BAIWA 4

Kiran da aka masa a waya yasa shi d’agawa ya na d’an matsawa daga wurin ya amsa da “Ina jinka Abdul, ka zo ne ?”
Jim ya yi alamar ya na sauraren me maganar kafin yace “Ok ina zuwa.”
Hanyar fita ya nufa yana fad’awa mai gadi “Bud’e k’ofa akwai wanda zai shigo.”
Bud’e k’ofar mai gadi ya yi ya fita har k’ofar gidan yana dubawa, cikin wata tsadaddiyar mota bak’on ya fito tare da matarshi da ita ma ta gaji da had’uwa, gaisawa sukayi sosai kafin ya musu alama da su wuce gaba, suna shiga shi ma ya bi bayansu da niyyar shigewa muryar Hafsatu ta dakatar da shi daga niyyar shigewar tana fad’in “Ina wuni Abban Saleema.”
Juyowa ya yi yana ganinta ganin dai ya d’an shaidata wasu lokuta Safiya na kai mata d’inki yasa shi d’an sakin fuskarshi ya amsa da “Lafiya lau, ina wuni ?”
“Lafiya lau, ina Saleema ?” Ta fad’a da fara’arta, ba yabo ba fallasa ya amsa da “Ta na ciki.”
Murmushi ta yi tace “Saleema kenan, akwai k’ok’ari wallahi, idan ta yi wani abun ba za ka ce yarinya ce ba, shiyasa ma na ce ta fad’a maka a siya mata telarta, dan hakan zai fi kawo mata sauk’i.”
Da mamaki da kuma rashin fahimtar inda zancenta ya dosa ya gyara tsayuwarsa yace” Tela kuma?”
Ba tare da tunanin komai ba tace” E, idan aka siya mata mai aiki da lantarki ma za ta fi gaskiya.”
Har yanzu dai da mamakin ya sake cewa” Dama ta na koyon d’inki ne?”
D’an shiru ta yi sai kuma tace” E, ta yiwu ka manta dai, ai kusan wata uku kenan da ta fara zuwa, dan ma ba na koya mata wasu abubuwan saboda k’arancin shekarunta.”
Wani kallo ya mata lokacin da idonshi suka fara yin launin ja na b’acin rai dan jin yaudara da ha’intarshi da Saleema da kuma mahaifiyarta sukayi, wato idan ya fahimta duk lokacin da Saleema ta ce mishi za tatafi karatu can ne ta ke zuwa? Jinjina kai kawai ya yi ya shige bayan ya furta “Nagode.”
Ya na shiga inda ya hangi Saleema zaune ita kad’ai ta dasa kanta k’asa ta na zana abu a takarda ya nufa, ya na zuwa kam takardar ya fincika da k’arfi, hakan yasa rabi ta yage ta bi hannunshi rabi kuma a hannun Saleema da ta d’aga kanta tana kallonshi a tsorace. Kallon takardar ya yi ya ga ta zana sanfirin wuya, duk da bai gane komai ba amma ya fahimci dai abunda aka fad’a gaskiya ne dan ga shaida nan.
Tsaye ta mik’e tana zazzare ido ta na kallonshi, tsareta ya yi da ido yace “Me ye wannan?”
Rarraba ido ta fara yi na rashin gaskiya, kafin ta ce wani abu Safiya da ta hangesu ta kuma kula kamar ba lafiya ba ta taho tace “Lafiya Alhaji?”
Rai b’ace ya kalleta yace “Me ye wannan?” Ya nuna mata takardar? Kallon rashin sani da fahimta ta ma takardar sai kuma ta girgiea kai tace “Ban sani ba, me ye wannan d’in?”
Nuna kanshi yayi yace “Ni ma kike tambaya?”
Sai kuma ya jinjina kai ya nunasu da yatsa yace “Ku jira a gama taron nan zan ji daku dukkanku.”
A fusace ya wuce ya barsu inda Safiya ta kalli Saleema tace “…
Alhamdulillah.