Uncategorized

HAJNA 7-8

 


♻️*Bismillahir Rahmanir Raheem*

PAGE 7-8


******************

Kamar yadda Fahna ta tsara haka kuwa aka yi, da isarta tashar motar gusau ta kira Alhaji Musa, ba’a yi minti 10 ba sai gashi ya zo, ɗaukar ta yayi suka kama hanyar abuja.


   A ɓangaren Hajna kuwa wanka tayi ta shirya cikin kayan makaranta, a ƙofar gida ta samu Baffa, “Baffa ni zan wuce sai na dawo “, kallon ta yayi yadda taci kwalliya kamar me shirin zuwa wani guri yace “yanzu Hajna zaki makaranta ma sai kinyi kwalliya?”, Umma ce ta iso ƙofar gidan dan ta shiga gidan su Fahna gurin inna su gaisa, dama duk sata tana zuwa su gaisa “kai ka fiye rigima wallahi, yanzu minene a ciki dan tayi kwalliya” Umma ta faɗa, kallon Umma yake da mamaki yace “wai ke kullum baki fahimtar abunda nake nufi ne”, Umma tace “fisabilillahi yarinyar nan tana iya ƙoƙarin ta, shi fa yaro ba’a matsa mishi “, Baffa yace “Jamila ki fita ido na fa”, kallon shi tayi tace “Allah ya baka haƙuri, ke kuma Hajna Allah ya baki ikon haƙuri da mu “.


(Masu karatu in kun fahimci rayuwar umma mutum ce da bata son ana matsawa yaro, wanda ta wani ɓangaren tana da gaskiya, matsawa yaro bazai hana shi lalalacewa ba in kuka buga misali da Fahna duk tsananin mahaifin ta ga yadda take, amma kuma haka baya nufin kada ku sawa yaran ku ido)



    Tashi Hajna tayi ta shiga cikin gida, wanke fuskantar tayi sannan ta dawo ta fita, a ran Baffa kuwa cewa yayi ina fatan ki fahimci son ki nake shiyasa nake baki tarbiyar da kowa ne uba yake ba ɗan sa.


    Mamakina Hajna ba makaranta ta nufa ba, bayan gari ta je ta zauna tana kallon mutane masu wucewa, har sai da aka tashi daga makaranta sannan ta dawo gida.



 A ɓangaren Fahna kuwa ƙarfe huɗu suka isa garin Abuja, inda Alhaji musa ya ɗauki waya ya kira abokin shi yake faɗa mishi yana cikin garin Abuja yanzu zasu zo gidan shi.


    Masu karatu nayi matuƙar mamaki da naga sun tsays gaban gate ɗin Qaseem buɗe gate ɗin aka yi suka shiga ciki. A parlor suka same shi zaune, ƴan mata guda biyu suna mishi tausa, ɗaya a kan jikin shi, Alhaji Musa ya kalle shi yace “mutumina baka da sauƙi indai harka mata ne “, Qaseem yace “Alhaji Musa kenan, wannan ce sabuwar beb ɗin taka”, Alhaji Musa yace “ka bari kawai yarinyar nan tayi ina gaya maka, ƴar gidan matsiya ta ce gaba da baya amma akwai daɗi “, Qaseem yace “to ka huta ga ɗaki can a kai ma ita, ni bari na gama da waɗannan”, Alhaji Musa yace “ai baka sani ba harka da mace ɗaya daɗi ne da shi “, murmushi Qaseem yayi yace “nima na kusa kama ɗayar nan ai”,“ kai dai kasani” Alhaji Musa ya faɗa yana tashi “ni zan shige sai gobe “, Qaseem yace “to yayi Alhajin ƴan iska ka fito lafiya”.



(Ohh ni ƴar mutum biyu jikar mutum biyu ina ganin rayuwa???? bari na bi su Alhaji Musa naga me suke ƙullawa)


  A ɗaki na same su Fahna tayi tuƙun-tuƙun da rai, “haba shalelen Alhaji “, “ni zaka kira ƴar matsiya ta” Fahna ta faɗa rai a ɓace, “sorry nayi kuskure za’a gyara “, “to wallahi ni ba irin sauran matan da kake ɗaukowa bane ka wulaƙanta, na fi gaban wulaƙanci, dan haka yazama na farko na ƙarshe”Fahna ta faɗa, Alhaji Musa yace “insha Allah za’a kiyaye yi haƙuri”, haka ya dinga lallashin ta har ta haƙura, wanka ya shiga yayi, dan dama ita tana shigowa ɗakin ta shiga tayi wanka, minti 10 yayi a ciki ya fito, boxers kawai ya saka, ita ɗin rigar barci ta saka suka shige bargo.


