BAIWATA 11
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
SADAUKARWA GA
*AHALINA*
GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.) 🤜🤛
(Burinmu d’aga muryoyinmu sama domin anfanar da al’umma had’e da ciyar da adabin hausa.)
☆ [G. M. N. A] ☆ 📖🖊️
Bismillahir rahamanir rahim
_11_
Yana shiga madafar ya tsaya cak! Ya na ƙare mata kallo daga baya, rumgume hannaye ya yi da tunanin to ita haka take shigarta kullum? Ko kuma dai baƙunta ce ta sa haka? Sai kuma wata zuciyar ta raya masa “Idan baƙunta ce ai ƴan uwanta ma baƙuntar suke, me ya hanasu kama jikinsu kamar ita?”
“Tarbiyya ce kawai.” Wata zuciyar ta bashi amsa, abaya ce jikinta da kallabinta wanda sam jikinta bai bayyana ba, a hankali ya sauke hannayenshi daga ƙirjin ya shiga takawa gareta, bayanta ya tsaya ya ɗan dubi tukunyar da ke kan wuta wacce take soya naman da ta samu a fridge, tsilalar da yake na jajjagen da ke jikin naman kuma aka saka cikin mai me zafi, wannan tsuwar ce ta hanata jin tako daga bayanta saboda tana ta ƙoƙarin kare kanta kar mai ya ki ƙonata.
Ba ta ankara ba, ba ta san da faruwar abun ba, hannaye bibbiyu kawai ta ji sun zagaya kumkuminta an kwantar da kai a bayanta cikin wata tattausar murya yace ” Leema sann…”
Tunda ta ji irin ruƙunƙumewar da aka mata ta sa ma ranta mace ba za ta mata haka ba, ko da ta ji muryar Mu’az tun bai gama maganar ba ta juyo a mugun tsorace kuma a fusace ta ɗauke fuskarshi da mari ta bayan hannunta. Kallon kallo su ka tsaya kowa da irin fitinannen kallon da yake aika wa ɗan uwanshi, ita kam mamaki da ɓacin rai ne suka lulluɓeta cike da dana-sanin zuwa gidan nan da ta yi wanda sam babu alkairi a ciki sai jafa’i da ta ke gani kala-kala.
Shi kuma mamakin ƙarfin halin ta da kuma tsoron da ya ke hangowa a idonta mai ɗauke da ɓacin rai na aljabi yasa shi sakin murmushi, a hnkali ya jaye hannunshi daga kumcinshi ya ɗa ja baya kaɗan, cikin raha alamar dai abun bai wani ɓata ransa ba yace “Na samu abinda na ke so, wannan shi ne abinda ya kamata na gani a tare da wacce na ke so sa’ilin da wani wanda bai da hurumi a kan ta ya kai hannunsa jikinta, hakan alamu na cewa za ki iya yankar duk wanda ya yi ƙoƙarin taɓa min halaliyata.”
Wasu mugayen hawaye ma su zafin gaske ne suka kwaranyo mata daga kurmin ido na takacin wannan rana da ta risketa, tunda ta balaga ko Mamanta kunya take ji ta rumgumeta bare kuma Abbanta, amma yau ƙato da ba ta da haɗin komai da shi ne ya kwanta a bayanta tamkar wata matarsa. Hannu tasa ta share hawayen ta furta “الحمد لله الذي بنعمته تتم الصالحات (Godiya ta tabbata ga Allah wanda saboda ni’imarsa ce kyawawan ayyuka suke cika).”
Da sauri ta yi azamar raɓashi za ta bar wurin duk da kuwa ta na jin naman da take suya ya na neman ƙonewa, da sauri ya tare gabanta har tana neman faɗawa kan shi ya yi saurin faɗin “Dakata.”
Da sauri ta kalleshi cikin muryar kuka da kuma ƙunar da ke cin zuciyarta tace “Ka matsa min a hanya, idan ba haka ba wallahi zan maka ihu.”
Cike da isa ya rumgume hannaye a ƙirji yana murmushi yace “Bismillah, yi, ko ba ihu ba? Yi ihu ki ce kwarto ne ni.”
Da mugun sauri ta liƙe kunnuwanta tana fashewa da kuka ta durƙushe ƙasa tana faɗin “Dan Allah ka rabu da ni, ka tafi ka bani wuri, wai me yasa ba ku da ɗa’a ne? Ku wasj irin karnuka ne?”
Da wani mugun sauri ya finciko hannunta da alamar ya ji zafin kalmar ta ƙarshe, ba tare da ya saki hannunta ba ya haɗata da bango ya matse mata wuri sosai, tsabar tsoron da ya kamata yasa ta duƙar da kanta ta gandarawa hannunshi cizo. Amma da ke ranshi ya ɓace da ta haɗashi da kare sai ya yi kamar bai ji ba, matse hannunta ya sake yi sosai har ta saki ƙara tana matse fuskarta, Mu’az kam mutum ne mai son raha da barkwwanci, sai dai akwai abun da sam ba ya ɗauka kuma a take ranshi ke ɓacewa. Cikin jin zafi ya kalli fuskarta yace “Wa ye kare? Ni ki ke haɗawa da dabbar da ake ajiyewa dan tsaro kawai?”
