Sultaan Hausa Novel

SULTAAAN 3

???? S U L T A A N

Mss Flower????

FITATTU HUƊU????

RESEMBLANCE OR SIMILARITIES OF STORY/LIFESTYLE SHOULD BE CONSIDERED AS TOTAL COINCIDENCE

FIRST CLASS WRITERS ASSO…

       *03*

LAILA POV

Misalin sha ɗaya na dare ne, sai juye-juye take ta kasa bacci don tunanin Sultaan ya hana mata saƙat, Allah Ya sani tsananin sonsa da take da zai so ta ko rabin rabi ne babu abin da zai sanya ta ja shi su gudu don ta san ko sama da ƙasa za ta haɗe mahaifanta ba za su bari ta auri bawa ba, amma wani irin mugun so take masa wanda ita ba ta duba wani class ɗinsa, soyayyar shi azalzalar zuciyarta take, da son shi ta girma har kawo yanzu, tun ba ta san so ɗin ba ta fahimci a kullum burinta ta yi tozali da shi, wata iriyar ajiyar zuciya ta sauke tare da duro da ƙafafunta daga ɗan gadon da take kwance. Janyo mayafinta kawai ta yi ta fice daga gidan cikin sanɗa, duk da kasancewar duhu ya yi sosai a garin amma ba ka rasa tsurarin mutane da dandali-dandali na samari suna gasa wata dabbar, wannan ɗabi’arsu ce saboda tsaron garin wasu sai su kwana a haka, wani irin sanyi ake ga iska sai kaɗawa take dalilin ruwan saman da aka ƙare babu jimawa, a hankali ta tura ƙofar gidansu Sultaan kasancewar ƙofar ta kara ce babu wani rufeta da suke, gidan ba baƙonta ba ne, hakan ya sa ko da ta ji shi tsit sai ta nufi hanyar ɗakinsa, ɗage labulen kabar ɗakin ta yi tare da shigewa, hasken fitilar ƙwan da ke kunne ce ya ba ta damar hangosa kwance kan tabarma yana bacci, ƙarasawa ta yi inda yake tare da tsura masa idanunta da suke cike da sonsa haɗe da wutar sha’awarsa, ɗan lumshe ido ta yi da tayi tozali da faffaɗan ƙirjinsa a buɗe wanda ya kuma bayyana cikar zatinsa na ɗa namiji, mayafin jikinta ta yaye tare da cire rigar saman da ta suturta jikinta, take wata farar riga ƴar ƙarama cotton mai hannun vest iya cinyarta ta bayyana, a hankali ta kwanta gefensa tare da shigewa cikin jikinsa tana shaƙar ƙamshinsa.

Firgigit ya farka daga bacci, wani irin hankaɗata ya yi daga jikinsa ya ɓata fuska yana bin ta da wani irin mugun kallo.

Kuka ta fashe da shi tana cewa ” me na yi maka ne da ka tsaneni?, da ina da iko da zuciyata da na jima da cire soyayyarka na watsar ko don kana bawa ƙasƙantacce, da ƴancina, da gatana, da arziƙina ban da so me zai sa na dinga bibiyar bawa kamar kai, ka aminta da soyayyata Sultaan na roƙeka, mu gudu mu bar garin nan, duk da kana bawa ni zan zauna da kai har abada!” Ta ce tana ɗora tafin hannunta saman cinyarsa tare da ɗan matsawa.

Janye hannunta ya yi tare da miƙewa tsaye, ya ba ta baya. Rungumesa ta yi ta baya ta zagaya hannunta zuwa ƙirjinsa tana sakin ajiyar zuciya ta ce “ka aminta da Ni, mu gudu mu bar garin nan, gwala-gwalaina sun ishemu arziƙin duniya”

Cikin wani irin fushi ya tureta tare da faɗuwa ya ce “ke wace iriyar nacacciya ce, har abada ki saka a ranki ba zan taɓa sonki ba, bare har na bar mahaifana na gudu tare da ke, ki fice min a nan, kina haddasa min ciwon kai”

Wani irin raɗaɗi take ji akan dukkan furucinsa, murmushi ta saki duk da ruwan hawaye na ɗiga ta ce “kai bawa ne, ka yi kaɗan ka wulaƙantani, don Allah Ya yi maka kyau ba yana nufin sunanka ya tashi daga bawa ba ne, a’a har yau a ƙasƙantacce kake, dubeni da kyau na fi ka da komai, da ƴancina, gatana,darajata, haka a matan garin nan na kasance zinariya, don na ba ka zuciyata sai ya zama tsanin da za ka wulaƙantani?!, Ka amince da ni mu raya daren nan cikin ƙauna, na yi maka gatan duniya, ka bijire min na shirya maka gadar da za ta rufta da kai!,ɗau zaɓinka!” Ta ce tana yaye dogon gashinta da ya rufe mata halittar ƙirjinta tare da turowa don jan hankalin Sultaan.

Ya cije leɓensa ya ɗan yi murmushi ya ce “ko za ki yawo tsirara ba za ki ɗauki hankalin Sultaan ba, ki fice min” ya mata nuni da ƙofa.

“Ko dai kai ba cikakken namiji ba ne?” Ta ce da ɗan murmushi yayin da take ƙoƙarin cire rigarta, bai tankata ba kuma ba ta damu da hakan ba ta miƙe tare da shiga gabansa tana takun da ke sanya ilahirin halittar jikinta girgiza, gabansa ta zo ta tsaya ta ce “mu gani, idan na tabbatar da halittarka ba ta cikakken namiji ba ce daga yau zan shafa maka lafiya, don babu abin da zan so ga mata maza, in kuwa akasin hakan ne a zaɓin da na ba ka a farko dole ka ɗau ɗaya” ta ce tana ƙoƙarin kama tazugensa. Wani irin wurgi Sultaan ya yi da ita yana cewa “ni ba mazinaci ba ne, akan ki kuwa ba zan fara zina ba, sakarya”

“Ka ɗau zaɓinka!” Ta ce tare da ƙwalla wata iriyar ƙara wadda ta yi amsa kuwwa, sannan ta fashe da wani irin gigitaccen kuka tana cewa “na shiga uku na lalace, wayyo ya kasheni, don Allah ku taimakeni, ya rabani da martabata, wayyyoooooo!”

Sultaan da ya fahimci sherin da take nufarsa da shi sai ya yi wata iriyar gigicewa tare da nufarta yana ƙoƙarin rufe bakinta, ɗage labulen kabar aka yi, daidai lokacin…

????FITATTU HUƊU????

????SULTAAN # Nml grp ~N~ 300 vip ~N~ 500 via 1401611541 Access bank, shaidar biyanki ta wannan numbern 08167888934
Mss Flower????

TSINTACCIYA
Nimcyluv

Baƙar fata
Autar manya

DATTIJON ARZIƘI
Real ladingo

Gaba ɗaya 800
Via 6850917335 Na’ima Shu’aibu Sulaiman Fidelity Bank, masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 za ku tuntuɓa. To show evidence of payment 08142105218

Mss Flower???? 08167888934 For more information????

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button