NOVELSUncategorized

RAINA KAMA (BOOK 2) 22&23

~book 2~????????22
…………….Cikin kuka Munubiya tace, “y’ar uwata ki taho gida please”.
        Munaya dake saurarenta ta share nata hawayen itama, “insha ALLAH zan taho, ki kwantar da hankalinki, daga yau zuwa gobe ko yaushe zaki iya ganina sweetheart”.

    Daga haka munaya ta mik’ama Galadima wayar tana cigaba da share hawaye.
    Hankalinsa atashe yace, “miyasa zakimata alk’awarin zuwa? bayan kinsan ga halin da kike a ciki”.
         “kayi hak’uri yalla6ai, gara ka barni Na tafi shine mafi a’ala, tun farko y’ar uwata bata 6oyeminba ta sanarmin naje gida Na haihu, idanma baka kainiba to wahala kawai zanta sha anan d’in tunda hakan take buk’ata”.
     Galadima jiyay tamkar ya make Munaya, ya haukace mata da masifa kaikace zai cinyeta d’anya, “wannan ai canfin banzane da wofi, ALLAH shine kawai maiyi ai bawani alk’awarinku ba, shin Ku bazaku tausayama kanku baneba? yaufa kwannanki biyu kina wahalarnan, wane irin taurinkai ne wannan…….?”.
     Dakatar dashi Momma tayi ta hanyar d’aga masa hannu, ta dafa k’afad’ar munaya dake kuka tana fad’in “y’ata dama kinmata alk’awarin zakije Nigeria ki haihu ne?”.
            “Momma ba alk’awari namataba, amma kusan 2months kenan tacemin gida zanzo Na haihu ko? nikuma bance mata komaiba”.
      Murmushi Momma tayi, ta kalli Galadima dake tsaye yanata kumbura dan haushi. “Muh’d anemi ticket d’in Nigeria yanzunnan”.
      Da sauri yace “Momma amma……”
     Hannu ta d’aga masa alamar bata buk’atar jin komai. ya had’iye wani k’ullutu daya tsaya masa a mak’oshi, shifa ba tafiyar tata bace matsalarsa, shima akwai tashi manufar da dalili, amma bashida ikon yin jayayya da Momma, waya ya zaro a aljihu. Ya lalubo wata number yay kira, ficewa yay daga d’akin.
     Momma tacigaba da lallashin Munaya daketa hawaye, ga zufa Na cigaba da jik’eta dukda AC dake aiki a d’akin.
          Kusan mintuna talatin Galadima yashigo shida doctor, dannan aka shirya Munaya, nurses biyu suka kaita mota.
     Wannan karon harda Momma rakkiya Airport, tanata jerama Munaya addu’oi har suka isa.
      Haka sukai wannan tafiya babu shiri, Galadima kayan tun safenema a jikinsa bai ko koma gida ya canjaba, hakama aunty Mimi.
      A jirgi yana rungume da ita tanata murk’ususu idan abin ya motsa, wai danma waje Na musamman aka basu dankarta takura. idan nak’udar ta lafa sai barci mai dad’i ya kwasheta, da abin yamotsa kuma tata kuka kenan tana k’ank’amesa, dukta jimasa ciwo da farce, shikam tausayinta dukya cika zuciyarsa.
           Yaa marwan ma cikin haushi yakira  inna ya gaya mata abinda Munubiya tayi, inna taita fad’a tamkar zata ari baki, itada ta haifi su munaya ita tasan halin kowa acikinsu, tabbas a fili Munaya tafi Munubiya fad’a, amma a bad’ini Munubiya tanada ak’idar tsiya da tsatstsauran ra’ayi, lokuta da dama idan takafe akan Abu bata tankwaruwa, kuma dolene Munaya ta amince ayi kokuwa tasha wahala, dan idan Munubiya ta murd’e abin bazai ta6a ya yuwuba saidai idan Ubangiji ya juna mata ikonsa, to amma bata ta6a zaton shirmen nasu zai iya ta6a har lafiyarsu irin hakaba.
                 Dole inna tashirya zuwa asibitin da kanta, taita zubama Munubiya dake fama da kanta fad’a, su mama Rabi’a da Maman Fauziyya sunata bata hak’uri, tunda dai anrigada an aikata, saidai kuma a kiyaye nagaba.
      
            Su Munaya sun iso Nigeria lokacin tsakkiyar ranane anan, dan irin 1pm d’innan ne, dayake yakira su sarkin mota ya sanar dasu time d’in dazasu iya isowa, tun wajen 11am ma suna airport d’in.. 
       Tunda Galadima yafara sakkowa daga matakalar jirgin rungume da Munaya akan idonsune, hakanne yasaka sarkin mota matso da motar bisa alfarmar ma’aikatan wajen, suna gama sakkowa k’afarta ta rik’e, dole ya d’auketa daga ita har nauyin cikin ya k’arasa da ita motar, mutane duk tausayinta yakamasu.
     Tunfa a mota labari yafara canjawa, dan Munaya tafita hayyacinta sosai, Galadima sai tsawa yakema sarkin mota, ALLAH daine kawai ya kaisu asibitin lafiya, aiko suna shiga dogarai suka shiga da gudu cikin asibitin kiran doctors.
      Tunima Galadima ya kuma sunkutarta yayi ciki, a hanya yagamu da nurses da gadon d’aukar marasa lafiya, bai d’orataba, yawucesu abinsa, doctor Farida ta nuna masa d’akin da aka canjama Munubiya.
     Gadon da aka tanada dan Munaya ya d’orata, Munubiya tashiga mik’o mata hannu tana kuka, itama a wahalce tamik’a mata nata, dan gadon kusa da kusa aka sakasu….
      A tare suka dinga Neman yafiyar junansu suna kuka, sai tausayinsu ya kamasu Galadima.
        Da k’yar doctor Farida tasamu Galadima ya fita suyi aikinsu, dama haka tasha dagama da Yaa marwan shima, saida ma Abbansu yamasa magana, Dan shima yana asibitin.
        Munubiya da Munaya Haka suke rik’e hannun juna kowa nashan azabar nak’uda, (wannan k’auna dabance gaskiya, nak’uda ba abun wasaba amma suna son jin junansu a kusa, wato koma mutuwace tazo musu a tare?????).
        Haihuwar Munubiya ce tafara gadan-gadan, Dan haka Munaya ta k’ank’ame hannun y’ar uwarta tana kuka da kiran sunanta a galabaice, itama sai labarin yafara canjawa, Nurse da doctor Farida and doctor Zainab dake Kansu duk suka maida hankali ga Munubiya, cikin rahamar ubangiji saiga jinjiri yayi sallama duniya da kuka. tamkar jira itama Munaya ta kar6a, a time d’in Munubiya tayi shid’ewar wucin gadi, amma hannunta na cikin na Munaya datake shan azaba itama. Ba’a d’auki tsawon lokaciba itama tata mace tafito, saikuma sabuwar nak’uda ta tashi a tare suduka, yanzu Munubiya mace Munaya kuma namiji, na Munaya na fad’owa wani yakuma biyo baya????.
    Turk’ashi, ALLAH sarkin rahama da tausayi, maiyin yanda yaso kuma ga Wanda yaso, Munubiya ALLAH yabata k’autar tagwaye mace da namiji, yayinda Munaya keda uku, maza biyu mace d’aya.
      Su doctor Farida duk sun kacame da murna da k’ok’arin gyara yaran, kaikace su akama haihuwar.
        Dandanan aka shiga goge yara da zaitun, amma cikin hattarar kar a had’esu agaza ganewa.. 
