HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 7

 *HALIN GIRMA*            7

*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107*  

I’m on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

***

Kukan ta ne yake karuwa Mama na tsaye a kanta, ta ja tsaki tace

“Bana son shirman banza kina ji na? Akan namiji zaki zauna kina rafka wannan kukan kamar uwarki ce ta mutu ko ubanki?”

“Mafita nake so mu samawa kanmu, saboda anga zaki huta shine aka shiga aka fita ake so ayi mana bakin ciki, idan ba haka ba, me ya kawo wadannan zantukan?”

Cikin kuka tace

“Wallahi Mama nasan Iman ce taje ta samu Gaji da maganar tunda dama ita yace yana so ai, shine dan taga wanda yazo wajen nata talaka ne shine zata min bakin ciki, toh wallahi babu wanda ya isa ya hanani auren Bashir, naji na gani kowanne hali ne dashi.”

Shiru Maman tayi tana kallon yar ta ta, idan har ta bari maganar ta sha ruwa akwai matsala, sanin cewa Zeenat din ba wani farin jini bane da ita, dama dai jamaar Iman din ne tun farko take sanin yadda zatayi, dole ta san abinda ya kamata amma duk da haka ba zata nunawa Zeenat din komai ba 

” Kina jina? Ki tashi ki tafi dakin ku, ki daina wannan kukan tunda ba ubanki bane ya mutu, zan san yadda zanyi komai ya daidaita.”

Da bayan hannun ta ta goge kukan, ta fice tana rangaji, tana sake kudurewa a ranta babu gudu babu ja da baya a auren ta da Bashir din.

  Tana isa daki ta tarar da missed calls din sa, ta bi kiran da sauri tana sake daidai ta kanta.

” Gani a waje.” Yace tana dagawa.

” Mu hadu a bayan layi akwai matsala karka zo gida.”

” Me ya faru?” Yace a kidime.

” Babu komai gani nan zuwa.”

Kashe wayar ta, tasan zai ta tambayar ta menene gwara kawai taje suyi magana su sama wa kansu mafita dan ba zata iya hakura dashi ba.

  

Ficewa tayi ta kofar kitchen bayan ta gyara fuskar ta, ta bar gidan cikin sauri tana tsoron haduwa da Ya Habib ko wani.

  A chan bayan layin ta hange shi jikin motar sa, a tsaye yake yana ta jijjiga jikin sa daga gani baya cikin nutsuwar sa, tana isa ya juyo da sauri.

” Lafiya baby?” Yace yana riko hannun ta. Kuka ta saka da sauri yace

” Na shiga uku, me ya faru?”

” Abba ne yace wai na rabu da kai, wai yayi bin…”

” Shisshsh…” Yace da sauri yana dora hannun sa a saman bakin ta

” Kinsan dai hakan ba gaskiya bane ko? Sharri akayi min ko menene akace domin a hana mu aure, duk wanda ya yi min wannan sharrin na bar shi da Allah kawai.” Yace yana girgiza kansa

” Shikenan yanzu rabuwa zaki dani? Nasan rayuwata shikenan ta kare, idan har zaki iya yarda mahassada su shiga tsakanin mu, bakya so na baby, rayuwata shikenan ni.”

” Ni ban yarda da duk abinda akace ba ai, kawai sharri ne na sani, amma ya zanyi da Abba? Bayan shi din kaifi daya ne akan maganar sa.”

” Dan Allah Zeenat karki yarda a raba mu, wallahi Ina sonki , bansan ya zanyi da rayuwa ta ba idan har baki aure ni ba.” 

Hawaye ya fara yi tayi saurin sa hannu ta goge masa

“Zanyi duk yadda zanyi, ba zan bari a raba mu ba…”

” Da gaske? Kinyi alkawari?”

” Nayi maka alkawari.”

” Dan Allah karki saba alkawari dan Allah, ki taimaka wa rayuwa ta, kinji?”

” Karka damu.” Tace tana jin wani karfin zuciya, 

” Ba zan taba yarda su yi min abinda bana so ba, Kai nake so kuma duk yadda kake ina son ka a haka.*

“Nagode nagode baby, in sha Allah ba zakiyi dana sanin amincewa dani ba.”

Zatayi magana wayar sa tayi kara

” Sorry.” Yace mata kafin ya daga yana rage volume din wayar sosai

” Malam tun dazu nake jiran ka, ka dawo min da mota zan fita, wai ina ka tsaya ne?”

” Gani nan yanzu in sha Allah.”

