NOVELSUncategorized

KWARATA 60

???? —— 60

       Ɗan bubbuɗawa nayi na lalleƙa gaskiya Yazeed baida hankali wannan irin haukan duk me ya jawoshi ? Duk abinda ya shafi na sakawa a jiki babu abinda Yazeed bai sako ba , turaruka mayuka gyaluluwa takalmi jikkuna materials masu kyau da tsada lessess shaddoji masu tsada atamfofi ƙarshen iskanci hada breziya da fants ondy da sabuwar waya cikin kwalinta mai tambarin apple a
bayanta , nima dai ya zubo kuɗi wanda saida suka bani tsoro ,

     Salati nayi naja baya da sauri banma sake gigin ko kallon inda kayan suke ba bare na sake tunanin taɓasu , ɗakin Kaka na nufa na samu tana waya da Inna wuri na samu na zauna cike da mamaki , ina zama tace ga Maryam nan ta faɗi maganar tare da miƙomin wayar ,

    Ansar wayar nayi tare da kallon Kaka ita tana san lulluɓi bata san ɗaura kallabi sai a wani fiddo kunne waje kome hakan yake nufi oho , Hajiya Inna haka na faɗa a dai² lokacin dana kara wayar a kunne na , ya kike ? Lafiya qalau wai yaushe zaki dawo ? Idan na dawo me zan miki ne ? Haba kema da Allah ki dawo Inna , zan dawo ai bai gama abinda yakeyi ba , waye ? Mijina mana , cikin in ina nace Inna miji……? Ey mana yanzu aure kikayi saboda Allah ? To kar inyi ? Wani irin kishin Babana naji ya kamani nace kawai sai kikayi aure haba Inna ke me zakiyi da aure da Allah ? Dariya tayi sosai naji tana cewa Sultana ce ,

      Sultana zaku gaisa da Alhaji , nace ki gaishe shi sallah zanyi , ina faɗin haka na maida ma Kaka wayarta na shige toilet nayo alwallah sallah magrib bayan na fito ɗakina nai tahowa ta , ina shigowa naji wayata na tsuwwa da sauri na isa wurin wayar , murmushi nayi tare da ɗaukar wayar cikin farin ciki,

      Na koma saman gado na kwanta cike da shaƙun so zuciyata nata tsumama da soyayyarshi nace hello , ke yarinya me kike nufi ne yau baki kirani ba ko kinyi fushi da nine ? Murmushi nayi tare da ɗan murginawa na lumshe idanuwa na gaskiya ina jin daɗin muryar Dikko tana sakani ciki wani irin yanayi dani kaina bana iya ganewa , nima irin abunda yakemin nayi cewa zanyi sallah idan na gama zan kiraka , tou kimin addu’a , nace me zan roƙar maka , ki roƙarmin Allah yasa miki soyayyarta wadda bata gogewa har abadan duniya , ubangiji yasa nine mijinki , duk wanda baya san aurenmu Allah ya sanyaya masa zuciyarshi shi da kanshi yace Dikko ka auri yarinyar nan kana santa tana sanka , 

      Nace zan maka amma ni bazan aure ka ba , murmushi yayi yace ni ko zan aureki in Allah ya yadda kuma inaji a jikina lokaci yana kusa , ai nace bazan aure ka ba , Ey dama ai nine zan aureki bake ba , kinsan Allah ki daina min abinda bashi da kyau idan ba haka idan na aureki duk abinda kikai min saina rama , ka rama idan na aurenka mana…

Haka kika ce ? Nace Ey , aiko yarinya zaki ga ramuwa hada ta gayya kice zaki je gida in koma daga gefe in haɗe rai ince baza ki ba , kice dan Allah…… Wata magana yaso yayi amma ganin nayi masa “yar ƙarama kamar yadda yake faɗa saidai yayi dariya yace An mata Allah dai yasa ke rabona ce , a cikin zuciyata nace amin tare da tsinke kiran….

