BAKAR WASIKA 3

Page -3️⃣
Shigowar Daddy ne yasa Momy ta cire farin gilashin idonta tana murmushi.
“Ranka ya dade an fito?”
Kusa da Amal ya zauna yana murmushi.
“Allah ya yarda”
Ya fada yana karewa katon falon kallo ganin Momy ce kawai sai Khadija da kuma Kabir, abun da ba kasafai yake gani ba, ya saba every weekend yana zuwa falon Momy ya zauna tare da ita da kuma yaransa, kowa ya fadi bukatarsa ayi hira a bawa juna shawara, ayi nishadi. Sometimes kuma shi zai kira su a bangarensa a tare a can.
“Daddy barka da wuni”
“Yauwa, Son”
Ya amsawa yana yi ma kowa kallon tsanaki, ciki har da yar autarsa Amal da ta wani hade rai.
“Hajiya ya ga falon ku kadai? Ina sauran yarana suke?”
Momy ta kalli Kabir dake kallonta sannan ta kalli Amal kamin tace komai Kabir ya tari numfashinta.
“Daddy yaranka biyu fushi suke da juna, kasan Angry Birds ne”
Daddy ya kalli Momy.
“Since when?”
Kabir zai sake magana Daddy ya dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu, wanda hakan ke nuna kai tsaye Momy yake son ta amsa masa tambayarsa. Momy ta sauke ajiyar zuciya.
“Ni ma dazun nan na sani…”
A tsanake ta labarta masa abun da ya faru ciki har da fadan da tai ma Leila.
“Amman baki fada min ba? Taya zaki bar Mu’az ya fita ba tare da yayi breakfast ba? And baki dama ki san a wane hali yake ba?”
Momy ta lumshe ido ta bude tana murmushi.
“Wani lokacin kana maida Talba kamar wani karamin yaro, ya san yadda zai kula da kansa Alhaji”
“Ko da Mu’az zai shekara dari matukar ina raye to shi yaro ne a gurina, a shirya mana abincin rana tare”
“An gama ranka ya dade”
Ya mike tsaye sai Amal ta kalleshi.
“Daddy ni ma fa kaga ina fushin nan amman baka ce komai ba”
Sai a lokacin Daddy ya tuna da tana gefensa sai ya kalleta yana murmushi.
“Amal sorry wata taba ki?”
Ta nuna Kabir sai Kabir yai saurin daga hannayensa sama ya mike tsaye.
“Na ma bar muku falon”
Kamin Daddy yace komai ya nufi kofar fita daga falon da saurinsa yana murmushi.
“Mu yi masa uzuri amman yau kawai next idan ya sake tsokanarki zamu raba gari da shi”
Daddy ya fada yana kallon kyakkyawar yarsa. Sai ta sakar masa murmushi.
“Toh Daddy”
“Good”
Cewar Daddy yana ciro wayarsa ya kira Talba, ringing daya yai picking kamar daman can kiran yake jira.
“Hello Daddy”
“Mu’az kana Ina?”
Ya kalli katon office din da yake ciki kamar mai son tantance inda yake.
“Office Daddy”
“Me kake a office? Yau Weekend?”
“I don’t know…Getting some fresh air”
“Baka fada min kana da damuwa ba, mu da kai ba abokai ba ne? Ba ma boyewa juna abu?”
Wani irin kasaitaccen murmushi ne ya bayyana a fuskarsa, ya mike tsaye daga inda yake zaune ya nufi windows.
“Daddy ba irin wannan ba you know dan crisis ne kadan”
Daddy ya tabe baki yana juya fuska kamar Talba na gabansa.
“Uhm.. Ka dawo gida yanzu zamu yi lunch tare”
“Okay Daddy Allah kara maka lafiya, i love you”
Daddy yayi murmushi ba tare da yace komai ba ya sauke wayar, sannan ya nufi wata kofa a dayan bangaren falon wanda zata sadashi da bangarensa.
“Ita Leila ba ya bace kenan? Da ba zaka kirata ka tambayi inda take ba?”
Daf da zai wuce Momy ta yi wannan maganar sai ya juyo ya kalleta, sannan ya dauke kai ya bude kofar ya fice.
Sai da ya rufe kofar sannan Momy ta tabe baki ta kai hannunta ta dauki wayarta ta kira Leila, sai da wayar ta kusa yankewa sannan Leila ta daga.
“Leila kina ina?”
“Gidansu Madina”
Ta amsa murya can ciki.
“Ki dawo da wuri, and make sure kin ci abinci”
“To Momy”
Momy ta sauke wayar sannan ta mike tsaye ta nufi kitchen.