Ya kashe kiran ya ce

” Baby bari naje, urgent call daga Baba, zamuyi waya kinji?”

” Tam shikenan.” Tace a sanyaye

” Yawwa ga sakon ki…” Ya bud’e murfin motar ya fiddo da ledoji, hannu tasa ta karba tayi godiya, ta juya ta soma tafiya shi kuma ya shiga motar ya tada ita da sauri ya bar wajen, yasan ba zasu kare kalou ba da ita, amma kuma hakan shine kadai zai kankaro masa mutuncin sa.

***Daki ta koma ta ajiye ledar bayan ta bud’e taga ice cream ne da Pizza, sai charger waya da yake ta lalace ta ta, sai wasu tarkachen alawoyi. Bata taba komai ba sai charger din ta jona wayarta a jiki sannan ta fice zuwa bangaren Gaji dan ta samu Iman a yi wacce za’a yi.

   Iman din ce kuwa kadai a falon tana karanta hisnul muslim. Sai ganin mutum tayi a kanta, bata tanka mata ba ta sauke kanta ta cigaba da karatun ta kawai.

“Saboda kina bakin ciki kin samu fakiri talaka shine zaki kai munafurci kice Bashir bashi da hali ko?”

“Wacce irin magana ce wannan Zeenat?”

” Malama karki pretending kaman baki sani ba, idan bake kika fad’a ma Gaji wata magana akan Bashir ba waye ya samu Abba ya fad’a masa Bashir bashi da hali me kyau?”

Tashi tayi zaune tana kallon ta, ta girgiza kanta kawai kafin tace

” Kinsan bani da lokacin batawa akan irin wadannan maganganun, dan haka please bana son maganar.”

” Zaki ce bakya so mana kina min bakin ciki, toh wallahi sai dai ki mutu da bakin ciki amma aure na dashi babu fashi, kije chan kiji da wanda zaki aura, mutum kamar shi ya kawo talauci duniya.”

Tashi kawai tayi ta bar falon zuwa bedroom din Gaji dan ba zata iya irin wannan shirmen na Zeenat ba, sai dai da gaske maganar ta taba ta, har taji ta rasa gaba daya walwala da farin cikin ta, kwanciya kawai tayi ta rufe idon ta tana hasaso rayuwar ta nan gaba!

***Cikin shigar Khaki pants da wata jibgegiyar rigar sanyi da ya saka a saman armless rigar sa ya fito, kansa da yake a kwance yasha gyara ya tsaya yana sake dubawa a katon mudubin da yake ajiye a falon, yasan Takawa zai saurare shi ya kuma bi abinda yake so sai dai baya son ko kad’an karya ko wasa ya shigo a cikin maganar auren sa. Kallon kafar sa yayi, sai ya koma ya sauya takalmin zuwa wani daban sannan ya fice yana tura hannun sa cikin aljihun dogon wandon nasa.

   Suna tsaye k’yam suna jiran fitowar sa, kowanne su cikin shigar da take nuna shi din waye, bud’e masa motar akayi da sauri ya fad’a yana makala bakin glass din sa yasan yau zai same shi a wajen hutawar sa, in da ya dace da maganar da zasu tattauna, shiyasa ma yayi shigar sa da yasan Takawan bazai masa surutu ba, dan ya riga ya san shi, ko yace kowa ya san shi da tsanar manyan kaya musamman a lokacin zafi sai yace wai takura masa suke.

   Da yake sun san in da zasu, kai tsaye suka wuce dashi Family house din, in da Takawan ke hutawa a duk ranaku irin wannan ba tare da shigowar wani shaani na mulki ba. Iyakar abinda ya shafi kansa da iyalin sa kawai yake tattaunawa a rana cikin saukakakkiyat shiga da ba zaka taba cewa sarki bane duba da ko yaushe yana nannade cikin rawani da manyan kaya.

   A kofar wajen motocin nasa suka tsaya, ya balle murfin tare da me bud’e masa ya fito yana kallon ko ina na harabar gidan. Kansa sanye da hular sanyi ya cire glass din idon sa ya shiga takawa zuwa ciki. Gaisuwar da ya tsana ya dinga kokarin kaucewa har ya dangana da inda takawan yake ya hange shi a zaune a cikin wajen yayi matashi da pillow yana kallon yadda yan yaran da suka kasance jikokin sa ke wasa a wajen.

   Sarkin dogarai ne ya fara ganin shi,ya washe cikin farin cikin ganin shi yace

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button