         Su Munaya ma dai kulawa ta musamman aka basu, amma Munubiya ta suma, kuma bata farfad’oba, hakanne ya tada hankalin su doctor Farida suka rufu akanta suna bata dukkan wani taimako, sama-sama Munaya ma kejin ‘Yar uwarta tashid’a, hakanne yasata kuma k’ank’ame hannunta hawaye na zurara mata, itama bawani k’arfine da itaba, Dan ko idanu dak’yar take iya d’agawa, dishi-dishima take ganin komai.
       Lamarin yana san zama babba, Dan saida wani babban doctor ya shigo dole, ganin shigi da ficinsu doctor Farida yayi yawa yafara ankarar dasu Galadima.
     Nanfa suka fara turkesu da tambayar ko lafiya?, sukuma suna basu amsa da babu komai, kowa dai bai yardaba, dukda suna jiyo kukan jariran.
      An d’auki wasu adadin mintuna kafin numfashin Munubiya ya dawo, ajiyar zuciyar da Munaya tasaki duk saida yasaka su doctor Farida kallon ta da tausayi, dukda tana cikin wani hali itama, amma hankalinta nakan ‘Yar uwarta.
     Sun kimtsasu tsaf, daganan aka musu allurar barci dansu sami Hutu, yara dai kam Alhmdllh, duk da sun lura d’aya daga cikin na Munaya bai cika kuzariba, kamar sauran mace da namijin sun fishi lafiya, amma basuda tabbas tunda basu bincikaba. Nurse d’aya tafito ta kar6i kayan haihuwar takoma, duk an saka musu, dukda basu zama iri d’aya ba tunda sunzo babu tabbacin miza’a haifa, musamman ma su Galadima, gara su Yaa Marwan sunsan ita Munubiya dama biyune.
           Tunda su doctor Farida suka fito Galadima dake ta kaikawo shida Yaa marwan da Muftahu suka maido hankalinsu Kansu, Galadima bai iya matsawa ba, saisu aunty mimine suka k’arasa ga su doctor Faridan.
       Kowa yana k’ok’arin tambayar abinda ke faruwa.
     Doctor Farida tayi murmushi, tace, “to ai bakine bazai iya fad’a ba ma, inaga kawai angunan k’arnin su shiga daga ciki, idan sun fito kwaji komai”.
       Yaa marwan da Galadima suka kalli juna, kowa yana fargabar abinda zai tarar d’in.
    Aunty Mimi ce takama hannayensu tana fad’in “kuje mana, mi kuke tsorone wai?”.
      Kowa tamkar an doke masa gwiwa haka suka nufi d’akin, Yaa marwan ne gaba Galadima a baya..  Duk sukayi sororo a k’ofar d’akin suna bin gadajen matan nasu da jariran kusa dasu da kallo.
     Badan kowa yasan kayan jikin matarsa ba dabasu iya banbancewa ba (kunsanfa mu 9ja ‘yan gargajiyane????, kod’an canja kayannan na asibiti bamayi????).
       Galadima da Yaa marwan suka kuma kallon juna, kowa ya kasa cewa uffan, doctor Farida dake bayansu tamkar ta kwashe da dariya, tadai daure ta danne.
      Ra6asu tayi ta shigo ciki sosai, ta tsaya tsakkiyar gadajen tana kallon hannun Munaya da Munubiya dake had’e da juna har yanzu, sunyi-sunyi su saki amma sunk’i, sai suka saka musu lokar asibiti a tsakkiyar aka d’ira hannayen Dan kar suyi sanyi.. Juyowa tayi ta kallesu da murmushi a fuskarta, tace, “wannan itace Munubiya ga babies d’inta nan 2 mace da namiji, wannan kuma Munaya ga nata 3 maza biyu mace d’aya. Ina muku fatan alkairi gaba d’aya, ALLAH ya rayasu akan sunna”. tana gama fad’a ta juya ta fita tabarsu.
      Binta sukayi da kallo harta fice, sannan suka maido ga iyalan nasu, saikuma kowa ya k’arasa da hanzari ga matarsa.
        Yaa marwan yasaki murmushi yana d’aukar macen, sanan ya d’auki namijin shima, dukya rungume.
       Galadima kam durk’usawa yay gaban gadon yasa gwiywoyinsa a k’asa ko k’yank’yami bayayi, dukda angyara wajen tsaf tamkarma ba’a haihunba.
    Hannunsa d’aya ya d’ora agoshin Munaya da duk yaga ta masifar rame masa yau, d’ayan kuma yafara tsafa kumatun yaran d’ai-d’ai, hawaye masu d’umi Wanda shikad’ai yasan ma’anarsu suka fara sauka a kumatunsa. Cikin lumshe ido ya matsa ya sumbaci goshin Munaya da hancinta, sannan ya dawo kan babies nashi yana sumbatarsu.
    Yaa marwan ma yanacan ya duk’ufa kan matarsa yana mata kalamai masu dad’i acikin kunne k’asa-k’asa, kai kace idonta biyu tana jinsane????.
        
    Galadima ya share hawayen fuskarsa, cikin murmushi yace, *“UBANGIJINA ka gamamin komai, yau nine da k’yautar abin cikin kwan d’ai-d’ai har 3 a lokaci d’aya, badan k’arfina kabaniba, bakuma Dan nafi sauran bayinka ka baniba, suma y’ay’a jarabawace ga iyaye, ya Mahaliccinmu kabamu ikon bama yarannan tarbiyar da zasu zama cikin alfaharin MANZON ka da addininmu mu da mahaifansu mata, ka rayasu bisa turbar addinin islama, ALLAH yasa suzama masu tausayi da jink’ai gana k’asa dasu damu kanmu, su zama masu girmamawa da mutunta na sama dasu a duk inda suka shiga, ya RABBI ka rinjayar da zukatansu ga bautarka domin rabauta a duniya da lahira, ka nisantar da zukatansu da gangangar jikinsu ga sa6onka komin k’ank’antarsa dagasu har ‘yan uwansu gasunan guda biyu da k’annensu masu zuwa da dukkan y’ay’an Al’ummar musulmi. I love you so more and more my Darling children’s, ina muku barka da isowa duniya gidan gwagwarmaya, ALLAH yabaku damar cinye jarabawar da ubangiji ya k’addaro a cikin tsawon rayuwar da zakuyi a dunia kafin Ku koma garesa”.*
      Yaa marwan ya amsa da amin shima fuskarsa d’auke da murmushi.
    Tashi Galadima yayi yaje gareshi suka rungume juna.
      Galadima yace, “d’an uwana ina tayaka murna”. Yaa marwan ma yace, “ranka ya dad’e nima ina tayaka murna”.
    Sakin juna sukayi suna dariya, saikuma suka kuma cafke hannun juna cikin musabaha da nuna tsantsar farincikin dake baibaye da zukatansu a yau d’innan.
       Aunty Mimi kasa hak’uri tayi ta danno kai d’akin babu ko sallama.
     To shigowarta cefa ta fallasa komai, kowa yasan d’unbin alkairin daya sauka a wannan families guda uku a yau. Dan danan labari yafara karad’e asibiti da gidajen su Galadima Dana su Munaya.
     Masarautar gagara badau, masarautar su papi, su Momma duk labari ya Isar musu harda hotunan babies gaba d’aya, kafin kacemi labari yafara zagaye social media, *FANS NA RAINA KAMA FA* babu ala, dama duk sungama shirinsu, (danma ansamu sa6ani masu tafiya india????, Wanda basu kai ga tafiya ba ALLAH ya taimakesu saiku tattala kud’in jiyginku babu ruwana????????????????).
