Uncategorized

TAKUN SAKA 35

 *_Typing????_**_Zafafa biyar na ku

ɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._**_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK????????_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK????????_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

_________________________

*_Chapter Thirty Five_*

……….Yaran A.G sun gama bincike ko ina babu Master da Hibbah a gidan. Sai da ga ƙarshe A.G ya farga da bin jinin da Master ya dinga zubarwa har cikin kitchen. Yay tsam yana auna inda jinin ya tsaya ya kuma zuba da yawa. 

     “John!”.

Ya kira sunan ɗaya da ga cikin yaran nasa cikin da ka tsawa. A guje sukazo. Batare da yayi magana ba ya nuna musu p.o.p yana zaro waya aljihu. Cikin ƙanƙanin lokaci suma suka shige cikin p.o.p ɗin. Koda suka shiga suma ta cikin bututun sukabi suna sanar masa abinda suka fahimta. Sai da suka ɓilla har ta wancan gidan sannan suka sanar masa ta waya.

        Wasu yaran ya bari anan ya fito ta cikin layin, gida uku ne tsakanin gidan da inda su Master suka zauna.

       “Lallai guy ɗin nan ya cika matsiyaci shu’umi. Kaga shege kamar wani kurege ta ko’ina fasa hanyoyi yake.”

      Ɗaya da ga cikin yaran A.G ya faɗa rai a ɓace. Komai A.G bai iya cewa ba. Dan zuciyarsa tabbas tana gab da fashewa a cikin ƙirjinsa. Jin shigowar wasu ɓangarori na jami’an tsaro cikin layin ya sakashi fita. Cikin ƙanƙanin lokaci anguwar ma baki ɗaya ta gama hargitsewa. Bakaji da ganin komai sai jami’an tsaro da ƴan jaridu. Kowa burinsa yaji wani abu da ga bakin su A.G da suka fara zuwa wajen. Sai dai ina komai ya kasa fita da ga bakin A.G. da ga ƙarshe ma zare jikinsa yay ya baro anguwar saboda kiran da Alhajin Mande yay masa akan ya maza yazo inda suke tunda zancen guduwar master harta sake bazuwa cikin ƙanƙanin lokaci.

         Gaba ɗayansu sun hallara ne a gidan hutun Dr Sufi, duk da kuwa kiraye-kirayen wayoyi da suketa samu daban-daban akan neman tabbacin kuɗaɗen da akace Master ya wawasar musu. R.D na zaune yana rusar kuka kamar ƙaramin yaro shi da Alhaji Sallau. A.G na shigowa R.D ya miƙe ya nufesa cikin rawar jiki. 

      “A.G an kamashi?”.

A.G da shima kusan kan nasa so yake ya juye ya girgiza masa kai.

       Kuka R.D ya sake fashewa da shi saboda tsabar tashin hankalin da yake a ciki. “A.G ya nakasta min rayuwa ya yasheni matsiyacin nan. Naira dubu hamsin kawai ya barmin a accaunt tsinannen……”

         “Kowa ma abinda ya bar masa kenan R.D. yanzu ba lokacin zaman kuka bane ko jajantama juna. Lokacine na himmar cimma rayuwarsa dan baiyi nisa ba. A yanzu haka na baro cikin gidan da yake ne saboda kiran da kukaimin. Amma na bar yarana duk da kuwa ya gudu. Yarinyar nan ta wajen Halilu ne ta tona asiri. Amma abinda ya bani mamaki da ga ƙarshe bayan mun tarfasu a cikin gidan duk da abinda tai masa shine ya ringa bata kariya daga harbin dana saka ai musu, sai shi harbin yayta sama shi a dole jarumi”

       “Dan ALLAH da gaske kun harbeshi!!”. Engineer yay maganar tamkar wani zararre. Dan alamu ma sun fara nuna kamar notin kan nasa ya fara kwancewa shima fiye da nasu R.D ɗin”.

      A.G ya kaɗa masa kai cikin tabbatarwa. “Tabbas mun harbesa. Sai dai harbin duk ya samesa inda bazai mutu ba…….”

      Cikin katse A.G Alhajin Mande yace, “Idan matsiyacin yaron nan ya mutu yanzu to ai muma mun mutu A.G. dolene yaƙinmu ya kasance na dawowar dukiyarmu hannunmu harma da wadda muka sakashi ya tara. Kafin mu walakanta rayuwarsa da duk ma wanda ya shafesa. Tunda har ya bama yarinyar kariyar hakan na nufin yana sonta kenan, dan nidai nasan baida imanin da zai kareta batare da soyayya ba…….”