        Wani irin ihun jin daɗi nayi na miƙe saman gado nayi rawa Allah yasa haka mutumina Allah yasa muyi aure , ina sanka ׳………….. Da tsalle na sauko daga saman gado ina rawar jin daɗi , rumgume hannuwana nayi nai juyi An mata…. Wai me yasa kake cemin An mata……? Banda mai bani ansar wannan tambayar….

          Murmushi Dikko yayi tare da gyara kwanciyar shi yace An mata kenan kinga irin yarintar taki wai zakimin addu’ar amma baza ki aureni ba , hmm yarinya kenan kinaji da ƙuruciya sosai har yanzu kanki ɗanye ne amma zan dafa miki shi gaki ga Dikko ubangiji yasa nine mijinki am3n ,

        Har yanzu Al ‘ Ameen bai dawo ba , likitoci suna ta bakin ƙoƙarinsu amma shiru kake ji kamar an aiki karuwa ɗakin kwarto , yauma abiyar zaman Momy ta kira Dady ta faɗa mishi har yanzu fa Al ‘ Ameen babu wani ci gaba sai ƙasa yake ƙarayi kuma Momy ko ganinshi bataje ba , kuma ta sani sarai ɗan ta yayi wannan iskancin tunda a gaban idonta ya doki Al ‘ Ameen bata ce komai ba tunda daga wurinta ya fito duk yadda akayi ma itace ta tiroshi sai Dikko ya zauna yaita iskanci amma ba’a iya ma yaro magana kamar ɗan ido , 

     Tuni nace ka kaishi gidan mahaukata sai kace ɗanka lafiyarshi qalau yanzu mai hankali zaiyi abinda Dikko yayi ? Cikin ɓacin rai Dady yace ni ban haifi mahaukaci ba , lafiyar Babana qalau kuma Maryam babu yadda za’ayi tasa Babana ya daki wani tunda tasan abinda yake damunshi , duk dai abinda mutum yayi shida Allah kuma ba Maryam aka cuta ba ni aka zalinta duk mai sa hannu a lalurar Babana nakai ƙararshi wurin ubangiji kuma sai Allah yayi min hisabi dani dashi wallahi ban yafe ba kuma bazan taɓa yafewa ba , yana kaiwa nan ya tsinke kiran ya fara kiran Dikko.

      Gaisawa sukayi bayan ya ɗauka Dady yace Babana har yanzu me kakeyi ne ? Dady ni ina Abuja , tou duk abinda kake ka kasance tare dani idan Allah ya kaimu gobe na faɗa maka , insha Allah , me ya haɗaka da Al ‘ Ameen kayi mishi duka haka ? Wai bana hanaka wannan doke²n ba ? Badai zaka zauna da rayuwarka lafiya ba ko ? Sai kayi ta abu ana dan ganaka da zararre ,

     Cikin kwantar da murya yace Dady kasan bana iya sarrafawa , tsohon laifi ne na daɗe ina ba zuciyata haƙuri jiya ne taji bata iyawa shi yasa haka ya faru , Allah ya kyauta ya baka lafiya , ubangiji ya yaye maka abinda yake damunka , da am3n ya ansa saida Dady yayi mishi nasiha sosai sannan yace kuma karya zo da kowa yazo shi ɗaya yace insha Allah , cike da soyayyar Dikko Dady ya ajiye waya yana mai tausayin ɗanshi da lalurar dake damunshi , gashi cikakken mutum mai cikar zati da ƙwarjini amma saboda haukan kishi na mata an birkita mishi kwalwar ɗa , matsalar dai kawai yayi fushi idan har yayi fushi tofa nan ake samun matsala danma ana ta roƙon Allah , kuma roƙon Allah gaskiya ne baya faɗuwa ƙasa dan ubangiji maji roƙon bayinsa ne….