      Bakin Galadima da Yaa marwan da dukkan ahalin wad’annan dangi kam yakasa rufuwa, hardamu ma masoyansu.
    Yauma dai su doctor Farida da jama’ar asibiti sunsha k’yaututtuka, Dan Muftahu ya baza abin mamaki, ( lokacin da su sarkin mota zasu fitone yagansu kamar a rikice, shikuma zai fita daga masarautar shine ya tambayesu, sarkin mota ya fad’a masa, bai bisuba saiya wuce asibiti, shine yasaka aka canjama Munubiya d’aki, aka tanadi gadon Munaya kuma). dukda Galadima yayi mamakin ganinsa hakan bai sakashi tambayarsa ba ko katse masa hanzari, ko’a fuskama bai nuna mamakiba.
***************
          Mama Fulani Na kishin gid’e bisa kilisarta kuyanginta Na bautar da suka saba, Wambai na  gefenta yana nuna mata pictures na gidaje dayake son za6ar d’aya daza’a gina masa shima acikin masarautar, don mama Fulani tamatsa suyi aure, shi matawalle yamace bazai zauna da matarsa a k’asarba. Amma mama Fulani tace dolene saiya zauna.
     Wata baiwace ta shigo jikinta sai 6ari yake, ta zube a gabansu tana huttai, Wambai ya daka mata tsawa.
    Firgita tay tayi baya zata fad’i, Mama Fulani ta d’aga masa hannu alamun ya barta.
     “haba Granny kina ganinfa yanda ta shigoma mutane a haukace, saikace wasu sa’ointane a wajen?”.
       Uffan mama Fulani batace masaba, sai wani k’asaitaccen murmushi datayi tana kallon amintacciyar baiwarta, alamu tamata da ido na ta tambayi mi dattijuwar tazo dashi?.domin itace dama mai kawo ma mama Fulani duk wata gulma takowane 6angare a masarautar, Dan ita babu sashen dabata da ‘yan lek’en asiri, kuma wannan dattijuwar baiwa itace shugabarsu, komai suka tattaro ita zasu fad’awa ita kuma takawo ga mama Fulani.
      “mike faruwa tulluwa?”. Amintacciyar baiwar mama Fulani ta fad’a tana kallon dattijuwa tulluwa dahar yanzu jikinta baibar 6ariba.
     “Ranki ya dad’e ki gafarceni da abinda nazo fad’a, banida za6in daya wuce hakan, domin da kiji a bakin wasu gara kifara ji abakina danki tabbatar nasan aikina”.
     Mama Fulani ta hura hanci, yayinda izzarta ta k’aru, sosai ta tashi zaune idonta akan tulluwa.
         Batareda tace uffanba tulluwa tacigaba da magana, Dan tasan ma’anar kallon ta cigaba da magana kenan.
     “ranki ya dad’e yanzunnan labarin haihuwar matar Galadima ta iso wannan masarauta, ba haihuwar baceba abin girgiza abinda ta haifanne, idan kinbani izini sai na fad’a uwar gijiyata”.
       Wani kakkauran yayu mama Fulani ta had’iye, Wambai daya cika yay fam da haushin wannan shegiyar baiwar ya Dalla mata harara, “dalla malama kifad’a kinwani zauna cancana magana kamar wata zuma”.
       “ALLAH ya huci zuciyarka ranka ya dad’e, maganarce tanada nauyi. dama labari ya iso ta haifi yara uku ne maza biyu mace d’aya….”
      Wambai yay masifar razana harda mik’ewa, mama Fulani kam ko motsi batayiba, sai wani k’ayataccen murmushi na k’asaitattun mata masu izza da mulki tayi, ta d’ago ido ta kalli Wambai cikin harara tace “kai kuma miye na mik’ewar?”.
        Tunawa yay akwai kuyangi saiya saki murmushi basarwa, yace “mamaki mana Granny, ‘ya’ya uku fa a 1 time, dolene na taya d’an uwana murna ai”. bai jira cewarta ba yafice da hanzari.
     Lumshe idanu mama Fulani tayi bayan Wambai ya 6acema ganinta, ta kalli amintacciyar baiwarta fuska d’auke da murmushi nan tace araba k’yaututtuka, takuma sallami kowa.
           
     K’yaututtukan da mama Fulani tasaka a rabama bayin gidan yasaka zancen haihuwar munaya yakuma karad’e lungu da sak’o na masarautar, masu murna nayi masu kuka nayi, dan kowa dai yasan magadan masarautar gagara badau sun iso, tunda kowa yasan Galadima ne magaji mai jiran gado, _(karku manta haryanzu sarkin yanzu sarautarsa ta ruk’on kwaryace, Dan mahaifin Galadima tsohon Sarki bawai mutuwa yayiba, sannan ba murabus yayi da kansa yace yabarma Sarki na yanzu sarautarba, so sarautar ruk’on k’warya yakeyi, kuma ko a yanzu tsohon Sarki yasamu lafiya dolene ya sauka yabashi kujerarsa, mai guri yazo kenan, mai tabarma dolensa ya nad’e????????)_.
**************
    A 6angaren gidansu Munaya ma bata canja zaniba, Dan hassada k’ararace tafito a fuskokinsu da matuk’ar razanuwa, kenan arana d’aya Innarsu munaya ta wayi gari da jikoki 5 kenan? miyasa a komai sai Ai’sha ta fisu ne? bayan kuma sun fita gata sun fita dukiya, sukeda dangi da tarin ‘ya’ya a gari, suke da ilimin zamani, k’asarsu ce ba karoro sukazoba?.
       Innaro kam dai tadage sai zuba gud’a take da taka rawa, gud’artace ma ta ankarar da jama’ar anguwar mi ake ciki, dandanan aka cika mata gida ana tayata murna.
    Babu kunya tasaka Shu’aibu ya kaita asibitin, bayan kwanakin munubiya biyu akan gwiwa kuma tasani amma bata ta6a nuna sha’awar zuwa dubata asibitin ba ma.????
***************
       Tunda kuyanginta suka fice tamik’e zaram itama, safa da marwa tafarayi na tsantsar tashin hankali a makeken falonta daya gama jin kayan alatu tamkar bana tsohuwa ba, zufa dukta jik’eta sharkaf, sai kuma maimaita fad’in “y’a’ya uku? Y’ay’a uku fa? wannan ‘yar yarinyar ta haifa y’ay’a uku?, kai banma yardaba gaskiya, kodai k’aryane basuji d’ai-daibane?. jikinta na rawa ta jawo wayarta tayi Kiran Momma.
         Momma dake cikin tsantsar farinciki saboda isowar labarin haihuwar jikokinta sabbi fil a Leda har uku, ta d’aga kiran mama Fulani.
     A mutunce ta gaisheta kamar yanda ta saba koyaushe.
     Mama Fulani bata amsaba, sai tambaya data jehoma Momma, “Zeenah ashe matar d’anki ta haihu? Amma aka kasa sanarmin sai dai naji a jita-jita?”.
      Murmushi momma tayi, tace, “ranki ya dad’e a gafarceni, amma Nima yanzunnanma nakeji, dan suna isowa Nigeria tafara nak’uda tun a mota”.
     Cikeda mamaki mama Fulani tace, “yo a ina ta haihun?”.
      “anan Nigeria ne ai mama”.
        “Ai nazata anan India ne shiyyasa na kira, to ALLAH ya raya, bara nasa a bincikan asibitin”. bata jira cewar Momma ba ta yanke wayar, murmushi kawai Momma tayi tana girgiza kai, ta k’agara Abie ya tashi a barci ta guntsa masa wannan daddad’an labari.
