Ni da Dr. Sadeeq

NI DA DR. SADEEQ Book 1, page 17-18

🅿️17&18

“Idan kika gudu kinjawa kanki”koma kin gudun baza’a barki kifitaba”gudunki k’ara laifine”yafad’a fuska ad’aure yana harararta”

murtala yayi k’asa da kansa yana dariya”Aysha kuwa jikinta sai kirma yakeyi”tana ja da baya tana kallonsa”

jira kikeyi na maimaita kizo ne?”nidai wlh kana takura wa rayuwata”yakakeso nayi da raina dan Allah?”tafad’a tana sakin kuka”

Idan kika wuce 5minit baki shigoba office d’in nan ba wlh saikin raina kanki”yana fad’in hakan yaja tsaki ya wuce cikin office nashi.

Kallon murtala tayi tace”.dan Allah kabashi hak’uri karya dakeni”kinga nidai bbu ruwana baki jamun gun both”tunda yace”.kije ,to kije mana”nina san bazai dakeki ba…

Shiru tayi ta rasa mafita”tabbas tana tsoron duka”dabadan hakan ba barata jeba”

Tura k’ofar tayi ta lek’a yana zaune kan kujera yana danna laptop”tsab yaganta, saima yanuna be gantaba”

dan Allah gani nazo karka dakeni wlh nabari”idan zaki shigo ki shigo”idan bazaki shigowa ki koma”

"shigowa tayi ta zauna kan kujera"ke meyasa bakya jin mgn?"idan baki sani surutu ba hankalinki be kwanciya"

Kayi hak’uri dan Allah”nidai yanzun aikin meye zanyi?”

Kije ki kwashe wa’acan books d’in kigoge table d’in da books d’in”

shiru tayi”hakan yasa ya d’ago kansa suka had’a ido”ban hanaki kallona ba?”shiru tayi ta mik’e tsaye ta wuce gun books d’in”tasha alwashin komai zai mata zata dena tankashi”

tanata aikinta bbu me mgn acikin su”har yafara ganin patient”

bayan Aysha tagama ta k’araso kanta ak’asa nesa dashi tace”.na idar bbu wani aikin?”shiru yayi bece komaiba”

Ahaka wata patient tashigo”budurwace taci bleeching”tana sanye da doguwar riga ta atamfa “wacce ta fito mata da suran jiki”gashin gaban kanta awaje”shatin k’irjin ta ana gani”

tana wata yatsina ta shigo ta zauna"kallo d'aya Aysha tamata ta fahimci bbu tarbiyya atare da yarinyar "

meke damunki?”abinda dr sadeeq yafad’a kenan”batare data samu darajar ya kalleta ba”shibema lura da dress d’in jikinta ba”

breath nawane ke ciwo”zaro ido Aysha tayi tana kafesa da ido”had’e rai yayi sosai ya d’ago kansa yamata kallo d’aya tanata wani fari da ido”

you are very stupid !neman lafiya kikazo ko shashanci”get out of my office now! yafad’a atsawace”sosai yarinyar ta tsorata”jikinta na b’ari ta fice”

Aysha kuwa tabbas tagama yarda dr sadeeq mutumin kirkine”ta tabbar idan da wanine bbu ruwansa zaice ta zaro yagani.

kallonsa tayi taga yana k’ok’arin tashi yafita”da sauri tace”.kaji akwai aikin dazanyine?

malama bakisan sunana bane?amma kaima kefa kake kirana dashi”bayan kuma kasan sunana”

Okay ramawa kikayi sbd ga sa’an wasanki ko?”nidai ah ah ba nufina kenan ba”

narasa yazanyi da raina gun nayimaka daidai”bazan iya kallon idonkaba nakira sunanka zahiri kai tsaye”nace yaya sadeeq ka disgani,nace y’allabai” shima bakaso”nace kaji”shima bakaso”yazanyi da raina dan Allah?”tafad’a tana fashewa da kuka…..hakan yyi daidai da shigowar dr habib”

Aysha naganinsa tayi saurin fita dg office d’in”kallon tambaya dr habib yamasa”shikuma yatab’e baki yazauna yafasa fitan”

gsky yakamata kaji tsoron Allah!akanmefa kenan?dr sadeeq yatambaya yana binsa da wani irin kallo”

Akan y’ar mutane mana”idan bakaso tamaka aiki ka sallameta mana”kullum saika sakata kuka fisabilillahi”

To shikenan nadena yaya habib”cewar dr sadeeq yana kallonsa da mamaki”

murmushi dr habib yyi yace”.ah ah inani nazama yayanka”to ai abin naka ne yasaka nace maka yaya”

yarinyar can batada kunya”kuka kuma yanzun nafara sakata miye ruwanka?”sannan indai akantane kazo dan Allah kafita kawai.

hmmm kadai bi Ahankali wlh”amma be kamata kana fad’a da k’ank’anuwar yarinya hakaba”wlh bakaji yadda ake maganar ku a asibitin nan ba”dama dr Amina tazo tana yambayata wacece yarinyar nan??”

kai kuma saika ce mata me?”ina ruwanta da sanin matsayinta?idan batayi sannuba wlh zan koreta dg asibitin nan”tanacin darajar yayanta (abokinsa)”,amma da tuni nayi waje da ita.