Misalin 2:30pm Talba ya daka motarsa harabar Daddy, ya fito ya nufi bangarensa kai tsaye hannayensa duka biyu zube a alhaji, tafiya yake kamar wanda baya son shiga bangaren, haka yake idan yana fushi be cika son ya rabi mutane ba ko kuma mutane su rabe shi, a tunaninsa tare da kowa zasu ci abinci, domin Daddy ya saba zuwa bangaren Momy ya zauna a ci abinci rana tare ko na dare wani lokacin har da na safe, sai dai yana yin haka ne kawai ranar kun Assabar da Lahadi. Domin ranar weekend ba ya fita ko’ina sai idan fitar mai dalili ce kamar daurin aure ko wani abun, wannan al’adar ba shi kadai ba har yaransa sun saba da ita, every weekend zaka samu kowa a gida sai mai dalilin fita yake fita.
Ya samu kusan dakika 40 zuwa 50 sannan ya danna door bell din kofar falon Daddy, babu bata lokaci Amal ta bude masa kofar.
“Ya Talba”
“Lil Sis… Waye da waye a ciki?”
“Just me and Daddy”
Ya sakar mata murmushi sannan ta shiga cikin falon, tun da ya hango dinning din babu komai a kai ya tabbatar daga shi sai Daddy za su ci abincin. Kai tsaye ya wuce karamin Falon Daddy inda ya saba zama. Yana shiga ya samu Daddy zaune saman kujera yana amsa waya, sai ya zauna a inda aka jera manyan kuloli ya dauki plate biyu ya zubawa Daddy shimkafa, ya zubawa kansa a dayan plate din sannan ya bude miyar dake ta kamshin naman kaji ya zuba ma kansa kadan domin ba ya son miya tai yawa a abinci ya zubawa Daddy ta jera kofuna biyu ta zuba musu lemu ya hada komai sannan ya dauki na Daddy ya dora masa a dan karamin center table dake gefen kujera da Daddy yake kai. Sannan ya koma ya dauko na shi ya dawo kusa da Daddy ya zauna a kasa, ya soma cin abinsa yana kallon katuwar plasma dake karamin falon, Bayan Daddy ya gama wayarsa ya kalli Talba.
“Na lura har yanzu baka san ka girma ba Mu’az, ya kamata ka koyi hakuri da iya danne fushi, idan ina kiranka na damu da inda kake, wata rana bana nan, domin akwai rayuwa akwai mutuwa, na san kana kokarin ganin ka kawarda damuwa a zuciyar wasu musamman yan’uwanka, amman kai baka san yadda zaka yi ka cire kanka a damuwa ba, sai dai ka karawa kanka”
Talba ya dakatar da cin abinci da yake yana sauraren Daddy ba tare da ya kalleshi ba.
“Ka daina fushi da abinci idan ranka ya bace, And su mata ba a fushi da su, lallabasu ake, idan ka san wahalar da na sha kamin ya auri Amina sai ka ji ka tsani matar nan, amman haka na daure dan marayan Allah da ni har Allah ya ba ni ita”
Talba ya kalli Daddy yana murmushi mai sauki.
“Haba Daddy”
Daddy ya kalleshi yana dariya.
“I’m telling you my friend”
Daddy ya kai hannunss ya fara cin abinci.
“So haka zaka yi hakuri kai ta lallabata, mata soyayya suke so da kulawa, no matter how rich they are, anya ma kana kiranta da safe ka ji ya ta tashi? Like hello Baby how was your night?”
Talba ya saka dariya sosai har yana kwantawa jikin kujerar dake bayansa. Daddy ma Murmushi yai.
“Yes… Gida daya muke da Hajiya kuma a guri daya muke kwana amman kana gani kullum sai na gaishe, ni ban san abun da yake damun ku yaran yanzu ba, mu a da kunya da rashin wayewar addini ya saka iyayenmu da mu kanmu ba su yi wasu abubuwan na more rayuwar aure ba, amman ku a yanzu ga ilmin addini da na zamani a arha ga wayewa amman kuke ta zaman matsalar zamantakewar aure, ban san miye matsalar matasan yanzu ba”
“So that’s mean nine mai laifi kenan?”
“Kai ne mana, taya zaka samu mace kai tsaye da irin wannan maganar, bana jin yadda kake zaunawa kai hira da ni kana yi da ita ma, kawai kai gaka boss, gaskiya you’re not romantic at all”
Daddy ya karasa yana wani yatsina fuska, wannan karon dariya sosai Talba yai har muryarsa tana fita kamar ba shi ba, dariyarsa ce ta saka Daddy murmushi mai sauti.
“Trust idan baka canja ba, za a iya kasa ka”