         “So! Kuma? Kai gaskiya bana tunanin haka”.

   Cewar Dr Sufi cikin kokwanto.

           Tsaki Alhaji Sallau yaja da faɗin. “Dr Sufi kana mamakin wacece mace. Duk wani shaiɗanci da kake ganin matsiyacin yaron nan ya iya bazai saka ya kasa shiga kaidin mace ba. Ai ni tun randa akace ya ruguza auren ƴaƴan halilu nakeji a raina akwai wata a ƙasa. Shiyyasa ban zauna ba sai da na gano inda ƴan uwan yarinyar suka koma yanzu haka. Jiya-jiya aka kawomin bayanan dama a meeting na weekend ɗin nan naso kawo zancen dan mu masa tarko da su koda yaso aikata cutarmu, to ashe shaiɗanin ya gama shirya mana tsaf.

      A zabure A.G yace, “Da gaske ka samo inda suke?”.

     “Tabbas kuwa bar kokwanto A.G”.

Alhaji Sallau ya faɗa yana zaro waya a jikinsa.

     Wata shegiyar dariya A.G ya sanya da faɗin, “Tabbas Master kazo hannu dan uban babanka. Dan da yarinyar zamuyi amfani kazo garemu. Yanda take son ahalinta muna damƙesu kaima bazata barka ka shaƙi numfashi lafiya ba”.

     Fahimtar gaskiyar zancen da manufarsa ya sakasu jin wani ɗan karen sanyi na ratsa zukatansu. A take suka gama aminta da zuciyarsu cewar Master yazo hannu ya gama kawai. Dan Alhaji Sallau na gama basu adireshin su Ummi A.G ya kira ya ransa ya basu Umarnin binsu Yaya Umar har wajen ayyukansu a kamo masa. Hakama su Ummi.

(Tabbas Master kayi gaskiya akwai matsala????????????????????????)

__________________________

            Ummi da surukanta gaba ɗaya na a sashenta suna hira kamar yanda suka saba zuwa mata a kowanne safiya su ɗan zauna bayan fitar mazajensu, matar Yaya Umar ta fara ganin abinda ke faruwa awayar hannunta. Cikin waro idanu waje take faɗin, “Tabɗi jan, shahararren ɓarawon nan yau ma ya sake guma uwar satar datafi ta kowanne lokaci a tarihi”.

      Kusan a tare suka haɗa baki wajen tambayar waye?.

     “Master mana. Gashi bbc ma har sun saki”.

     Ta basu amsa kanta tsaye. Gaban Ummi ne ya faɗi dan a saninta dai na yanzu Isma’il shine Master. Kafin ta samu damar cewa wani abu Zahidah tace, “To bara mu kunna television”. Batare da jiran amsaba ta dauka remote ta kunna. Cikin sa’a kuwa ana tsaka da nuna rahoton ne dan kowanne gidan tv da na redio shine latest labarinsu na yanzu-yanzun nan da gaba ɗaya ya hargitsa ƙasar dama duniya. Dan anyi itifaƙin bai taɓa mahaukacin sata makamancin na wannan karon ba ma. Ya yashe asusu goma sha ɗaya a lokaci guda. Asusai kuma masu matuƙar nauyi na kuma manyan mutane da ake matuƙar ganin mutuncinsu cikin dattijan ƙasa. Harda jami’an tsaron da ke farautar rayuwarsa.

       Hankalin Ummi bai gama tashi ba sai da taji sabon rahoton da ɗan jaridar ke faɗa cewar a yanzu haka labari yazo musu wata matashiyar budurwa da Master yay garkuwa da ita  ta samu nasarar tona masa a siri ta hanyar kiran wayar ƴan sanda ta sanar musu a inda ya ɓoyeta. Sun sami labari kuma a majiya mai ƙarfi a yanzu haka ƴan sanda sun zagaye gidan inda suke da tabbacin Master yana ciki shima. 

     Karkarwa jikin Ummi ya farayi, ta ɗauka waya da nufin kiran layin yaya Abubakar taji tabbacin zancen, sai ga ƴan sanda sun faɗo musu su huɗu. A razane duk suka miƙe da ɗaga da yin surrender, dan bindigu duk suka nuna musu. 

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button