        Saman kujera mama Fulani ta jefa wayarta tana cije la66anta da sakin wata k’aramar k’ara hawaye na zubo mata, ita kuma tata ta k’are, Matawalle ya dace da haihuwar wad’annan ‘ya’yan ba Galadima ba, dolene tanemo mafita da gaggawa kafin lokaci ya k’ure mata.
????????????
★★★★★★★★★★
      Kiran Momma daya shigo a wayar Muftahu ya saka shi mik’ama Galadima, dama shiya kirata ya Sanar mata haihuwar, ganin haka ta kirashi danya had’ata da Galadima, tunda taga suna tare.
      Hakkanne yasaka Galadima fitowa harabar asibitin yana amsa mata, cikeda tsantsar farin ciki suka shiga taya juna murna, ya tambayi ina Abie, ta Sanar masa yana barcine.
       Momma tace, “an sallamekune?”.
     “a’a Momma, har yanzu suduka barcima suke, gashi magriba ma ta gabato anan, banama zaton sallamarnan yau, maybe sai zuwa safiya”.
      Ajiyar zuciya momma ta sauke, tace, “to Muh’d yau fa barci bai gankaba, dolene idonka yazama abud’e tundaga kan doctors, Nurse’s, da makusantanka, hankalin duk wani idon mak’iyinka yanzu akan wad’annan bayin ALLAH guda uku yake,  sunsan shine kawai tarko mafi tsauri dazasu maka a yanzu, su zaituna suna hanya itada kuyangi 5 amintatu da zasu zauna daku, itama Zaitun (mom) bazata komaba sai anyi suna, anayin suna kuma Munaya zata koma gidansu tayi wanka irin na al’ada da kowa ya Sani, tunda kasan dokar masarautar taku kenan. Wannan kawai shine mafita”.
     Ajiyar zuciya Galadima ya sauke, muryarsa cike da damuwa yace, “insha ALLAH Momma duk za’ayi hakan, amma zama gidan nasu bak’ya ganinsa kamar had’ari? tunda za’a iya tsutar dasu a can, dan babu wani tsaro”.
     Murmushi Momma tayi har Galadima najin sautinsa, tace, “nasan abinda nakeyi ai Muh’d, bazance aturasu canba nasan zasu cutu, kaidai kawai kayi hakan, sauran bayani saika dawo zakaji komai, su zaitun nasan suna gab da isowa insha ALLAH. Papi ma yace yakira wayarka bata shigoba daga kai har Haneefa”.
      “tab, yoni Momma ai banmazo da waya ko d’aya ba wlhy, duk nan na mantasu a mota, kima saka khumar ya kawo miki, saidai zuwa Safiya nasamu k’arama na r’ik’e”.
        “to shikenan, dama haka nafad’a masa nima maybe kabar wayoyin anan,  idan ta farka dai a kirani naji muryar d’iyata nima, konaji sanyi”.
    Murmushi Galadima yayi yace “insha ALLAH Momma”.
     Koda wayar ta yanke saiyayta juya maganganun momma a ransa yana musu fashin bak’i d’ai-d’ai. Haka ya koma zuwa cikin asibitin, dan anfara addabarsa da kallo, shi saiya rasama mi suke kallon? Shidai bayasha banban da sauran halitta bane, bakuma za’a kallesa ace ba bak’in fata bane, bakuma wasu kayan ado na musamman ya sakaba, hasalima k’yank’yamin kayan jikinsa yakeyi, dan sun kwana suna Neman yini a jikinsa, (tunda ba time d’inmu d’aya da India ba) yaja guntun tsaki yana k’arasawa ciki ya mik’ama Muftahu wayarsa.
       
   ***********
 Sai bayan isha’i su mom suka iso, dan basu sami jirgi da wuri ba, a lokacin jama’ar gidansu Munaya suna asibitin, masu kukan zuci nayi masu murna da gaskiya nayi, hakama a wasu daga masarauta suna nan, wasu lek’en asiri kawai aka turosu, wasu ko na taya farincikine da tabbatarwa.
        Yau dai yan gidansu Munaya suna kallon abin mamaki, da gaske dai inna Ai’sha tamusu fintinkau irinna jirgi, saidai hange daga nesa da harara cikin duhu.
     Mom bakinta yak’i rufuwa, harda rungume Galadima, Nuren kuwa hardasu taka rawa????, Muftahu na masa lik’i.
     Mutane abin ya birgesu, Galadima yay murmushi yana d’an dukan kafad’ar Nuren da Muftahu kawai.
      Su Munubiya basu farkaba har sannan, doctors sunce babu wata Matsala, a barsu su huta sosai yanda zasu tashi da kwarinsu zuwa Safiya.
       Dole dai Galadima yasa aka zuba police a asibitinan ranar, sauran kuma anbarma UBANGINJIN TALIKAI dake kallon motsin kowa.
       Masu tafiya duk suka tafi, aka bar masu kwana kawai.
    Galadima da ya dage anan zai kwana shima, da k’yar dai mom ta lalla6ashi ya tafi gida kodan yasamu yad’an huta, kallo d’aya zaka masa ka gane a matuk’ar gajiye yake, jijiyoyin Kansa sunyi rad’a-rad’a, ga yunwa waddama ya manta da ita da alama.
      Wannan dare dai ya kwana rayashi da bautar ALLAH ne da godiya mai yawan gaske.
    Innarsu Munaya ma dai kuka sosai tasha na dad’i, itama haka ta raya wannan dare, hakama Abba, shima yamik’a godiyarsa ga ALLAH dan lokacin dayake buri da tanadi ya cika, koba komai zai sauke nauyin dake rataye a wuyansa insha ALLAH.
      Washe gari……………????????
*_media ko bala’i, kayi turanci a novel ace ka cika iyayi da son asan ka iya turanci????????, muda muke koyo muyi ace bamusan abinda mukeba????????, kai jama’a babu mai iyama ‘yan social media sai ALLAH, ko uwarka ka yanka kagasa tasha mai kwallan tana d’iga, da wani yagama ci zaice bataji gishiri ba????, ALLAH ya shiryar damu muda bakunanmu dai.????????._*
_Ayshan sadiq sak’onki ya iso gareni, nakuma gode kwarai da gaske, saidai ina mai baki hak’uri da sauran fans d’ina, a gaskiya weekend d’inan ina muhimman abubuwane a cikinsa, bazan iya alk’awarin typing ba, sannan ni kaina idanuna ????????da Brain ???? d’ina suna buk’atar hutu, inada aure, akwai wasu hak’k’oki a kaina bana typing kawai ba, kunga yadace suma na basu lokacina, dan Ku gamsu nake zaman yin typing mai tsawo, insha ALLAH idan mukai hak’uri kamar yaune raina kama zaizo k’arshe abarma yayinsa Ku manta dashi saikuma wasu dazasu 6ullo daga sauran writers namu, dan haka muringa hak’uri da abinda ALLAH ya k’addara namu a lokacin da ya tsara, kar muyi gaggawa domin aikin shaid’ance, nima Ku duba nawa buk’atun amatsayina na mutum kuma mace mai rataye da igiyar auren. Ina godiya kwarai da gaske da k’aunar da kuke nunama wannan buk, bammasan yanda zan nuna muku farincikina ba kusan inajin dad’in Comments naku nima, amma ina sonku irin sosai d’inan a raina, kumuje zuwa guys, duk Nisan jifa k’asa zai fad’o????????_
  I love you mazga-mazga all.????????????????????????????????????.
Ayshan sadiq, ina miki fatan alkairi a duk Inda kike????????????????????????.
*_ALLAH ka gafarma iyayenmu_*????????????
