

A sakon da ta wallafa a shafinta na Intagram ranar Asabar da daddare, tauraruwar ta ce ta ji dadin rawar da ta taka a cikin shirin, sai dai ta ce ba za ta iya ci gaba da shi ba saboda wasu dalilai na kashin kanta.
Amma wasu majiyoyi sun tabbatar wa BBC Hausa cewa ta dauki matakin ne saboda rashin jituwar da aka samu tsakaninta da mai shirya shirin kuma shugaban kamfanin Saira Movies, Malam Aminu Saira.
Nafisa ita ce babbar tauraruwa a shirin na Labarina mai farin jini a tsakanin ‘yan kallo inda take taka rawa a matsayin Sumayya.
Nafisa ita ce babbar tauraruwa a shirin na Labarina mai farin jini a tsakanin ‘yan kallo inda take taka rawa a matsayin Sumayya.
Janyewata daga [shirin] a wannan lokaci ya faru ne saboda yawan da ayyuka da suka yi mini, ganin cewa hakan ba zai ba ni damar shiga wajen daukar fim din na ‘Labarina’ ba,” a cewar tauraruwar.
[ad_2]