    Dikko yana da mutunci kuma yana da kirki Allah yasa mishi tausayi amma yafi tausayin mata a rayuwarshi , kuma tun kafin matsalar nan ta sameshi bai ɗaukar raini kuma da an taɓoshi sai anji babu daɗi bai iya zuciya ba haka kuma sai laifin wani ya shafe wanda baisan anyi mishi ba , dariyar mugunta dama haka Allah ya halicceshi tun fil’azal baya dariya kuma shi bai cika murmushi ba ,

      Koda Dady bai samu namiji ba ya tashi hankali sosai kuma duk matanshi kowa addu’a take Allah yasa itace zata haifo , shi kuma a tunaninshi duk wacce ta haifa duk ɗaya tunda suma “ya “yanshi mata baice baya sansu ba kuma kowa tana da , amma tunda aka haifi Dikko sai wutar kishi taita ruruwa sai jefe² har suke ganin kauda Dikko daga duniya shine kawai kwanciyar hankalinsu , tun yana ƙarami suke asirinsu kuma basu gaji ba daga ƙarshe aka tura mishi aljannu su shanye jininshi ya mutu , yasha wahala sosai babu wanda yayi tunanin zai sake rayuwa amma ubangiji yayi alƙawarin rayayye ne , 

Ganin ba’a samu nasarar hakan ba yasa akayi amfani da fushinshi wurin saka wani fushin idan har yayi zuciya sai ya fita hayyacinshi yayi ta hauka bayaji baya gani ya riƙa kiran saiya kashe sai yabi takan mutum da mota , tou kalmar kisan itace ba’aso yana faɗa idan yana fushi dan idan yace zaiyi kawai sai yayi yake samun natsuwa , to idan yace saina kashe ka daga nan yake tafi sai ya ɗauke wuta ya faɗi , tanan ake neman sa’ar sa ake farautar numfashin shi a haka aljannu ke so suyi nasarar raba gangar jikinshi da ruhinshi su shanye mishi jini ya mutu…. Shi yasa ya faɗawa Sultana idan yayi fushi bashi bane ba ta kiyayi fushin shi saboda baya da kyau , tayi ta haƙuri dashi har Allah ya bashi lafiya !

      Ana ta neman taimako dai , wannan magungunan da ake mishi amfani dashi na cikin baki dana shaƙawa abokin Dady ne ya nemosu dan ya tausayawa Dady akan lalurar Dikko saboda Dikko ke ciwon amma Dady ke jinyar bawai jinya ta kula ba , jinyar kar Dikko ya mutu shi yasa duk abokanan shi suka miƙe suka tayashi neman taimako , kuma har yanzu ba’ar nema ba , yanzu haka ma idan Dikko ya samu Dady a inda yake idan ya gama ganin likita zai wuce saudiyya suyi umara tare sai ya dawo dashi inda wani amininshi yace mai maganin yace sai an kawo mishi Dikkon , dan da Dady ya bari saiya dawo amma haukan da yayi jiya yasa Dady yace ya sameshi.

        Dikko ganin Sultana bata da niyar kiranshi yasa shi ya kirata , har na fara bacci kiran wayar shi ne ya tashe ni , cikin gigin bacci na ɗauki wayar na gaishe shi da muryar wanda bacci yafi ƙarfin shi , cikin murya mai nuna da fushi yace har yanzu baki gama sallar ba ? Bacci ya riga yafi ƙarfina kawai na kashe wayar banma san na kashe ba , ƙara kira yayi har yanzu bacci bai sakeni ba , dakel na ɗauki wayar na ɗorata a saman kunne nace inajinkan , ni zaki kashe ma waya har kin isa in kiraki ki kashemin waya An mata……?

      Da sauri na buɗe idona dan namayi tunani ko a mafarki nake wayar wallahi , yi haƙuri don Allah wallahi na fara bacci ne tsoki yayi tare da kashe wayarshi gaba ɗaya , da sauri nabi bayan kiranshi amma har ya kashe wayarshi akace a kashe take….

          Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un haba ina amfani halin Dikko dan Allah anyi mutum rayuwarshi babu uziri , kwata² bayamin adalci bayan yasan da kaina ina kiranshi , shi so nawa na kirashi bama ya ɗauka tou idan ka kira kai baka cika Dikko ba , kuma nima har abadan duniya bazan sake kiranka ba da Allah can tsamiyar biri dakai mtsww….

      Komawa nayi nai kwanciyata cikin ɓacin rai , shi wannan Dikko baida haƙuri ko kaɗan sai zafin kai shi ɗan zafin zuciya ko an faɗa maka bana iya rabuwa dakai , ko zan ragu ne idan na ɓata dakai duk abokanka ma sunfi ka kirki masu haƙuri kaiko komai fushi duk namiji shi ke sarrafa fushin mace amma kai ƙato dakai saini zanyi ta haƙuri dakai ? To bazanyi haƙurin ba kuma an ɓata babu ranar shiryawa…..

       Wuri ɗaya ya ƙurawa ido yana kallo , ajiyar zuciya ya sauke mai tattare da ɓacin rai , murmushin ƙarfin hali yayi a bayyane yace wai Allahna , wai….. Wayyo ya ƙarasa yana mai kwanciya dakel cikin yanayi mai nuni da wahaltuwa , 
lumshe idanuwanshi yayi ya ƙara cewa wai…….. Wai Allahna , kukan Sultana ya riƙaji a zuciyarshi idonshi ya cika da hawaye yayin daya tuno yadda yayi da ita a safiyar daya anshi budurcinta ta ƙarfi da yaji ya ɓata mata , gangarowa hawayen yayi daga cikin idonshi saida ya sake wai….. Wayyo har yanzu idonshi a rufe a zuciyarshi yace Allah na tuba ׳ , Allah ka ƙaddara aure na da “yar yarinyar nan ya ubangiji kasa An mata rabona ce duk abinda zanma yarinyar nan nidai nafi so kawai na aureta ta samu natsuwa dani , ya Allah kaji ƙaina ka tabbatar da auren mu , zan nunawa An mata tsantsar soyayya mai tsafta zan gatanta ta kuma zata samu natsuwa daga gareni mai sa natsuwa ,

       Ashiru ya kwalawa kira bayan ya samu natsuwa , da sauri ya shigo cikin girmamawa yace mai gida , ran Dikko a haɗe yace wani tunani nayi me kake tunani game da Yazeed da yace zaije zance…..? Cikin girmamawa Ashiru yace mai gida kila wasa yakeyi , 

     Murmushi Dikko yayi tare dayin shiru yana nazari , bayan wani lokaci yace tabbas sai yaje wallahi sai yaje wurin An mata , nasan halin Yazeed ciki da waje , yanzu nayi wani tunani idan ka fahimci rayuwarshi ya cika leƙe² aiko idan har ya leƙo An mata saina tada katsina da bala’e ,

      Tun bansan meye iskanci ba nakejin kalmar iskanci a bakin Yazeed , idan kayi tunani goruba ba majalissar shi bace tunda yaga An mata ranar dana daketa ya dawo da zama gidan nan , jinjina kai Dikko yayi yaci gaba da cewa lallai akwai abinda zai faru , miƙewa yayi tsaye yace zafa a samu matsala ya ƙarasa maganar yana ma Ashiru wani irin kallo , da sauri yaja da baya yana cewa mai gida haka bazai faru ba , 

      Dikko yace abun yakemin yawo a zuciya yace An mata ta cika zama ɗaki kamar mai jego , yawan zama da hijabi kamar mai takaba , ya gajiyan hawa doki ko zaki hau na bankwana , kyautar zobe a maimakon kuɗi kamar yadda sauran sukayi mata , duk haka yana nufin wasa ne…..? Me yasa su sauran basuce haka ba ? Mahaifiyar An mata bata nan tayi tafiya zuwa Dubai ita da mijinta da mukayi waya da ita nace sai ta dawo zan dawo da An mata , abinda yasa na mayar da ita shine ,

      Washe garin ranar dana bata kashi su Yazeed su suke riƙeni lokacin dana bigawa An mata kai da bango , tayi ƙara sau ɗaya mai tsananin tayar da hankali , ihunta shine ya jawosu suka shigo ciki da gudu a lokacin ita kuma ta suma….