Dariya dr habib yyi yace”.yakamata ka sassautawa yarinyar nan kodan darajar tanada sunan amminka”

hmmm!ko yanzunma kuka takeyi wai ita da ke nake kiranta bana fad’in sunanta”

saika sanar mata dalili ko?”wani kallon bakada hankali dr sadeeq yayiwa dr habib”kafin yace”.mlm zan cigaba da diba patient nawa kafita idan wannan shirmen yakawoka”

Dr habib yafita yana masa dariya”shi kuma yaci gaba da duba patient.

Aysha kuwa bata koma zuwa office d’in ba”saida taga yatafi masjeed,sannan ta shiga ta gyara tafito taje gun anty murja”

bayan sun gama sallar azahar suka wuce gida”antyn ita tabiya mata kud’in nafef”sbd akwai nisa dg asibitin zuwa gidansu Aysha.


Kwanci tashi bbu wuya agun Allah”halin dr sadeeq har Aysha ta saba dashi”

danma yanzun bata cika yawan masa musu ko sa’insa dashi”idan kuma yab’ata mata rai”saita fito tayi kukanta ta koma”

dg ina kwana bbu abinda ke had’ata dashi”shikansa yanzun har mamakinta yakeyi”

Duk aikin dazai sakata sbd yak’untata mata tana hak’ura tayi bata masa musu ko gaddama”

yyinda murtala nata cusa kansa agunta sbd ko fira sudingayi”ita kuma tak’i bashi fuska”

Dr abbas kuwa yarasa ta yaya zai fara jan Aysha ajiki”kafin yasami abinda yakeso”duk time d’in da yayi yunk’urin mata mgn” sai yaga da mutane ko kuma tana office d’in dr sadeeq”

Ayau yakama friday kuma ayau za’a basu albashi”kuma Aysha tasanarwa baffa sbd damunta da zancen tabashi kud’i daya keyi.

tun 6 am ta taho k’asa sai 6:47 am ta iso asibitin sbd batada ko bicika”wankan ma da ruwa tayi sbd rashin sabili da bbu agunta.

Dr sadeeq k’arfe 7:am yake isowa asibitin”amma yau har 9: am shiru”gaba d’aya Aysha ak’agare take yazo yabasu kud’in ta tafi dasu kota huta da bala’in baffa idi”karma takoma yace”.taje duk Inda zata samo mishi kud’i taje saita samo”tsab zai iya haka”

Tana wannan tunanin k’amshin turarensa yakaiwa hancinta kuwa”ta kalli gefenta”

dr sadeeq tagani zai shiga office nashi”yaci wankan k’ananun kaya”jeans da farar t shirt”da takalmi sawu ciki”fuskarsa tasha gyara “sajensa yyi lub gwanin kyau”sumarsa kuwa har salk’i takeyi”breaf case nashi ahannunsa da wasu takardu”fuskarsa ad’aure kamar kullum.

Aranta tace”. mutumin nan akwai iya d’aukar wanka”tashi tsaye tayi gudun kartayi laifi agunsa”

Ahankali ta tura k’ofar office d’in”tayi sallama kanta ak’asa gudun karyace ta kallesa”har k’asa ta duk’a nesa dashi tace”.ina kwana?”

lfy ! yafad’a batare daya kalletaba”shiru tayi kanta ak’asa”yatsina fuska yayi yace”.wannan d’ukiyar nasan akan albashin kine”nabawa sister murja tabaki yanzun”

yau zanyi tafiya sainayi 6 weeks ko 4 weeks zandawo”

Allah yatsare “dallah kijira kiji meye zance”batace komaiba sbd tasaba da halin sa”

baby zatazo yanzun kuje da ita gida”kiga gidan saiki dinga zuwa kullum acan” zaki cigaba da aiki da tayata zama kafin nadawo saina sallameki”

Amma idan bana ra’ayi fa?”bana buk’atar kiyi ra’ayi”dolene zakije”

kima godewa Allah dayasaka har kikayi sa’ar zan kaiki cikin family d’ina”

Amma inafa zuwa skul”sister murja tace”bakya zuwa ai”

rashin kud’i ne yahanani zuwa “kuma yanzun nasamu zan dinga zuwa”

narigada nagama mgn”idan nadawo kinje skul d’in ai ba kyauta zaki yi aikin ba….be k’arasa zancensa ba aka turo k’ofar.

Atare suka kalli k’ofar….✍️

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button