BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 51 to 60

Bai iya magana ba sai nunata da yayi a tsayen da yake inda zufa ta shiga wanke masa fuska,Matarsa da ta shigo da tuwon tsakin da ta yi masa mai dan banzan dadi, wato mahaifiyar Anna ta ja ta tsaya da mamakin yannayinsa,

A hankali ta karaso dan gannin me ya firgita shi haka? Me yake kallo a waya?

Kurawa Anna ido ta yi, duda dan duhun wajen dan da haske aman ba irin tau din nan ba, sannan da yannayin girmanta da ya fara kama Anna, ba zai yiwu ta bace mata ba, tun usul mai kama da ita haka mutun daya ne, wanda suka nema suka rasa, kwararo kwararo har tsayin shekaru, wanda daga karshe ta yi hakuri kamar yanda mijinta ya roka, suka ajiye a jiyu, in da ranta Allah ya bayana masu ita , sannan sukai sadaka idan ta mutu ne Allah ya nuna masu gawarta ya sa ta huta,

A hankali ta karbi wayar inda jikinta ya kwashi rawa tana kallo ta kara kurawa wayar ido, a hankali ta ce” *ALLATCHI?* ALLATCHI ke ce? 

Anna ta fashe da kuka, bata san lokacin da ta karaso kusa da wayar ta karbe a hannun sarkin ba ta matso wayar sosai kusa da ita tana kallon iyayen nata, 

*Hatimi* wato mahaifiyar Anna ta yi taga taga zata kife inda mijinta *Gukunni* ya tareta jikinsa da wayar a hannunsa sunna duban Anna,

Shima muryarsa na rawan ya ce” Allatchi, dama kina raye? Ina kike yanzu mu zo Allatchi? Ki dawo gare mu, muna son ki Allatchi,

Anna ta lumshe idannuwanta ta bude ta ce” ina so na ganni wajenku yanzu , sai dai ba hali , 

Mahaifiyarta ta ce” mu gamunan zuwa! 

Kit suka datse kiran inda Anna ta kifa kanta cikin cinyoyinta tana kuka, iyayenta du tsufa ya fara zuwan masu danma ana cikin rayuwar dadi, duda auren wuri sukai tsakaninsu dan tun suna yan university suka yi aure, 

Girman soyayar da suke mata ta tuna, ta tuna irin yanda suka rayu babu ita tsayin shekarunnan danma an san musulmi da tawakali, Ba Ba hm! 

Hajia aminiyar Ayya ce ta shigo dalilin kiran da Sarki ya saka a yi mata domin itace uwar gidan sarki 

Tana zuwa Suka gaisa da Sarkin Timiya, 

Sarki ya nuna mata Anna a matsayin y’ar gidan amininsa da ta bata wato Gukunni

Ta sha mamakin wannan lamari, daga baya ta shiga murna,

Nan ta matso kusa da Anna ta duka inda Anna ta zauna kasa wajen cafet ta ce” ki yi hakuri da kukannan haka, muma mun san da batanki, dan a lokacin sarki bai hau sarauta ba, baima aureni ba (Sarkin Agadez dogon karatu yayi , dalilin da ya saka bai yi auren wuri ba, aka ajiye masa yar kanwarsa karama sosai domin dai sarauniyar Agadez itama ba zata wani fi su Annan ba)

Sarki dake dan nesa ya yi gyaran murya ya ce” ai mai yiwuwa sunma taso, duda na fada masa kar yayi tafiar gagawa aman fir ya kiya,

Anna ta kale shi da sauri ta ce” aa, kar su taso a mota bayan har dare yayi, dan Allah su bari mu mu tarar da su,

Sarki ya yi murmushi ya ce” mota fa, aa, ai yanada jirginsa da ya malaka wato ket privé, sannan yanada damar tashi a lokacin da ta kama dan sune hukumar.

