BAIWATA 10

*NA*
SAMIRA HAROUNA
SADAUKARWA GA
*AHALINA*
GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.) 🤜🤛
(Burinmu d’aga muryoyinmu sama domin anfanar da al’umma had’e da ciyar da adabin hausa.)
☆ [G. M. N. A] ☆ 📖🖊️
Bismillahir rahamanir rahim
_10_
Girgiza kai tayi cike da takaici ta sake kallonshi tace “Mu’awwaz abunda ka aikata zunubi ne babba, sai dai har yanzu kana da damar tuba a wajen Allah, game da ni kuma kar ka ɗaga hankalinka, ba zan tona abinda Allah ma ya rufe ba, ni ma kuma ina so ya rufa min asiri duniyata da lahirata, na maka alƙawarin babu wanda zai ji wannan maganar, amma fa idan ka yi alƙawarin kai ma na farko kenan kuma na ƙarshe.”
Cike da yaudara yace” Na miki alƙawari Saleema, na farko kenan kuma na ƙarshe, wallahi ba zan sake ba.”
Jinjina kai tayi tace” Shikenan, Allah ya sa.”
Raɓashi tayi ta wuce tana faɗin” Sai da safe.” Da kallo ya bi bayanta yana ɗan taune leɓenshi na ƙasa, abunda zuciyarshi ke raya mishi shine” Lokacin da ka san wata a ranar ka ke ganin wata sabuwar halittar.”
Murmusawa kawai yayi ya sauka daga matakalar ya kama hanyar ɗakinshi da tunanin ba ma zai iya da Saleema ba, ba wai dan ta fi ƙarfinshi ba, sai dan gani yake ko aura masa ita aka yi wannan za ta fi ƙarfin iyawarshi saboda suffarta, amma kuma wani ɓangare na zuciyar nuna masa yake zai iya tunda dai mace ce.
*Washe Gari*
Kamar daga sama ta ji ana sallame salla, a zabure ta tashi zaune ta na rarraba ido, dubanta ta kai ga agogo dan ganin lokaci, sai dai inda agogon take babu haske sosai bare ta fahimci, hannu ta kai ta ɗauki wayar Hameeda ta duba, rufe baki tayi cike da rashin jin daɗi tace “Kenan dai sallah ce aka idar?”
Da sauri ta aje wayar ta sauko a gadon tana daddaɓa Hameeda, a ƙala sai da ta daddaɓata sau biyar kafin ta motsa tana faɗin “Ummm! Wai me ye?”
Da sauri tace “Ki tashi har an gama sallah.”
Ta na gama faɗin haka ta nufi ban ɗaki dan rabon da ta tuna ranar da ta rasa sallah irin haka har ta manta, ma fi yawan lokuta dama Mamanta ke tashinta daga bacci, sauran lokuta kuma ita ke tashi da kanta da taimakon wayar Mamanta, juyowa tayi ta kalli Hameeda da ta sake gyara kwanciyarta tace “Dan Allah ki tashi Hameeda, ki tashe su suma su yi sallah.”
Shigewa ban-ɗakin ta yi ta gabatar da abinda za ta yi ta fito a gaggauce, yanda ta barta haka ta sameta, ganin za ta ɓata lokaci wajen tashinsu ita ta makara su su rasa yasa kawai ta canza kayanta ta kabarta sallarta, duk da farilla ce a kanta yanzu, amma saida ta fara yin raka’atanil fijir saboda ta ji fatawar da aka ce indai ka saba yin raka’a biyu kafin fitowar alfijir, to ba laifi idan wani dalili ya sa sallah ta kubce maka ka yi kafin ka yi ta farilla, har ta idar da sallata su Hadeeya ba su motsa ba, cike da takaici ta miƙe ta koma ban-ɗakin ta ɗauko ƙaramar buta da ruwa a ciki, dan su ne kaɗai za su iya tashinsu, ta na zuwa kam ɗaya bayan ɗaya ta dinga watsa musu suna tashi a zabure kamar waɗanda aka firgita.
Cike da tsiwa da rashin kirki Ummee tace “Malama me ye haka? Wannan wane irin jahilci ne? Ya mutane suna bacci za ki tashesu da ruwa? Ba ki da hankali ne?”
Ɗan cije leɓe Saleema ta yi ta lumshe idonta, hakan ya bata damar haɗe abunda ke ranta kafin ta buɗe ta kalleta tace “Ku yi sallah, lokaci na wucewa.”
Hadeeya ce tace “Saboda hakane ki ka tashemu? Dan baki san darajar ɗan adam ba.”
Da alamu irin na ba ta jin daɗin maganar ranta kuma ya fara ɓacewa ta kawar da kanta kaɗan tace “Da sallah ku ka je kuka gabatar ya fi muku alkairi.”