     Gaba ɗayansu sun riƙeni , ni kuma ina zabura cewa saina kasheta , kowa haƙuri yake bani hankalin kowa yana kaina amma idon Yazeed yana saman An mata , abinda tayi min suka fara tambaya ina cikin wani yanayi saina ce na hanata fita shine ta fita maza suka daketa to da wani ya daketa gara ni da hannuna in kasheta , ko ina cikin yanayin fushi duk abinda akeyi ina sane kuma kar nake bana mantuwa , tabbas naji Yazeed yace wannan tafassar fa…….?

     A dai² lokacin na kwace na fita daga gidan , ranar a gidan ya yini har 1:21am yana nan a tunaninshi zan tafi baisan tunda na dawo da An mata goruba na daina kwana gidana nake kwana tare da ita , ita kanta bata san gidan nake kwana ba saidai kawai ta ganni da safe , Yazeed yace min DK yaushe zaka wuce ne ? Nace masa aini bana fita sai kowa yabar gidan nake fita , sai yacemin tare zamu fita , nace masa bana zuwa da kowa kuma bana fita da kowa , yace zai bini a haka dai saida nayi mishi gatso² ya tafi , misalin 2:09am ya kirani na ɗauka yace wai na wuce ko ina goruba ne ? Nace masa ya akayi ne ? Murmushi Dikko yayi tare da cewa waini za’a ɗauka sakarai bayan har “yan cikin Yazeed ina kallo.

      Kallon Ashiru yayi sosai tare da buɗe duk girman idonuwan shi masu ba mutane tsoro yace , kawai Yazeed cewa yayi wai “yar yarinyar nan nake tausayi an barta ko yata ƙara jin jikinta ne ? Sakaran banza sai na rubza shi a rami mayen kuma saiya faɗa , { bai faɗi maganar da yayi da Yazeed ba haka kawai yacewa Ashiru } Dikko yaci gaba da cewa ,

Da safe sai An mata ta fito palo ta sameni tana kuka , bata yafe ba duk wanda yaji mata ciwo a gefen fuskarta , na kirata tazo kusa dani na bata haƙuri kuma na lallasheta ta saki ranta mun fara magana Yazeed ya shigo , ni kaɗai nasan fassarar kallon da yayi mata , ta tashi na zaunar da ita saman kujera , kallon da yake mata yasa nace ta ɗauki makullin mota ta ɗauko mana abinci , tana fita ya matsamin muka fita , bayan takai miya ta kwanta yasa na fiddota , nayi niyar zuwa da ita wani wani taron da zamuyi a ranar daka maida ita gida bayan shine ya matsamin naje , na yadda yace inje da An mata nace masa bazani da ita ba , hmmm waini zaima wayau sai ya zuƙe da matarshi kaza ² ya kawo wani makirci ya raɓa , da naga zai maidani wani ruwan tsakar dare kawai na maida An mata gida wurin kakarta bayan na faɗawa mahaifiyarta , yaga gidan shine yace zaizo zance , kawai na ɗauka yana wasa ne amma naji a jikina kamar yaje , ko zaije Allah ya tsallake shi a tarko fitinata ,

       Ashiru yace mai gida anya zaiyi haka duk halakcin da kayi mishi , Dikko yace manta da wannan matsayin dana ajiyeshi daban kuma idan ya kuskura yace zai shiga rayuwar An mata zanci ubanshi ne kawai kuma dan naci mutunci shi bazaisa na rabashi daga inda na ajiyeshi ba jeka kawai , fita Ashiru yayi Dikko kuma toilet ya shiga dan yayi wanka…..

