TAYI MIN KANKANTA COMPLETE HAUSA NOVEL

TAYI MIN KANKANTA 38

 ???????????????????????????????? *TAYI MIN ƘANƘANTA*

????????????????????????????????

*Zahra Surbajo*

*SHIMFIƊAR AURENA,na fara posting free page,wanda zanyi daga ɗaya zuwa page 15 duka free,kiyi ƙoƙarin biyan kuɗinki akan kari,kar ayi babu ke,ze nishaɗantar,faɗakar,wa’azantar,daku masu karatu,shikaɗai ne irinsa beda na biyu, shi ɗin na musamman ne 500 kacal*

*Zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044 a turo shaidar biya tanan*

*masu tambayar ta littafi,ko sabo ko tsoho shima ki biya 500 din zan turo miki,masu cewa insasu a group shima ki biya 500 ɗin zan saki????*

*38*

A harabar gidan ya adana motarshi sannan ya shiga falon,da sallamarsa,bakowa aciki hakanne yasa ya ɗauka suna ɗakin mummy,

Da saurinsa ya ƙarasa falon mummyn,zaune take kan kujera,Zahra tayi matashin kai da cinyarta,suna kallon news,wanda ita zahran sam bata fahimtar komai hankalinta na kan yayan nata.jinshi shuru da tayi se duk kishi ya taso mata.

Sallamarshi ce tasata saurin miƙewa tana duban hanyar daya shigo,da saurinta ta nufeshi,dan ta mance da mummy dake gurin.

Shima itan kawai yakeson gani,dan yinin da yayi babu ita duk ya takura,hannayenshi ya buɗe mata ta shige,ya maida hannun ya rungumeta,wata ajiyar zuciya suka saki atare,cikin shagwaɓa tana ɗan dukan ƙirjinshi tace”yaya shine ka tafi kabarni ko?”

Ɗago haɓarta yayi ya tsura mata sexy eyes ɗinshi ɗan nazarinta yayi na ƴan daƙiƙu,sannan yace yana shafa lips ɗinta”baby me ya sameki bayan bana nan?ina can jikina ke bani kamar kina cikin damuwa kuma gashi nazo naganki ba yadda na tafi na barki ba,oya tell me”ya ƙarasa maganar yana ƙara matseta a ƙirjinshi.

Ƙara narke mishi tayi,cikin kukan shagwaɓa,tace”ba daddy bane yasako wani turare in naji ƙamshin se amai yay ta zuwa min,wuni nayi inata amai”ta ƙarasa maganar kwalla na biyo mata fuska.

A gigice  yace “what!!!shi daddyn meyasa yasako abinda bakya so,yabarmin ke kinata amai,da mummy ce ze sako ne?”ya ƙarasa maganar yana shafa gadon bayanta.

“ina fa ze sako rasa kunya,”mummy dake zaune kamar gunki ta bashi amsa.

Da sauri yakai dubansa gunta shi se yanzu ya ganta tun bayan shigowarshi,akunyace ya saki zahra ya ƙarasa gaban mummyn ya durƙusa yana sosa ƙeya.

Itama zahran bayanshi taje ta rakuɓe tana leƙo mummyn.

Miƙewa mummyn tayi,tana  murmushi tace”to daddy de besan matarka nada cikin da beson ƙamshin turarensa shine yasa ya sako,ay masa afuwa”

Da sauri suka dibi junansu sannan suka kai dubansu gun mummyn,bakin Hammad har harɗewa yake yace”mummy nufinki zahra nada ciki ko me kikeson kice?”

“kwarai tana da ciki,ɗazu na dibata na tabbatar da hakan,se akula iyayen rawar kai,kuma ku tashi ku bar mana gida,dan Alhaji yasamu sukunin saka turaren dayakeso batare da anga bekensa ba”ta ƙarasa maganar cikin sigar zolaya.

Wata irin runguma hammad yayiwa zahra hawaye na biyo idonsa,ya kasa cewa komai,se hawayen da yakeyi.hamdala kawai yakewa Allah,daya nuna masa wannan lokacin da baze taɓa mancewa ba.

Rarrashinshi zahra take da kyar yayi shuru ya ɗago idonsa yana kallonta,dariya yake ya kamo fuskarta yace “tnks you baby,tnks you,kim bani farinciki da yawa arayuwata wanda baki baze iya gode miki ba”

Kai kallonshi yayi gun mummy dake tsaye tana kallonsu cikin so da ƙaunar ganinsu atare,yace”mummu ladan albishir da kikamin , zan siyo miki G-wagon 2020 ladan albishir”ya faɗi yana murmushi.

“Allah yay muku albarka ku tashi ku tafi gida kar dare yayi,zan ayko muku da breakfast”

Miƙewa sukayi,zahra ko wacce tunda akace tana da ciki wata mahaukaciyar kunyar mummy ta kamata,se ɓoyewa take a bayan hammad.

Mummy wucewa tayi ta ƙyalesu,ay tana gama ficewa Hammad ya manna bakinshi kan na zahra yashiga kissing da saurinsa kamar zaa kwace masa ita.

Seda taga yaƙi sakinta ne tasa mishi ɗan kukan shagwaɓa,da sauri ya saketa yana faɗin”am sorry baby,muje gida ingaisa da babyna”yana kaiwa nan yaja hannunta suka fice bayan ta ɗauko mayafinta.

Ko a mota hannun Hmmad nakan cikin zahra yana shafawa  sosai ƙaunar zahra da cikin jikinta ke ƙara ratsa zuciyarshi.

Muje zuwa

Surbajo for life.

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button