Ni kuwa bazan iya binsu ba na fito abuna na basu guri ????‍♀️????‍♀️????‍♀️????‍♀️????‍♀️


    Qaseem kuwa ɗaki ya shiga kamar jiya sallah yayi sannan ya kwanta, da misalin ƙarfe tare ya  dannan wani abu a gefen gadon shi sai ga ƴan mata sun shigo, mutum ya zaɓa bana jiya ba sannan sauran suka tafi, tausa suka fara mishi, sannan yaja ɗaya jikin shi, ni kuwa na ja ƙofa na fito.




Washe gari da safe.


   Fahna suna zaune a parlor, Alhaji Qaseem ya sauko, kasancewar yau weekend ne bazai fita ba sai suka zauna suna ta fira, “kasan me Alhaji Qaseem bari na nuna maka hoton Alhaji Musa jiya a mota yana barci ya hangame baki “Fahna ta faɗa tana kwance a jikin Alhaji Musa”, Qaseem yace “yauwa nuna min, dama Musa akwai barci “????, miƙa mishi wayar tayi, Alhaji Musa yace “haba beb, ya zaki min haka kinsan fa nace karki nuna mishi”, Qaseem da ke zaune sai da ya faɗi ƙasa dan dariya yace “to sai me in an nuna min kaifa shu’umin mutum ne “, dariya Qaseem ya cigaba da yi, scrolling yayi dan ya ga wani, unfortunately sai ya yaga hoto wata kyakkyawar yarinya, ƙoƙarin gaɗa yawu yake, ba shiri ya sarƙe, Alhaji Musa ya fara dariya, yace “mugu, ga abunda dariya ta haifar maka ai”, ruwa yasa aka kawo mishi ya sha, sannan ya gyara zama, cigaba da scrolling yayi, wani guri yaga hoton guri kuma ya ganta tare da Fahna, gyara murya yayi yace “Fahna wacece wannan”, Fahna da bata kawo komai a ranta ba tace “babbar ƙawa ta ce Hajna”, lumshe ido yayi yace “wow Hajna suna mai daɗi, kuma kyakkyawar yarinya “, Alhaji Musa yace “ko dai ka faɗa ne”, Qaseem yace “eh wallahi ni dai ta min, ya za kiyi ki haɗa ni da ita “, Fahna tace “ka hutar da kanka dan Hajna bazata saurare ni ba, na jima ina so ta shiga harkar nan amma taƙi, ni wallahi tausayin ta ma nake ji, abinci ma rasawa suke yi a gidan su”, Qaseem da tunda Fahna ta fara magana yake kallon ta yace “Fahna so nake ki jawo hankalin ta yadda ya dace, ni kuma zan miki kyautar million uku da kuma mota sabuwa dal “, Alhaji Musa yace “wace yarinya ce wannan da har Qaseem yake so a harkar shi da zai biya waɗannan maƙudan kuɗi, abunda baka taɓa yi ba”, Qaseem yace “ni ban damu da ko wacece ba in dai zan same ta to zan biya ko nawa ne, dan ajin ta ya min kuma zan zama na farko da zai yaga ta, ke dai Fahna kawai ki cika aikin ki “, Fahna kuwa jin an ambaci kuɗi har haka yasa ta amshi tayi jikin ta na rawa tace “an gama, kai dai kawai ka saka min number ka, kuma ka turo min hoton ka zaka ga aiki da cikawa, dan nasan ba macen da zata ganka ta ƙi ka”, haka kuwa aka yi, number yasaka mata, sannan suka cigaba da fira.



    (to masu karatu kunji dai yadda Fahna da Qaseem suka, aje)


Abun tambaya anan shine, shin ko Hajna zata karɓi tayin da Hajna ta mata.


  Mu haɗu a next chapter dan jin yadda zata kasance.



LOVE U ALL READERS, NAGODE MUKU SOSAI, INA GANIN SOYAYYAR KU, NIMA INA YINKU.



Haɗin guiwar :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya


ALQALAMI YAFI TAKOBI ????????.



COMMENTS PLSSS ????❤️❤️

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button