Juyawa tayi tana cire hijabinta Ummee tace “An ƙi a yi sallar to, dole n…”
Fauuuu! Cikin zafin nama Saleema ta kashe fuskarta da mari, a kiɗime Ummee ta dafe kunci tana kallon Saleema, Hadeeya da Hameeda ma a tsorace da kuma mamaki suke kallon Saleema, yo ko su dake ƙannenta ba ta taɓa marin ɗaya daga cikinsu ba, hasalima ko faɗa irin wannan na yara ba su cika yi ba. Girgiza kai Saleema tayi cikin jin haushi tace “Kin gani, kin hassalani, kina ƴar musulma ne za ki furta wannan kalmar? Kin kuwa san hukuncinki a wannan lokacin?”
Ummee da takaici ya gama kasheta a mugun haukace ta nuna kanta tace “Ni kika mara?”
A tausashe ka rantse ba ita ce ta mareta ba tace “An mareki, ki rama mana.”
A harzuƙe Ummee ta sauko daga kan gadon ta yi hanyar fita tana faɗin “Na zan rama da kaina ba, amma zan kira wanda zai rama min.”
Taɓe baki Saleema tayi da tunanin Allah yasa ma rayuka su ɓace ta samu damar tafiyarta daga wannan gida mai cike da kuraye ta ko ina, wa ya sani ma ko gado sukayi? A nutse ta gyara ɗaurin ɗan-kwalin doguwar rigar da ta saka ta jawo silifas ɗinta ta saka, ta kala hanya za ta fita ta juyo ta kalli su Hadeeya da har yanzu ke kallon kamar ba sa hayyacinsu tace “Sallar fa?”
Da sauri Hameeda ta sauko daga gadon ta nufi ban-ɗakin da alamar ta tsorata, Hadeeya kula saida ta murguɗa baki kafin ta sauko ta nufi ban-ɗakin ta tsaya tana jiran fitowar Hameeda. Murmushi tayi da ke nuna “Ku shiga hankalinku tun wuri.”
Za ta fita a ɗakin amarya ta banko kai cike da masifa hannunta riƙe da hannun Ummee, a bayanta kuma Alhaji Auwal ne da Hajia babba a gefenshi.
Kallon kallo suka dinga yi kafin amarya ta nuna Saleema tace “Ke! A kan wane dalili ki ka marar min ƴa?”
Saleema dake mamakin ganin yanayinsu dukansu, kayan da ke jikinsu bai nuna alamar su kansu sun yi sallah ba, dama-dama ma Hajia babba da alamar ruwa a jikinta, wataƙila alwala ta yi dan ko hular kanta bata ɗora dai-dai ba, cike da kunya ta kalli amaryar a ladabce tace “Aunty, sallah na tashesu su yi ba su tashi ba, shi ne ita ta ke faɗin wai an ƙi a yi sallar, shiyasa na mareta.”
Da ɗumbin mamaki amarya tace “Shiyasa kika mareta? Ke baki san fuska daraja ne da ita ba? Kawai sai ki mareta dan ta ce an ƙi.”
Da mamaki Saleema ta kalleta tace “Fuskar ce ke da daraja? Wa ya faɗa?”
Cike da sababi amarya tace “Ai ko a wa’azi ana faɗa cewa babu kyau dukan mace a fuska saboda tana da daraja.”
Wani ɗan murmushi Saleema tayi cike da raha tace “To aunty ai wanda ya ba fuskar daraja shi ne kuma ya ce shi kaɗai yake so a turmusa fuskar nan ƙasa dominshi, kenan ya dace ta ce ba za ta yi ba?”
A hassale amarya ta sake nunota da yatsa tace “Ke Saleema! Tunda kika zo gidan nan dama na fahimci wani tsageran iskanci kike ji, to ni bana son irin haka, ki tsaya a matsayinki kawai, amma ya za ki zo gidan uban yarinya kuma ki mareta, ina aka taɓa haka?”
Gyara tsayuwa Alhaji Auwal yayi wanda da farko jikinshi ne yayi sanyi, duba da an mari ƴarsa akan ba ta yi sallah ba, to ya kenan shi idan ta ji bai tashi ba sai kukan Ummee ne ya tasheshi shi da uwar Ummeen? Cikin nutsuwa ya kalli Ummee yace” Ke je kiyi sallah.”
Sai kuma ya kalli Saleema yace” Shikenan ya wuce, kowa ta je ta yi sallah.”
Cike da damuwa Saleema tace” Ni na yi sallah Abba, amma dai ka faɗa musu su dinga tsayar da sallah a kan lokacinta, kamar Ummee da su Hadeeya idan aka umarcesu suyi sallah su ka ƙi kuma ba tare da wani uziri ba, sannan sun yarda babu abun bauta da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad Manzon Allah ne, aka tabbatar sun yarda da duka shika-shikan musulunci, to fa wasu suna ganin kashesu za’ayi ta hanyar cire musu kai, wasu kuma suna ganin a’a za’a jinkirta musu ne su yi sallar sannan ya kashesu…”