[7/9, 11:05 AM] y’ar K’asa: *_typing????_*
 ???? *_HASKE WRITERS ASSO….._*
           *_RAINA KAMA…..!!_*
                  _(Kaga gayya)_
              *_Bilyn Abdull ce????????_*
   ~Book 2~ ????????23
……………Koda Muftahu ya sauke Galadima saiya sake shiri Yakoma asibitin, tunda ya shigo idon Nuren a kansa, sai mamaki ya kamasa, shin miya maido Muftahu asibitin? bayan kuma tare suka tafi da Galadima.
        Bai masa maganaba dan karma yasan ya gansa, saiya saka ido a dukkan wani motsin Muftahu d’in, shidai Muftahu baisan yanayiba, dan baima je d’akinda su Munaya sukeba, sai zagaye-zagaye dayaketa famanyi har ALLAH ya wayi gari lafiya.
         Wannan lamarifa ya zaune a zuciyar Nuren yanata kaikawo, anya kuwa ba suna zargine akan abinda ba haka yakeba?, dukda jami’an tsaro dake wajen Muftahu Nada damar aiwatar dadukkan abinda yay k’uduri tunda kowa namasa kallon makusancin Galadima, amma har ALLAH ya wayi gari baimayi wani yunk’uri na shiga d’akinba balle alamun rashin gaskiya, saima aikinsa dayay kama dana mai k’ok’arin bama wani abu kariya, “ya ALLAH ka warware wannan lamari cikin sauk’i kodan wannan bawa naka yasamu nutsuwa shima”. Nuren ya fad’a a fili yana d’aga hannayensa sama alamar rok’o.
      Muftahu dake kallonsa yay murmushi yana amsawa da amin a la66ansa, daga nan yafice abinsa ya koma masarauta, saboda anata kiraye-kirayen sallar asubahi
 ****************
       Misalin 7:30am Munaya ta farka, kamar a kunnen Munubiya itama saita farka, su mom dake d’akin suka shiga musu sannu, cikin tsantsar farin cikin farkawar tasu, dandanan aka kira doctor.
         Alhmdllh babu wata matsala a tattare dasu, aka kikkimtsasu dagasu har yaran daketa barci irinna jinjirai, daga Munu… Har munaya dai kallon y’ay’a biyar sukeyi, amma tunaninsu ko cikin y’ay’an y’an uwansune.
    Doctor Farida data lura da hakan tayi murmushi kawai. umarni tabama Nurses d’in abama kowa nata, kallon kallo akeyi tsakanin Munaya da Munubiya, amma kowa bakinsa yagaza furta komi, saisu kalli juna sukuma kalli jariran gabansu.
    Doctor Farida dai dataga basuda niyyar d’aukar yaran tace “y’an biyu wannan itace k’yautar da ALLAH ya baku, Munubiya 2, Munaya 3.
    Duk waro ido sukayi, Dan Na Munaya ne yabasu mamaki, tunda dukansu sunsan Na Munubiya dama.
     Munubiya ta sakko daga gadonta batareda ta d’auki ko d’a d’aya anata ba, gadon Munaya ta nufo, ta durk’usa k’asa tana rungumo yaran, ga hawaye ga dariya tanayi, saikace sokuwa.
       Munaya ma dai batabi takan nata d’inba, saita nufi Na Munubiya ta d’auka duk ta sakasu a jikinta, k’aunarsu Na ratsa dukkan 6argonta kamar yanda take k’aunar mahaifiyarsu.
     Galadima da Yaa marwan dake tsaye a bakin k’ofa suka kalli juna suna murmushi, kowanne yana mamaki a ransa, anacewa y’an biyu akwai shak’uwa, sukam suna mamakin ta wad’annan Matan nasu, soyayyar dake tsakaninsu tanada ban mamaki da birgewa.
      Galadima ya k’arasa ga Munaya da har yanzu take a tsaye idonta arufe y’an biyun Munubiya na jikinta, had’ata yay itada yaran ya rungume.
     A firgice tabud’e ido, saitaji k’amshin turarensa, tayi baya kad’an yay saurin ruk’ota. Idonsa ya saka cikin nata yana wani murmushin dabata ta6a ganiba daga garesa. Ahankali ya furta haba “Maman y’an biyar a hankali mana”.
       K’aramar harara ta sakar masa, ya saka k’aramar dariyar da tadawo da Yaa marwan daga duniyar daya tafi????, danshifa mutunmin naku har yana Neman sakin layi????????.
      Mom dake bayansu tayi gyaran murya, kowa saiyaja baya daga jikin matarsa????, suna wani susar k’eya.
      Munubiya da Munaya sai suka koma kusa da juna, Munaya ta kama hannun Munubiya a cikin nata. ita mom dariyama suka bata, Dan haka tad’an dara tana fad’in “An sallamemu to yanzu ya za’ayi?”.
     Munubiya da Munaya suka kalli juna, da alama dai basa buk’atar rabuwa, sudai su Galadima kallonsu suke kawai.
       Ganinfa zasuyi daru sai mom tai murmushi, da ido taima Galadima da Yaa marwan magana akan su fita.
    Babu musu suka fice, itakuma takama hannun Munaya da Munubiya ta zaunar a bakin gado. Magana take musu k’asa-k’asa wadda (banajin????).
     Sai naga duk sunyi murmushi suna 6oye fuska. Itama murmushin tayi tana saka musu albarka. Dan murmushin nasu ya tabbatar mata dasun amince.
     Daga nanfa shiri aka fara, kowacce aka had’a mata kayanta da y’ay’anta.
     Gayyar gidansu Munubiya su mama Rabi’a suka kwashi nasu, nasu Galadima ma haka.
     Manne da hannun juna suka fito, mutane sai kallonau sukeyi abin sha’awa da birgewa. Harda masu musu hotuna daga gefe.. 
     Su doctor Farida ma saida suka matso akayi musu hoto danya zama acikin tarihin wannan asibiti.
     Saida Munubiya ta saka munaya a mota sannan takona tashiga wajen mijinta itama, kowanne Na share hawaye, ba’a San ransu za’a rabasuba.
   Saikace wad’anda za’a raba gaba d’aya????, kai ALLAH yabamu ‘yan biyu????⛹????♀⛹????.
★★★★★★★★★★★★
      Tarba ta musamman su Munaya suka samu a masarauta, harma abin yaso basu mamaki, hakan dai baisa Mom tayi sake da yaran ba, duk wani motsi dai idonta Na Kansu, an musu rakkiya har sashensu dayasha gyara, yayinda Galadima keta kar6ar barka ga ahalin wannan masarauta, tun daga hadimai zuwa y’an uwansa na  jini, maza da mata yaro da babba.
       Za’ayi walimar cin abinda data sannu da zuwa ga y’an uku a masarautar k’arfe 8pm, wannan yasa ba’a jimaba aka barsu suka shige Dan Munaya tasamu ta huta.
            Mamaki ya kama Munaya ganin an cika mata gado da tarkacen Teddy’s, wannan abun haushi da yawa yake, kuzo Ku kama jera d’iyan aljanu agado kawai.
     Sudai su mom suka jasu gefe aka kwantar da yaran, itama zama tayi abakin gadon tana dafe kai.
       Aunty Mimi tace, “lafiya dai k’anwa?”.
      “wlhy kaina ke ciwo aunty mimi”.
       Sannu suka shiga yimata, mom tace, “bara laraba tazo ayi wanka kisamu kici abinci saiki sha magani”..   
        Munaya ta amsa da “to” tana d’an kwanciya a bakin gadon.
