BAK’A CE Page 61 to 70

Wayarta dake jakar Agaishat ce ta shiga kuka a hankali da kidan celine dion i love u,
Cirota Agaishat ta yi ta mika mata , nan ta daga ta kara a kunnenta tana hangen motar dake kama da tasu mutanen ciki basu fito ba aman ta hangi angon nata ya fito ya karasa wajen motar,
Kallon Agaishat ta yi dake son a bude mata ta je wajen su sajida ta riko hannunta kafin take amsa shi da ohk in sha Allah,
Tana kashewa ta dubi Agaishat ta ce” Agaishana, dan Allah kar ki layu da kowani namiji kin ji? Ki zo mu shiga tare da ke mu saka Colonel tsakiya (wato mijinta)
Agaishat ta zaro ido da mamaki ta ce” wani irin ku saka shi tsakiya ba wani tsari sai kace mai.mata biyu? Allah ya sawaka yo dan me ba zan layu fa wani ba sai kace matar wani?
Alhinayett ta zaro ido ta hada hannayenta ta ce” ki rufa mini asiri dan Allah kar ki yi haka, walahi idan kika yi ina tsoron wajen nan ya hargitse ????????
Agaishat ta yi mata wani kallon mamaki, da tarin tambayar me take nufi? Sai fai kafin take aika mata da tambayar aka bude motar,
Colonel ne, cikin shigarsa ta kakin shima, ya hade ya gama haduwa, hannunsa ya mikowa Alhinayett nan ta saka nata ta sauko,
Idannuwan Agaishat ne suka sauka kansa, shine a cikin motar ashe, ta madubi take hangensu, shi da matarsa, ta sha doguwar riga baka mai shegen kyau, ko dan ta san ita din fara ce take son saka bakin kaya? Sai dan gyale baki da ta dan yane kanta ta yi irin daurin larabawa da shi ya zagaye kyakyawar fuskarta, sai tanfatsetsiyar jaka baka mai adon fari fari wace ke cike da yayan banki domin yau ranar ta kara kankarowa kanta mutunci ne .
Kanta ta kauda cikin jin zuciyarta wani iri, a hankali ta kara kai dubanta wajensa, kaki ne jikinsa irin na kowa, sai hular kansa da ta dan banbanta, sai bakin takalmi dake walwalwal ko daga nesa ka hanga ka san zai yi kudi,
Fuskarsa a hade take yana duban yanda ake laya mutanen dan shiga wajen diner da yake fatan a yi a gama lafia,
Bai ga adonta ba, bai san a ya ta zo wajennan ba, yana fatan bata yi dinki irin na yan matannan ba , domin doguwar riga ce du suka yi sai dai an yi mata fant har saman kaubri, so yake ta fito a motar aman har yanzu shiru …. shi ne damuwar Wardugu!
Kallonta ta kawar daga dubansa ta mayar kan Alhinayett dake tsaye tana jiranta,
Murmushi ta yi ta saki kafarta ta fito a motar ta tsaya gabansu,
Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, shi ne abinda Wardugu ya fada a file kafin ya kawar da kansa daga dubanta ya maida wajen gugun mazan wajen,
Ido hudu suka yi da Mu.azam dake tsaye tare da Khadija da kuma daya daga cikin Kanwar Alhinayet tanai masu magiyar su zo su bi layin masu shiga da amarya aman fir ya kiya kan shi da ba soja ba ya zai bi lafi ya bata masu tsari
Kawar da kansa wardugu ya yi ya maida inda suke tsaye, nan ya yi ido hudu da mijin Alhinayett dake masa magana da fuska aman bai gane me yake nufi ba,
A hankali ya maida dubansa wajenta, dinkin shadar doguwar rigar da akai mata da sket , an saba lesh da shada ne cikin juna, leshen kuwa mai manyan tiloli ne, sannan du inda aka saka shi mai yawa ake sakawa, ga tsagun da akai gefe da gefe har saman ciki duda sket din ya hau har saman cikin aman du yanda ta yi wani juyi sai rigar ta dage dan kuwa an rage mata nauyi sosai tana daguwa du yanda aka so ta dagun,
Rintse idannuwansa ya yi lokacin da ta juya tana dafe kanta da alama fafatawa suke kan maganar ba zata jera da wani gardi ba bisa umarninsa, juyawar da ta yi, kamar da gangan ta hargitsa bayin Allah dake biye da ita ba dare ba rana wa.inda Allah ya halitata da su dan ta ringa zaman kawai (????), sai da sukai sama sukai kasa hakan ya saka shi jin kansa ya sara sakamakon tunanin ko ba shi kadai ya ga hakan ba?
