushi yace “kawai ki k’yale ta Ammey ma kawota nida Abdul Malik”
“Rufamin asiri Abdul jabbar Baffanku baisan nazo da itaba, kabari tunda bikin ta za ayi tazo tayi muku kwana biyu” sai da gabansa ya fad’i da yaji wai bikin ta za ayi dan har ga Allah tayi masa sosai.
“To ‘yata sai kinzo gyaran jikin ni da kaina zanwa ‘yata gyara na musamman, dake sana ‘ar tane gyaran amare da haka sukayi sallama.
Tana zaune cikin jin dad’in cikar burinta haj. Zakiyya ta kira tana d’agowa tace “ba nutsuwa ba kwanciyar hankali ita ba mahaukaciya ba kuma ba mai hankali ba sannan ita ba rayayya ba sannan kuma ba matacciya ba” hhhhhhhhh suka saki wata muguwar dariya haj. Zakiyya tace an aikata ke nan?”
Me zan jira k’awata kinajifa boka yace uban yatsaida aurenta da wannan tsinannen yaron dana fi tsana fiye da komai a rayuwata wallahi bazan bar wannan banzan auren ya faru ba na rantse kuma” ta k’arasa maganar tana huci
Har lokacin MD yana d’akin sa cikin tsantsar damuwa da nazarin son gane shin cikin Ammey ko Maryam wa akayi wannan bak’in asirin dayai masifar d’aga masa hankali?
Ya sandai wannan tarkacen bala in ba abin arzik’i aka shuka a cikinsu ba.
Kamar wanda aka tsikara ya mik’e zumbur domin kaiwa haj. Sailuba fatanyar ta da ta manta.
Yana fitowa ana budewa motar su Ammey gidan, dan haka ya dakata har driver ya shigo ya faka motar duk suka fito da gudu Nassar ya k’araso ya rungume MD wanda yai kasak’e yana kallon su, yana mai murnan ganin yayan nasa.
Da wani irin kallon mamaki Ammey tabi kayan hannun MD yayin da Maryam ta wuce ciki tana mai dok’in ganin mamanta.
“MUHAMMAD wannanfa me kayi dasu naganka futu futu haka?’
” Ammey” sai kuma yai shiriu zuciyar sa na wani irin zafi yay saurin dafe kansa kafin yace “wa take son kashewa Ammey ke ko ZUCIYA TA?
Muje dai
DAGA MAMAN ISLAM
???? BA JININA BACE????
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 43
Kallon Ammey yake dafe da kirjin sa wanda zuciyar sa take barazanar fitowa, itama kallonsa take da son k’arin bayani.
Dak’yar ya bud’a baki yace “Ammey wani aikin nayi mai wahalarwa Ammey me waccen matar take nufin yi ne akan ni da matata Ammey na rantse da Allah wani abu yasamu matata ni da kaina zan d’auke kanta da wu’ka da wadannan hannayen nawa.
Ya fad’a yana d’aga hannun nasa wanda suke wata irin rawa sama.
Da wani irin rawa Ammey ta danki hannun MD jikinta na kakkarwa tace “wayyo Muhammad rik’e ni zan fad’i” tayi luuuuuu da wani azababban zafin nama MD ya rik’o ta cikin wani irin rikitaccen yanayi yace “Ammey lafiya kuwa”?
“Kaini d’akina Muhammad banida lafiya” da sauri ya d’auke ta akafad’unsa yayin da jikinsa yake wani irin rawa jikinsa kuwa ta ko ina gumine yay masa wanka.
Da sauri ta janye wayar daga kunnenta tana fad’in “zan sake kiranki anjima k’awata” nakamakon juyowa da tayi sukayi ido biyu da Maryam da tajima abakin k’ofar tanajin irin mugun abun da maman tata take k’ullawa tambayar da Maryam take wa kanta shine
“Shin waye za’a haukata?
Waza a tozarta ya wulak’anta?
Waye zai zama abin k’yamar al’umma?
Me yaye mata take son ya zamo kamar mujiya?
Akan me take so yayi warin jab’a?
Shin dama mama tana yawon bin malamai ko yanzun ta fara?
Ta yarda da daukar wannan babban zunubin ko kuwa?
Dawa take wannan Killin?”
Inda haka ne mama baki da imani baki da tausayi baki damutunci matsayin ki na musulma ki rink’a had’a mugun k’ulli haka?
Duk tayiwa zuciyar ta wadannan tambayoyin, yayin da zuciyar ta yake wani irin bugawa sai taji hankalin ta yai masifar tashi wani irin tsoron maman tata ya mugun kamata da gudu ta juya ta fice daga d’akin cikin tashin hankali gaba d’aya idanunta ya rufe.
Tazo shiga d’akin suka gwabza karo da MD wanda yazo neman ta ta tsaya da Ammey wacce ya gama duba zai nemo mata magani, take tayi baya zata fad’i da sauri MD ya taro ta ya rik’e ta yana kallon yadda jikinta yake rawa
Suna had’a ido da shi ta fashe da wani irin kuka har da shashshek’a, ina ma ace Ammey ce maman ta ba wannan matar mai bak’ar zuciya ba, inama ace hannun agogo zai dawo baya data rok’i ubangiji ta fito a tsatson Ammey, sai dai Kash d’an Adam bashi da damar zab’a ma kansa rayuwa sai yadda ubangiji yayi da bawan sa,
“Allah kaza gatana Allah kazama gatana Allah kazama gatana” take ta maimaitawa cikin tashin hankali da wani irin fitinannen kuka, baisan lokacin da yajata jikinsa ya rungumeta da mugun k’arfi hannunsa na wata irin rawa ya d’ora abayan ta yana shafawa a hankali.
Jabbar Mama ta koma saman gado ta zauna tare da d’ora hannunta saman kanta tace “shi kenan na shiga uku taji komai wayyo Allah yau dubana ya cika innalillahi asiri na zai tonu”
Jiki na rawa ta ja waya ta kira haj. Zakiyya tun kafin ta d’aga tace “shi kenan k’awata yau taji komai dakanta ta kamani muna waya dake shikenan zata had’a ni da Baffa na shiga uku na lalace”
“Ke taya akayi kika san tajiki ba kince sun fita da Amina ba?”
“Wllh taji karkiga mugun kallon da take bina dashi dana ganta ma zan wayance bata saurare ni ba juyawa tayi da gudu ta fice”
Kinsan ya za ayi?”
“A’a”
“Zuwa zakiyi kiji idan kin tabbatar da taji abinda muka tattauna sai kibi duk hanyar da zakini nuna mata cewar kunnenta bai juyo mata daidai ba” daga haka suka yi sallama ta mik’e tayi d’akin Maryam.
Tana d’aga labulan tayi wani irin baya cikin girgizar zuciya batasan sanda ta kurma wani mugun ihu tace” jama’a kukawo min d’auki kwarto zai lalata min ‘ya”