Baiwata

BAIWATA 1

A hassale Yusuf yace” Koma dai menene ai gaskiya ta fad’a, saboda hakane fa yasa ko nunaki bana so na yi a matsayin iyalina, ba yanda zanyi ne tunda iyayena ne suka had’ani da ke, amma ‘yata dole na d’orata akan irin tsarina.”

Tsamm! Safeeya tayi tana kallonshi da mamakin kalamanshi, bai tab’ a kwatanta fad’a mata haka ba sai yau, me ya yi zafi daga magana har yake cizgata haka? Hawayen da suka malalo mata ne yasa ta saurin juyawa da sauri ta koma d’akinta, da harara ya bita tare da d’auke kanshi ya mayar kan Saleema wacce ke kuka kamar ranta zai fita, sake gyara zama ya yi alamar dai za sucigaba daga inda suka tsaya.

Bayan sati d’aya

A shirye dukansu suka fito cikin kyakyawar shiga, sai dai duka yaran na Ardayi riga da wndo ne na siket a jikinsu yayin da kawunansu ke bud’e sai dogon gashinsu da aka mishi fasalin kitso mai kyau. Daga cikin mota yake hangen yaran na tunkaroshi, tabbas ya fi son ‘ya’yan Ardayi, sai dai bai san me yasa ya fi son su ba, saboda kyawonsu da farar fatarsu ne? Ko kuma dai saboda ilinmunsu ne? Maida kallonshi yayi kan Saleema dake bayansu cikin shigarta ta doguwar rigar shadda da kyakyawan hijab d’inta, ba za ka kirata bak’a ba saboda tana da d’an haske, sai dai idan ta jera da su Hadeeya bak’a take komawa saboda haskensu, kyawu kuma ba’a magana dan ba wani kyan fuska gareta ba, shi mamaki ma yake wasu lokutan yanda Saleema ta zama jininshi, duba da shi dai yayi tashen kyawu a zamanin k’uruciyarsa, kuma har yanzu da yake da shekara arba’in da yan kai, sannan mahaifiyarta ma kyakyawa ce dan ta wata fuskar ta fi Ardayi kyau, duhu ne kawai gareta na fata wanda kuma yake k’ara fito da kyawunta. Amma Saleema ba kyan fuska ba hasken na fata, wanda daga shi har uwarta da ta yo d’aya daga cikinsu to fa da ita ma kyakyawa ce, ga kuma wani munin na daban wato rashin ilimi.

Drebanshi ne ya bud’e musu inda mahaifin na su ke zaune duk suka shiga, da fara’a ya amsa musu da “Kun gama shiryawa?”

“E Abba.” Suka fad’a kusan a tare, a hankali dreba ya fara jan motar suka fita a harabar gidan, cikin sanyayyar murya Saleema ta kalli mhaifin na ta tace “…

Yan uwa barkanmu da sallah, da fatan Allah ya karb’i inadunmu yasa muna cikin ‘yantattun bayi, Allah ya gafarta mana zunubanmu.

Alhamdulillah.

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button