MADADI Page 81 to 90

Wani irin kuka takeyi mara sauti! tana so tayi magana amma ta kasa saboda kukan daya ci karfinta sai kawai ta kama hannunsa ta riqe gam a cikin nata….a haka suka isa inda Mmn Sajida take zaune….Jama’ar dake gurin duk suka zubo idanunsu suna kallonsu har suka karaso gurin, Mmn Sajida ta miqe tsaye cikin karramawa takewa Abba barka da zuwa sai washe bakinta takeyi tana fad’in ya shigo cikin gidan su gaisa sosai.” Abbah cikin kulawa yace.”Tayi hakuri ba sai ya shiga ba tunda a kan hanya yake, ya umarci Naja’atu ta shiga gidan ta dauki abinda take ganin zata dauka ta fito su tafi!
Mmn Sajida ta bita cikin gidan da sauri, shi kuma ya shiga nazarin gurin, matar na bukatar taimako ko ga yanayin sana’arta, barin gurin yayi saboda shi mutum ne da baya kaunar kallo a rayuwarsa sai yaje ya bude mota ya zauna yana jiran fitowarta…….Mmn Sajida na kuka Naja’atu na kuka a haka suka fito, suka shiga gidan Mmn Ladi sai gasu sun fito dukkaninsu su ukun suna kuka gwanin tausayi(sabo turken wawa ba) Mmn Sajida da Mmn Ladi sun shiga damuwa gami da alhinin tafiyar Naja’atu mutuka sun shaqu da ita mussaman Mmn Sajida gabadaya kasa magana tayi sai rintse hannun Naja’atu takeyi a cikin nata
A haka suka isa gurin motar, Abbah ya fito yana kallonsu sai kuka suke abun ya bashi mamaki sosai, yace.”Kuyi hakuri ku daina kuka ba wai kun rabu da itaba har abada ba insha Allah zata dinga kawo muku ziyara sa’i da lokaci.”
Mmn Ladi tace”Alhaji dole ne muyi kuka wallahi mun saba da yarinyar nan tana da hankali tana bani shawarwari masu amfani idan taga muna fad’a da mijina tayi ta bani hakuri tana kawo min misalai ni kam a rayuwar aurena ba zan ta’ba mancewa da wannan yarinyar ba.” Abbah Abbas ya shiga mamaki mutuka Naja’atunsa har ta iya sulhun aure kai alhamdullhi ashe zamanta a garin ya haifar da alkairai amma yaji dadin wannan labarin.
Mmn Sajida tace”Ballantana kuma ni da muke kwana a guri daya mu tashi a guri daya kullum cikin nuna kulawarta take a kaina da ‘ya’yana hakika ban ta’ba zama da mutum mai nutsuwa gami da iya mu’amula ba kamar wannan yarinyar kafin na saba da rashinta nasan zan sha fama.”
Abbah yayi murmushi mai ma’ana kafin yace.” Duk maganar da kuka fada akan Naja’atu naji dadinta kwarai da gaske inaso na sake jaddada muku kamar yanda na fada muku da farko cewar ba wai kun rabu da ita bane har abada insha Allah ni nayi muku alkawarin kawo muku ita a duk sanda ta bukaci hakan ina fatan zaku kwantar da hankalinku baku rabu da Naja’atu ba.”
Naja’atu share hawaye tayi ta kallesu murya na rawa tace”Mmn Sajida kamar yanda Abbana ya fad’a muku cewar muna tare har abada hakane ku daina kuka da damuwa kuna ganin kamar kun rabu dani wallahi bamu rabu ba, domin ba zan ta’ba mance alkairinku a gare ni ba, kun tallafe ni a lokacin da nake bukatar taimako baku qyamace ni ba kun jani a jikinki kun bani kulawa ni kuwa me zance muku ai idan na cika ‘yar halak baku cancanci na tsawar daku a rayuwata ba insha Allah zan dinga kawo muku ziyara kamar yanda Abbana ya fad’a muku.”
To jin haka dasu Mmn Sajida sukayi sai hankalinsu ya kwanta suka daina kuke kuken da sukeyi…Abbah ya bude mota ya shiga minti biyu ya fito hannunsa ri’ke da kudi yan dubu dubu sun kai talatin ya miqa wa Naja’atu da fad’in ta basu.” motar ya koma yana zauna yana qoqarin tashinta…..Mmn Sajida ta rungume Naja’atu tana zirarar da hawaye da kyar ta saketa Mmn Ladi ma tazo ta rungumeta sukayi sallama cike da alhini da damuwa Naja’atu ta bud’e mota ta shiga, suna tsaye a gurin suna daga musu hannu har sai da motar ta ‘bace daga gurin…..Sannan suka juya da mataccen jiki, Mmn Sajida hada ido sukayi da Dantalle daya zubo mata ido yana kallonta shima tamkar yayi kuka! Yarinyar da yake qulafuci ashe ba tsararsa bace, yaso ya yaudareta da kudi da kayan kwadayi ya biya bukatarsa sai ya lura ba wannan ne a gabanta ba, sai yanzu ya qara tabbatar da cewar yarinyar ‘yar manyan mutane ce ganin motar da’a kazo d’aukar ta yayi masifar sanyayyar masa da jiki da duk wani wanda yake mata kallon banza a gurin..
Abbah gabad’aya hankalinsa nakan driving din da yake sai dai kiraye kirayen wayar da yake shigowa wayarsa shine yake so yasa masa rashin nutsuwa a qalla an kirashi yafi sau ashirin bai daga ba, yasan dai labarin gizo baya wuce na’ko’ki duk wanda zai kirashi a yanzu zaiyi masa jajen abinda ya sameshi ne, wannan dalilin yasa ya’ki daga wayar kowa kawai ya mayar da hankalinsa kan driving din da yake…….Naja’atu kanta a qasa nauyi da kunya gami da nadama ya hanata kwakkwaran motsi! a duniya ita kuwa tana da masoyi wanda ya kai Abbahnta kuwa? Wai tambayar kanta takeyi….(To nima dai a ganina baki da masoyin daya wuce shi) Taji wasu hawayen na kokarin kwace mata data tuna zalintar kanta da tayi, yanzu data hakura ta zauna da auransa da tuni tana zaune hankalinta a kwance, da tuni ma wannan cikin dake jikinta nasa ne zata haihu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ba tare da fargabar abinda ka iya zuwa ya dawo ba, yanzu ya za tayi da d’an Bash idan ta haifeshi? wane namiji zata aura wanda zai ri’ke mata d’anta! hawayen da take ta kokarin dannewa suka shiga zuba a kumatunta…..Inama ace ana dawo da abinda ya wuce a baya data gyara kuskuranta, ita da kanta tasan ta aikata kuskure mai muni wanda har ta mutu ba zata daina nadama ba…………..Wayar da yake ce ta dawo da ita hayyacinta.