       Ashiru kuma tunani yake akan maganganun Dikko idan ko har Yazeed ya shiga rayuwar Sultana za’a samu matsala , kuma yayi ƙaton butulci dan Dikko ya suturashi ya farfaɗoshi daga masifar talauci ya kwato mishi “yan cinshi a cikin abokansu , yana zalincin Dikko amma dake shi abun duniya bai rufe mishi ido ba bayajin komai , domin Yazeed yana wulaƙanta dukiyar Dikko da ƙeta an faɗawa Dikko sai yace ai idan Allah ya baka arziƙi tou ba naka bane ba kai ɗaya , yace kuɗinshi na kowa da kowa ne duk yadda Yazeed ke facaka da kuɗin Dikko baya mishi magana kuma ko abokansu da sukayi ma Dikko magana ya kori Yazeed daga dukiyarshi karya talautashi kamar yadda ya lalata arziƙin mahaifishi Dikko cewa yayi ko haka ya tsaya ya daina neman kuɗi nan da shakaru dubu baya talauci….

       Ajiyar zuciya Ashiru yayi tare da cewa gaskiya mai gida yana da haƙuri addu’a yayi Allah ya tsare arziƙin Dikko domin shi bangone ga duk wanda ya raɓeshi dan Allah yayi ma Dikko kyauta kuma kyauta mai ɗauke lumfashi hannunshi buɗe yake shi yasa Dady ke cewa yasan koya mutu Dikko zai zama uba ga “yan uwanshi , gaskiya Dikko yana da kirki sosai saidai matsalarshi fushi sai mugunta da ƙeta…

      Yazeed abokin Dikko ne , kuma shima Yazeed ɗin babanshi cikakken attajiri ne sai Allah ya kawo mishi karayar arziƙi kuma duk Yazeed shine silar lalacewar komai na ubanshi dan shima yana harkar wasan danbe ya daɗe sosai a cikin harkar , da abokai suka ga bashi da wani kuɗi a hannunshi sai suka cireshi daga cikinsu shi kuma lokacin Dikko baya nan…..

     Bayan ya dawo daga tafiya yaga baya ganin Yazeed daya tambaya sai sukace gaskiya DK mun cire Yazeed a cikinmu , bashi da ko sisi zai zama mana damuwa , Dikko yace ba’a rayuwa haka kar a barshi rashin kuɗi yasa ya shiga wani hali na daban gaskiya a ceto rayuwarshi dan duk wanda ya saba mu’amula da kuɗi idan ya rasa yana samun damuwa , a tausayawa duk wanda ya samu ya rasa….

      Sai sukace sudai basa zama dashi gaskiya zai rage musu matsayi ne kuma ana ganin girmansu a gari duk wani matashi addu’a yakeyi ya zama kamarsu sai kuma su fara rage zafi gaskiya basa iyawa , amma sai kuma suka ɓoyewa Dikko Yazeed yana wasan danbe…..

         Shine Dikko ya farfaɗo da rayuwar Yazeed ya bashi manager a wani companyn shi , yaga kuɗin banza ya shiga daddagar musu uwa , mutane yadda suka ga Yazeed lokaci guda ya zama mutum yana wulaƙanci da kuɗi sai sannan suka cewa Dikko ai yana wasan danbe Dikko yace ai basu faɗa ba shi kuma ya wuce wurin dan idan ya tafi baya dawowa , duk wulaƙancin da yakeyi da kuɗin Dikko shidai Dikkon bai taɓa nuna mishi komai ba , koda ya fara mai gida Dikko yace baya so ya kirashi kamar yadda ya saba tun farko ,

      Sai ki haɗa mace 20 zakiji duk sunce su “yan matan Yazeed ne , ɗan neman matane na bala’e , duk macen daya gani saiya lasa ta , tunda yaga Sultana tsutsar masifar jarabarshi ya tashi kuma ya ɗana mata tarko itama so yake ya lashe ya wuce , idan har mace ta kuskura ta faɗa tarkon Yazeed nata ya ƙare……