Juyowa ta yi tana duban mijin Alhinsyett ta ce” dan me ni kadai za.a hana cikin mu duka? Wani abin na yi? Ni a maida ni wajen Ayyana dan kuwa ba zan zo dan taron ba ace ni ba zan shiga ba
Ta karashe tana yin takwaf takwaf da fuskarta tamkar zata fashe masu da kuka,
Alhinayett ta matso ta kama hannunta zata yi magana kennan sai ga Farid, cikin shigar shada gizner ta sha aiki simple ruwan sararin samaniya ya dan dora wani mayafi fari kar a kansa abin rawaninsa ne sai ya yi yafe da shi, dogon buzu fari, bashi da jiki ko kadan ,
Ya jima a wajen tun kafin motar amarya ta karaso yana ts nemanta,
Gaban Alhinayet ne ya fadi ta yi saurin kara damkar hannun Agaishat tana dan waiwayen Wardugu ta ga kyam a tsaye yake su kawai yake kallo,
Da dan karfi ta janyo Agaishat da ta ga Farid ta sakar masa dan murmushi tana kokarin gaisawa da shi Alhinayet ta janyota,
Alhinayett ta hade fuska sosai ta ce” ki rufa mana asiri, ki rufawa kanki asiri Agaishat,
Kar ki tabo abinda ya fi karfinmu,
Kina wasa da lamarin da ba zaki iya tara ba,
Kar ki kula kowani namiji a wajen nan, idan ba haka ba ina mai tabatar maki zaki janyo rigimar da zamu kwana muna tserere a wajen nan a yau!
Ido ta zaro da yannayin tsoron yanda Alhinayett ke magana, ga mijinta shima sai waige waige yake yannayinsa na nuna bashi da nutsuwa,
Bata kara tsurewa ba sai da ya matso ya ce” Alhi, idan ta ki amincewa mu juya gida mu duka a fasa dinern,
Agaishat ta ce” wai me ke faruwa? Meye aka yi?
Mijin Alhinayett ya dubeta da kyau ya dan karancin yannayin firgicin da ta shiga , dan haka ya ce” wajen ne da hatsari, shi yasa ake kare lafiarki domin ba.a san me dauke da hatsarin ba,
Ai kuwa nan da nan ta shiga kifta ido ta rike hannun Alhinayett ta shiga waiwaye, ganninsa ta yi kyam a tsaye, ba zata iya fadin yannayinsa ba domin dare ne koda kuwa wajen ya kawatu da hasken fitila dare dare ne,
A yanzu muradinta ta kasance kusa da Ya Wardugu, snce waje da hatsari? Dubanta ta maida wajen shigar, an layu su kawai ake jira,
Sai ta maida wajen Farid ta ga yana tsaye da wayarsa a hannunsa, ita yake kallo, hakan ya saka da hannunta ta masa nuni da ya biyo bayansu,
Juyawa suka yi suka je gaban layin inda Wardugu ya cira kafarsa da Walyn da hannunta ke cikin nasa ta gama wayar da take amsawa suka bi bayansu,
Da farko tsakiya suka saka mijin Alhinayett, daga baya ta bar wajen ta koma bayan su Alhinayett ya kasance su Wardugu da Alhinayett sun sakata tsakiya,
Yau Wardugunma bata iya gaisarwa ba, dan a dan rikice take , fama take su yi su shige, aman ganninta kusa da shi sai ta ji ta samu nutsuwa, ko ba komai ta san idan wani abin ya nufota da yardar Allah zai tare mata, kai ba ita ba, du wanda ke wajen bashi da dar!
A hankali suke takawa, salon kidan ya canza, daga can gefe aka harba bindigar toka ta yi kara sannan aka saki kidan harbin bindiga wanda ya saka du jiki ya kwashi wani tsam,
Idannuwansa a kanta, du wani motsi nata , sannan hankalinsa du a tashe yake, sai dai a fuskarsa ba zaka taba fahimtar hakan ba domin ya hade fuskar tamau ba wani fara.a, hakama yaran nasa ba wani mai isashen sakewa dan kuwa kasancewa a wajen party ba zai hana ya ci ubanka ba idan ta kama!
Yanda tsarin yake sai amarya da angonta sun zauna kafin kowani namiji da ya jero da mace ya rakata har wajen zamanta gefen hagu sannan ya koma gefen dama domin rawar guitar, (sai wanda ya san yanda ake yi zai fahimata????????????????????),