   
*********
      Laraba amintacciyar baiwar inno tama Munaya cikakken wanka da babu algus acikinsa, itako sai raki takeyi da zille-zille. a haka dai aka gama wannan wanka, lokacin da suka fito sun iske yaranma Mom tamusu da kanta, ana tsaka da shafesu da mai itada Aunty Mimi.
    Munaya dake d’aure da zani ta rufo babban towel a jikinta ta zauna a bakin gadon tana jingina da fuskar gadon, k’asa-k’asa take kallon yaran da mamakin anya kuwa itace wai ta haifesu? koda yake ba’a jayayya da ikon ALLAH ai, tanajin k’aunar yaranta a har cikin jininta, hakama Na y’ar uwarta, amma data tuna zasu rabu kwana kusa sai hawaye suka cika mata ido.
     A dai-dai wannan time d’inne Galadima yay sallama, hannunsa d’auke da Leda fara.
      Aunty mimi da mom dake sakama yaran kayan sanyi suka d’ago duk suka kallesa suna amsa masa sallamar.
     Idonsa akan Munaya datai masa kallo d’aya ta d’auke ido, murmushi yayi kawai ya zauna a bakin gadon yanama su mom sannu.
      Cikin tsokana mom tace, “aikin kud’i nikam nakeyi, musamman akan kishiya sa haushi, bar saurin godemin”, tai maganar tana dungure d’an hancin macen dake hannunta.
     Murmushi kawai Galadima yayi, sai Aunty Mimi CE ke bama mom amsa da “habawa Mom, dukfa kishinki keda Momma kwayi Ku gama, itafa wannan sarauniyar saita za6a ta darje ehe”.
            Mom tai dariya tana mik’ama Galadima ita, “yo da wannan nanannen hancinne zata za6a ta darje d’in? maji magani dai ai”.
            Galadima ya lumshe ido yana manna yarinyar da k’irjinsa, k’aunarta Na rsatsashi, ya sumbaci goshinta sannan ya bud’e idonsa, kwantar da ita yayi akan cinyarsa ya bud’e ledar yana fiddo dabino mai k’yau da tsafta, a bakinsa ya saka ya tauna, kafin ya d’ora bakin nasa akan na yarinyar ya zuba mata, da farko yamutse fuska ta shigayi, taji bak’on abu a bakinta, saikuma a hankali tafara motsa d’an bakin, galadima dai yana kallonta da murmushi, dadai taji zak’i saita mamule abinta.
      Mom tace, “oh su madan kamila kenan, anji zak’i”.
     Dariya duk sukayi, ya d’auketa yamata kiran sallar hud’uba a kunnenta sanan ya ajiyeta a gefe yana fad’in “ALLAH ya rayaki akan sunnah da tafarkin gaskiya”.
       Su mom suka amsa masa da amin.
      Kallon Munaya daketa shafa manta kamarma batasan dasu a d’akinba yayi, yanda taketa wani basarwa shi mamaki tabashi, baiyi zaton hakanba gaskiya, cayake zata nuna tsantsar farincikinta akan yaran?. janye idanunsa yayi ya kar6i d’ayan yaron.
       Shima haka ya tauna dabino ya bashi, sannan yamasa hud’uba da addu’a ya kwantar dashi. Kar6ar d’ayan ma yayi, Wanda bai cika kuzariba, yad’an masa kallon wasu mintuna yana tatta6a jikin yaron, sai kuma ya kalli mom da Aunty Mimi da suma kallonsa sukeyi.
    Mom tace “Yaya dai Sameer?”..  
      K’aramar ajiyar zuciya yayi yana shafa sumar yaron, “mom yaronnan kamar baida kuzarin sauran ‘yan uwansa”.
       “nima na lura da gakan Sameer, amma maybe yanayinsa kenan, kasan kowa da yanayin da ALLAH yake yinsa ai”.
      “hakane”. ya fad’a cikin sauke ajiyar zuciya, sannan ya d’auki dabino shima yamasa tamkar sauran y’an uwansa, yaron yadad’e bai shanye dabinon ba, daga Bayama saiya fara kuka mara sauti.
     Rungumesa Galadima yayi yana hura masa k’aramar iska a kunne da d’an jijigashi, sai kuwa yayi shiru, shima hud’uba yamasa, ya kwantar dashi kusada y’an uwansa amma sai yaron yakuma Sanya kuka, gashi muryarsa bata fita da k’yau.
       d’aukarsa ya kumayi yana murmushi da fad’in “oh little Sameer what happen?”.
          Mom tace, “shagwa6a ce mana”.
        Dariya Aunty Mimi tayi, yayinda Galadima da Munaya suka murmusa, Dan duk abinda ke faruwa tana allonsu ta gefen ido, amma ta basar kamar bata d’akin.
      Fita Aunty Mimi da Mom sukayi suka barmusu d’akin.
     tuni 6angaren ya rikice da k’amshin girki, dan cikin kuyangin da su mom sukazo dasune suke tsara girki wa maijego dasu kansu.
      Tashi Galadima yayi d’auke da yaron a jikinsa ya nufi inda Munaya take zaune, tun d’azun tagama shafa man amma tak’i tashi ta saka kaya.
      Zama yay kusada ita sosai jikinsa har yana gogar nata.
      Da sauri ta yunk’ura zata mik’e, ya saka hannu d’aya ya ruk’ota yana maidata.
     Kallonsa tayi fuska a cunkushe kamar zata fasa kuka, idanunsa ya saka acikin nata yanda bazata iya janyewa ba, aiko duk k’ok’arinta nason ta janye d’in ta kasa, sai cika sukayi da kwalla, dan yana ganin k’yallin ruwan hawayen.
      Yad’an murmusa yana lumshe ido da bud’ewa a kanta. muryarsa cikeda k’asaita da sanyi yace, “kekuma salon taki murnar kenan?”.
      Had’iye kukan dake Neman kufce mata Wanda itama batasan dalilinsa ba tayi, tayi murmushin takaici tana janye idanunta daga cikin nasa, muryarta a sark’e cikin sanyin rauni tace, “Ina tayaka murnar sosai yalla6ai”.
       Lips nashi yad’an cije, ya lalla6a ya ajiye yaron da barci ya d’auka gefen y’an uwansa, Munaya duk tana kallonsa.
      Kuma matsawa yay jikinta sosai ya jawota jikinsa, batayi yunk’urin hanashiba, kamar yanda bata hana hawayenta zubaba. Ya saka tattausan hannunsa yana share mata hawayen, “Friend dukda bansan miya sakaki kukaba ina mai baki hak’uri, wannan ranar bana buk’atar damuwar kowa sai farinciki, musamman ma daga gareki, ina rok’onki alfarmar fansar wannan damuwar taki da farinciki akan kowanne farashi, komai tsadarsa kuwa”. ya k’are maganar da sumbatar sumar kanta.
      Murmushi tayi, ta d’ago daga jikinsa idonta akan yaran dake jere reras abin sha’awa. Shima d’in su yake kallo.
          “bana cikin kowacce damuwa da kake tunani yalla6ai, kawai dai…” sai tayi shiru.
       Kallonsa ya maido gareta, yace, “kawai dai mi yalla6iya?”. ‘ya k’are maganar cike da tsokana’.
       Ta murmusa tana mik’ewa tsaye, wardrobe ta nufa ta fiddo sabbin kayanta cikin na lefe, bata kuma kallonsa ba ta wuce bathroom domin saka kayan.
      Binta yay da kallo harta shige, yasaki miskilin murmushi yana kwantawa kusada yaran, a fili ya furta “yarinya nasan matsalarki”. yay maganar yana sumbatar kuncin na kusa da shi, sauran kuma ya shafa Kansu.
      A haka Munaya ta fito ta iskeshi, ya ta6a wannan ya ta6a wancan, kallo d’aya tamasu ta d’auke kanta.