Wani kukan ta sake sakawa mai ban tausayi tana neman sulalewa ƙasa a ƙasan maƙoshi ta furta “Hannuna.”
Da sauri ya kalli hannunta da ya matse, a hankali ya sassauta mata riƙo yana jin tausayinta na mamaye zuciyarshi, saida ya saki hannunta gaba-ɗaya sannan ya sunkuyar da kai yace “Ki yi haƙuri, kuma nagode da marina da ki ka yi.”
Juyawa ya yi har zai fita sai kuma ya tsaya, a hankali ya tako ya dawo gabanta ya tsaya duk da ta rufe fuska tana kuka, cikin tattausan murya mai kashe jiki yace ” Ina son ki.”
Da sauri ya juya ya fita a madafar ya ma manta me ya shigo da shi da fari, tana jin ya fita da sauri ta ƙarasa gaban gas ɗin ta kashe wutar, tana kwashe naman ta na sako da hawaye har ta kammala abinda ta fara sannan ta barsu a nan ta fita a madafar, tana haurawa sama tana tunanin tafiyarta gida ne, ba zata iya zama a gidan nan ba ko kaɗan, ba ta sani ba ko mahaifinsu ya san haka gidan yake ya turosu? Amma dai ba ta zauna ba ita kam, dan in suka zauna daga ita har ƙannenta cikunna ne za su bayyana garesu nan da kwana kaɗan, dan ita tsoronta kar shi ma uban haka ya ke ya fara ƙare musu kallo.
Tana shiga ɗakinsu da kuka ta share hawayenta ta nufi inda jakarta take da kayanta da basu wuce guda uku ba bayan na bacci, Hadeeya na kwance da waya a hannunta, Hameeda ma kwance take suna kallon hotuna a waya ita da Ummee, da kallo duk suka bita sanda ta ɗauki jakar tana tattara kaya tana zubawa ciki, saida ta gama tsaf ta ɗauki zunbulelen hijabinta ta saka, ta ɗauki jakar kenan za ta fita Hameeda da ta fi damuwa da abinda ta ga Saleema na yi tace “Ina za ki je?”
Juyowa ta yi ta kalleta tace “Gida, sai kun zo.”
Da mamaki Saleema tace “Gida kuma? Abba fa cewa ya yi…”
Cike da raini Hadeeya tace “Ki barta ta tafi mana, ai ta san Abba ya faɗa mana zai turo a ɗaukemu bayan kwana biyu, shi ne dan ta rainashi za ta ce za ta tafi yanzu.”
Dogon tsaki ta ja ta maida hankalinta ga abinda take, Hameeda kuma ci gaba da kallonta tayi har saida ta fita a falon, tana sauka ƙasa Hajia Rabi na fitowa daga madafa, dama kuma ta shiga ne dan ɗorawa Alhaji abinda ya buƙata, ta samu abun kari an gama shiryawa amma ba ta ga Saleema ba, fitowarta dan ta duba ɗakinsu ne sai kuma suka haɗe.
Cike da kulawa da kuma fara’a a fuska tace “Yawwa Saleema, na duba ciki ai ban ganki ba, ashe har kin gama girkin? Kai gaskiya Saleema kin yi ƙoƙari, dama haka kika iya girki?”
Hijabin da ta jawo tana ƙara goge fuskarta yasa Hajia Rabi ganin jakar dake hannunta, da mamaki ta matso kusanta tana faɗin” A’a! Saleema ina za ki je da jaka kuma?”
Sunkuyar da kanta tayi cike da kunya da shaƙaƙƙiyar murya tace” Mama gida nake so na tafi, ina kewar Mamana ne… “
Da sauri ta riƙo hannun Hajia tana ci gaba da faɗin” Dan Allah Mama kar ki hanani tafiya, ina so na ga Mamana ne.”
Sosai Hajia ta shiga mamaki da kuma zuba mata ido tana nazarinta da kuma son gano gaskiyar kalamanta, cike da kokonto tace” Saleema, wani abu aka miki ne a gidan da ba ki ji daɗi ba?”
Da sauri ta girgiza kai tace” A’a Mama, ba abinda aka min, nk dai kawai ki barni na tafi.”
Sakin hannunta tayi ta ƙara riƙe jakarta ta ɗan raɓata tace” Nagode Mama, sai anj…”
Riƙota Hajia tayi tace” A’a Saleema, ba zan barki ki tafi ba, ko dai ki faɗa min abinda aka miki? Ko kuma na kira Alhaji na faɗa masa.”
Kamar za ta durƙusa ƙasa ta shiga gurfanawa tana faɗin” Mama, Mama kar ki faɗa mana dan Allah, Mamata na ke ji kamar tana cikin wani hali, ki barni na je na duba idan na sameta lafiya sai na dawo.”