        Cikin farin ciki na wayi gari , a murnace nake ta huɗɗoni na sai shiri nake na tafiya Daura , tun ina wanka ake cemin nayi baƙo a waje , dan gaskiya rayuwar gidansu Inna babu takura zan fita duk lokacin da nake so in dawo babu wani tsanani , idan zan fita Kaka tana nan zatace min Allah ya tsare kuma idan na dawo taga dawowa na zatamin sannu !

       Ina fitowa daga wanka hijabi na saka nayi waje , a harabar gidanmu naga motar Dikko , da farin ciki nayi wurin motar ina zuwa Ashiru ya sauke gilashi ya gaisheni , ansawa nayi cikin halin ko in kula , yace ranki ya daɗe mai gida yace inzo in zauna dake harsai ya dawo kuma duk inda zakije nine zan kaiki ,

     Cike da masifa nace kamar ya ka zauna dani ? Ko ance neman wanda zai tayani zama nakeyi ni bana san kilbibi kawai ka kama gabanka , Ashiru yace babu inda zanje ko a napep zaki fita yace kawai in riƙa bin bayanki shine abinda yace , to me yake nufi da abi bayana , Ashiru yace nima haka yacemin , aiko sai inga wanda ya isa yabi bayana , Ashiru yace mai gida ya isa kuma sai nabi bayanki saidai ki fasa fita amma ina nan daga nan har Allah ya dawo dashi lafiya , 

       Cike da masifa na nuna Ashiru da ɗan yatsa nace kasan sharrina kuwa ? Banza yayi ya ƙyaleni , nace tou bakai ba ko ubangidan naka bai isa ya sakawa rayuwata ido ba dani dakai mu zuba , nayi wanka yanzu zanje daura ka biyoni idan ka isa kuma ta gabanka zanbi in wuce lusari kawai dakai , ina faɗin haka nayi ciki ,

      Murmushi Ashiru yayi tare dabin bayan Sultana da kallo , tunanin Dikko yayi da yace masa , An mata tana wayau sosai kuma haɗarinta yawa gareshi tana anfani da wani abu take sa mutane bacci dashi sai ka kula , mai gida ya akayi ka sani , wurin “yan daban da take amfani dasu domin saida nasa aka tattaromin su akan wani binke daya shafeni ka kula tafiyata ta zama dole saboda Dady yana jirana Yazeed sharrinshi yana da ƙarfi na baka amanar An mata Ashiru idan har wani abu ya faru da ita bazanyi kuka da kowa ba sai kai , Ashiru yace mai gida bana tunanin zata fita ta tsorata dakai , Dikko yace batajin tsoro na irin An mata duka baya mata  amma zata tsorata dani da zaran na aureta dan irin su An mata hukunci ɗaya ne maganin su kuma dashi zan horata kowa zaiyi mamakin natsuwarta dan yadda nasan zan mutu haka nasan sai An mata ta fita ,

Ashiru yace lallai kuwa gata ita daura zata tafi ma , zanga ta gidan ubanda zaki bi ki fita , fitowa yayi daga cikin mota ya fara duba saman katangar gidan da aka zagayeta da wayoyi masu raba mutum gida biyu su tsisstige masa hanji , zagaya gidan ya farayi ko zai samu wani wuri daya buɗa inda zai ba mutum damar fita ,

      Dariya nayi nace ga ɗan boko wanda ya zaga duniya ga jahila wacce ba ilimin boko kuma babu inda taje tana rayuwarta ne a cikin birninsu yau zanga yadda zamuyi wannan wasan dakai malam Ashiru dan wallahi ko min bala’e sai naje daura kuma sai naje na dawo kana nan banza kwance a mota kana baccin asara…………

                Muyi wasan…..

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button