      Sallamar da akayi a bakin k’ofar ya saka Munaya amsawa da bada izinin shigowa.
    Laraba tashigo d’auke da tire babba.
     Da sauri Munaya ta nufeta ta kar6a, Dan dattijuwace sosai, sannu ta mata tana fad’in “iya aida wanine ya kawo”.
      ‘Yar dariya laraba tayi, tace, “dole na kula da amanar uwar gijiyata ai ranki ya dad’e”.
       Munaya da Galadima suka kalli juna suna murmushi, Dan sunsan inno take nufi.
         Laraba ta juya zata Fifa saboda ganin Galadima na nan.
    Kiranta yay ta juyo, yace, “zokiyi aikinki kar Inno taga ta rame tace baki rik’e amanaba, nima yarana abincinsu suke buk’ata”.
       Hararsa Munaya tayi, yay Biris kamar bai gantaba, saima d’an yatsansa daya saka cikin hannun yaron, shiko ya rik’e gam tamkar yasan minene.
           Laraba tace Munaya ta zauna ga abinci taci..   
     Yamutsa fuska Munaya tayi, kamar zatayi kuka tace, “wlhy iya bakina banajin d’and’anon koda yawuna ma”.
            “hakane ai saidai hak’uri ranki ya dad’e, dama wasu idan sun haihu sukanyi k’am baki, amma a hankali zai canja”.
        Badan munaya tasoba ta zauna, laraba tabata kunu mai k’yau da aka dama don ita, sai k’amshin kayan yaji yakeyi, sai farfesu.
     Kallon abincin kawai Munaya keyi, amma ko kad’an batajin sha’awar ci, ta tuna kwanakin baya da idan taga abinci jikinta har rawa yakeyi wajen son ci, hikimar ubangiji daban ce, ta d’ago ido suka kalli juna itada Galadima dake kallonta tun d’azu, a zuciyarsa yana tuna kwanaki uku rak dasuka shige, yanda ta maida abinci, murmushi yamata ta d’auke idonta ta maida ga abincin.
      A haka Mom ta shigo ta iskesu, zama tayi tana fad’in “yanaga bakici komaiba?”.
        Idon Munaya cike da kwalla tace, “ALLAH mom banajin d’and’ano”.
     Zama mom tai kusada ita, tace laraba taje itama ta karya. Kunun ta d’auka ta tsiyaya a Kofi ta d’iba mata farfesun, “kar6a maza runtse ido ki shanye kunun nan d’iyata”.
      Kunyar Mom ta sakata k’ar6a tana had’iye kwallarta, tafara sha badan tanajin dad’inba, sai dan tsatstsareta da ido da Galadima yayi shida Mom. ahaka dai tasamu tasha yafi rabi, dama yunwar takeji, dad’in bakinne kawai bataji, shima farfesun tad’anci, dandanan tafara zufa. tace,
       “Mom dan ALLAH bara na kunna AC”.
     “a ina?”. ‘galadima ya fad’a yana tashi zaune da sauri’.
      Ita mom ma dariya ya bata, yawani had’e fuska yana harar Munaya, “malama babu wani AC da zaki sakama mutane anan, kina ganin yara duk da mura sukazo duniya saboda rashin jin maganarki…..”
       Mom ta katseshi da fad’in “ai bama zai yuwuba, itada ke jego ko fankace a d’akinnan ai saidai kallo kuma, yanzu ruwan sha ma sai mai zafi”.
       Galadima ya sakko daga gadon yana fad’in “hakan ai shine dai-dai wlhy, remote d’in AC d’in ya d’auka a lokan gefen gadon ya masa yanda bazata iya control d’insa bama gaba d’aya, sannan yafice abinsa yana murmushin mugunta.
     Mom ta girgiza kai kawai, a ranta tana mamaki canjawar Sameer……
     Maganarsa ce ta katse mata tunani, harya fita ya dawo baya, “mom ga maganinta nan tasha, kuma yaranan yunwa sukeji”. ‘yak’are maganar cikin marairaicewa’.
    Dakuwa mom tamasa, “Sameer kaci kidanku, wai yaushe kama fetsare hakane ban saniba?”.
      Fita yayi yana dariya, ta kirashi da sauri. Kuma dawowa yayi, tace, “kasandai Doctor tace a nemi madara, naga kuma bama kada niyyar hakan”.
       Gaba d’aya fara’ar fuskarsa ta d’auke, yad’an shafi girarsa da d’anyatsa d’aya yana fad’in “Mom wai wace madara ga abincinsu?, ALLAH dai ai shiya haliccesu, kuma shine zai wadatasu da abincin nasu, amma kawai sai a kama wani danna musu wata madara? dan ALLAH mu ajiye zancen madarar nan ma gefe mom”.
        Numfashi mom ta sauke, tasan murd’ad’d’en halin Galadima da dagewa akan ra’ayinsa, cikin kwantar da murya tace, “na yarda da maganarka, amma ita za’a tausaya mawa, shayar da yara uku bafa abune mai sauk’iba Sameer, wasuma d’ayane idan suna da fargabar shayarwa kaga duksun k’are sun lalace, koda dai sau d’ayane sai a ringa basu madarar a rana, tunda ALLAH dai baya hanaka yanda zakayi bane”.
         Tashi Munaya tayi tana hawaye, taje ta hau gadon kawai tayi kwanciyarta, ta kula Galadima yacika son kansa, tanaga saita tuna masa da matsayin auren nasu da alfarmar yarda ta haifa masa y’ay’an dayake neman nuna mata mulki a kansu, aidai abin shayarwar a jikinta yake, sai kuma yanda taso tayi da kayanta, dolene ta takama wannan homar tasa birki.
     Daga Mom har Galadima da kallo suka bita, yaja guntun tsaki yana juyawa zai fita.
     Mom tace, “zaka siyo d’in?”.
      A k’ufule yace, “zan duba”. Yay ficewarsa. shifa ya lura yarinyarnan ma batason yarannan, shin bak’in ciki take ALLAH yamasa k’yautar abinda kud’i baya sayane ko me? ALLAH zaiyi maganinta kuwa.
     ????????ho Galadima, uwa ta ta6a k’in d’antane????????.
★★★★★★★★★★★★
           Mama Fulani dai yau tagaza gane kanta, duk yanda taso danne zuciyarta tayi murnar koda ganin idone ta kasa, shiyyasa ko zuwa wajen tarbarsu batayiba.
     Takuma hana dukkanin bayinta da kuyangi shiga inda take.
      Abinda bata saniba idon Galadima fes yake akan dukkan Wanda ya tayashi murna da samun k’yautar ALLAH, wad’anda bama su fitoba sun shiga black lists, kuma d’aya bayan d’aya saiya kartama kowa rashin m acikinsu.
★★★★★★★★★
        Innaro kuwa dai saita hau tsiya dataji labarin su Munaya kowa mijinta ya d’auketa zuwa gidanta, tahau zazzaga masifa anmata ba daidaiba, babu Wanda ya kulata, dan masu zugatan suma hassada ta ishesu, basuda kuzarin taya 6era 6ari????..
        Haka tagama jarabarta takoma gida tana huci, Abba yasha dariya, danshi lamarin mahaifiyar tasu yanzu kallon rikicin tsufa kawai yake masa, inba rikicin tsufaba miye abin tada jijiyar wuya anan? Sunada damar hana yaran komawa gidajen mazajen sune?.
        Shikam baba k’arami ma lokacin da take jarabar zuwa yay ya ra6a ta gefenta ya fice daga gidan.
     Ai lamarin innaro sai ita????????????.
******************
       A 6angaren Munubiya ma Alhmdllh, dukkan wata kulawa mama rabi’a tana tsaye akan ‘yarta da jikokinta, sai zuba mata gata akeyi da k’yak’yk’yawar kulawa mai ban sha’awa.
   Suruka ta gari dadi alkur’an????????????????????????.
★★★★★★★★★★★★
            Mom dai da k’yar suka lalla6a Munaya itada Aunty Mimi ta amince ta shayar da yaran, suna sha tana kukan zafi kuma????,  sunsan zataji zafi tunda Na farkone, ga yaran a buk’ace suke dama, amma kukan datake yawuce Na zafi kad’ai, (basusan harda haushi Galadima bane????????).
      Mom data fahimci hakan saita fara lallashin da nuna mata muhimmanci hak’uri, su maza komai zasu iyayi akan y’ay’ansu, musamman ma shi da yake tsaka da d’okinsu yanzu, karma tabari irin wad’annam abubuwan su dameta, shima yafad’ane kawai amma zai sayo madaran”.
        Itadai Munaya kai kawai take d’agawa amma batace uffanba, dan tagama Sanin Galadima da halinsa Na kafiyar tsiya da dagiya akan ra’ayinsa.
     Bayan duk sunsha sun k’oshi Aunty Mimi tace ta kwanta ta huta kafin time d’in walimar yayi. ALLAH ya taimaketa maganin yasata barci kuwa, yaran Na gefenta suma suna nasu barcin, kowa cikinsa ya cika kenan????.
         Ajiyar zuciya Aunty Mimi ta sauke tana murmushi, tace, “Mom d’an nan naki bazai canja ba dai ashe? lamarin Sameer saishi wlhy, koda bayaso susha madarar saiya fad’a da harshe mai dad’i ba fad’aba”.
         “Humm, kibari kawai, nifa harna fara murnar ya canja, Ashe yana nan yanda nasan kayana, yarinyar tanada hak’uri kuma wlhy, dan zama da mai halin Sameer saika daure, muma iyayen idan mun k’ureshi ba iya mana kawaici yakeba”.
         Aunty Mimi tayi dariya, “papi ne mai tankwarashi kobai soba ai, idan yak’i bari abasu madaran dashi kawai za’a had’ashi, komin wadatar nono shayar da yara uku ba sauk’i ne dashiba, balle ita farin Shiga ma”.. 
           Mom tace, “hakanma shine kawai mafita ai”.
***************************
*_8:15pm_*
        Liyafar cin abinci tafara gudana a babban d’akin taro Na masarautar gagara badau, Munaya da y’an uku duk sunsha k’yau, hakama uban gayya Baban y’an uku Galadima, duk d’insu sunci kwalliyane cikin ainahin kayan sarauta, yaranma an nad’esu cikin k’ananun alk’yabbu. (Gado kenan????)
        Kwai da kwarkwata Na gidan nan zaka sameshi a wajen, saidai marasa lafiya da wad’anda basa nan, mai martaba ma yana wajen, dan shine da Kansa ya shirya liyafar domin taya d’ansa murnar k’aruwa da kar6ar bak’uncin jarirai, yaran duk suna kusa dashi cikin d’an gadon da aka ajiyesu a ciki.
      Kowa anan yake zuwa ya lek’asu, yamusu addu’a.
       Yara sunsha addu’oi da k’yaututtuka ga iyaye da kakanni, abin zakkyau da birgewa.
     Ita kanta Munaya tasha nata k’yautar.
       ( k’yauta da bajinta kan saka zama isashe a gidan sarauta, wannan babbar al’adace tamasu mulki a masarautun k’asar hausa, shiyyasa suke ado da ita akowanne motsinsu????????????).
      Tsakanin Munaya da Galadima babu uhum babu um-um, sai y’ar wullama juna harara (????nifa dariya suke ban), banga abin jin haushin junaba, duk da Na lura ita dama Munaya akwai haushi kaine ka jamin shan wahala????, kaikuma Galadima k’asaita da jinkai ya sa kakasa fahimta balle kayi lallashi da kwantar dakai aji da y’an jariranka????.
      To maji dai maga yanda za’a kwashe????.
         Sai 11 dai-dai taro ya tashi lafiya kowa ya kama gabansa.
      Shirin kwanciya Munaya tayi, suma yaran aka musu, saiga Galadima ya shigo cikin tasa shirin kwanciyar shima, mom tace, “yauwa Sameer ya za’ayi kwanciyar kenan? A falo zaka kwanta saboda tsaro ko?”.
     Murmushi Galadima yayi yana shafa kansa, yace, “kai Mom wai saboda tsaro”.
        “ALLAH kuwa Sameer, lamarinne yanada ban tsoro ai, dukda nasan ga dogarainan suma suna aikinsu, gakuma mu kammu, amma dole saida namiji a kusa, da canai shima Nuren ya dawo nan Ku had’u”.
      “mom kincika tsoro gaskiya, karki damu, ko ina Na sashennan akwai CCTV camera, kuma koyaya aka ta6a k’ofa ko windows akwai securitys a jiki zanji insha ALLAH”.
          “To shikenan Alhmdllh, ALLAH yak’ara tsaremu da tsarewarsa”.
    Galadima ya amsa da “amin” yana matsawa jikin gadon wajen yaran.
       Munaya dake saurarensu a ranta tace to ALLAH ya k’yauta, a gidanka kana zama saida tsaro inaga kafita?, amma jibarsu a awajen walimarnan kaikace kowa zuciyarsa fes take babu wani k’udiri, lamarin sarauta sai ALLAH, kaita buri tamkar ALLAH yamaka alk’awarin dawwama a cikin duniyar ne, bazaka mutuba bazaka tsufa ba, ALLAH ka iya mana da iyawarka, da ace inada dama saina cirema yaranan burin sarauta a ransu, amma ya zanyi, tarigada ta zama jininsu sai dai addu’a kawai……. Saukar numfashin dataji a gefen wuyanta ya sakata saurin dawowa daga tunanin data tafi, ta waigo da sauri sai taga Galadima.
        Fuska ta had’e shima yaci serious yana gyara zama.
    Waige-waige ta fara saitaga babu kowa a d’akin, ashe Mom ta fita.
      Baki ya ta6e ya nuna mata k’ofar bayi da d’an yatsa alamar mom tana ciki kenan.
      Cikin zaro ido ta kalli yanda yazo yawani shige mata, saitaja baya, ai da kunya dai mom ta fito ta gansu a haka wlhy.
     Yanda tayi d’in sai yaso bashi dariya, amma saiya had’iye, ya ciji lips nashi yana kallon yaransa, “tunanin mikikeyi ne? kinsan dai doctor tace jininki har yanzu bai gama sauka ba gaba d’aya, so ki kula, shi tunani baya kawo mafita sai matsala”. ya k’are maganar yana mik’ewa tsaye, itadai kallonsa kawai takeyi, bata ankaraba taji saukar tagwayen kisses a goshinta da kan bakinta.
      Idanu ta ware waje baki bud’e, ko kallonta bai sakeyiba ya fice abinsa yana murmushi.
     Mom data fito daga bayin ta girgiza kai kawai, don ganinda Galadima yamatane ya sakashi ficewa.
         Kallon Munaya tayi tace, “to rufe bakin kema”.
     Kunya ta kama Munaya taja bargo tarufe har fuskarta tana fad’in ka kasheni wlhy yalla6ai.
      A falonsa ya iske Nuren haryayi shirin barci shima, yana zaune yana shan tea da laptop a gabansa yana aiki, Galadima ya zauna yana sauke numfashi………….????
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????_*l

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button