Wani sanyi ta kara ji a ranta a yau yau kennan idan Allah ya yarje mata zata ga mahaifanta? Kai Allah da girma yake, Allah da jinkan bayi yake.

                     Paris

Wardugu na kowama Hotel ya fice a motar ba tare da ya cewa Agaishat ta fito ba, hasalima kule motar ya yi tana ciki ya shige hotel din

Yana zuwa dakin da ya dauka ya dauki jakarsa ya zuba abinda yake iya dauka ya goya ya dauki echarp na maza na wuya ya rike a hannunsa ya fito ya basu kys dinsu ya fice abinsa

Yana zuwa motar ya ga ta kara volume din kukanta aman yana zuwa ta yi dif tana kikifta ido,

Motar ya bude ya shiga ya ja,

Bai zame ko.ina ba sai butik,

Yana zuwa ya fada masu kaya yake so a zaba mata cikin gagawa da dan kwali,

Abinka da kasar ……, sai ya kasance suturun da ake nuno masa du daga dogon damamen wando, sai yan bintiyalan riguna, sai dogayen riguna aman masu mugun bin jiki,

Kansa ya dafe gannin lokaci na neman yi ba damar ya je wani butik din sai jirgi ya barsu, ransa ne ya kara baci wai su basu da Abaya ne? 

Basu da Abaya, sai da babarsu ta mike da kyar ta zakulo cikin kayansu masu tsadar gaske wa.inda sai wane da wane suke nunawa su ko a kasar, ta cirota wata riga blue mai hasken sama ta kawo masa tana tunanin bama zai iya ba dandai idan batai masa ba ya dauki wata ne dan tsadarta

Dagata ta yi inda suka bita da kallo, doguwar riga ce itama mai rike jiki bale daga sama, aman tanada dogon hannu daya kwal, sai dan siriri tamkar na shimi da akai masa wani irin kwana aka malaka shi jikin rigar daga sama, 

Sai dan kwali irin kananuwan nan sosai shima mai sharashara mai ruwan fari fari da blue blue din 

Kansa ya dafe yana duban kayan, ba kudin da aka fada masa bane damuwarsa dan kudin sun kai jika dari hudu, aa, yannayin rigar ne, aman gannin ya yi rantsuwa, sai kawai ya bata umarnin ta shiga wajen saka kayan ta saka su fice,

Da sauri mai butik din ta nuna mata ta bita ta tsaya daga kofa ta saka kayan sannan ta shiga ta gyara mata sosai, ta saka dan kum ta dan cacaje mata lalausan gashin kanta ta dora mata dan kwalin ya nadu ya yi kyau a fuskarta,

Wani irin kyau kayan sukai mata sannan suka fitar da kirar jikinta inda cikarta ta bayanna ,

Waouh macen ta fada kafin su fito tana nunawa Wardugu,

Mikewa ya yi bai kaleta ba dan shi ba dan hakan ya zo siyen kayan ba ya karbi jakar takalmin ya mikawa macen sannan ya juya bayan ya cewa Agaishat idan ta saka takalmin ta dauko wa.inda ta cire din maza su tafi

Da sauri ta saka takalmin, Allah ya taimaketa bai daukar mata mai tsini ba, plat ne mai igiya dan haka ta daura igiyar ta dauki wa.inda ta cire ta fito da sauri sauri ta nufi motar

Ja yayi suka tafi, tana ji tana ganni ya tsaya kofar gidan da bada jimawa ba yake gidan mijinta ya jefa kayan da ta cire ya dawo ya shiga motar yana tafe yana waya da yaronsa har suka karasa aeroport din

Nan suka iske shi har ya karaso dan haka wardugu ya bashi ky din motar sukai salama suma suka daga sai Niger Garin taraya Niamey garin zabarmawa, garin ka zo na zo

                      *Niamey*

Mota na tsayawa na fice da gudu daga motar inda sai a lokacin ya bita da kallo, yanda ta kwasa a gujen har dan kwalin kanta ya sulube daga saman kan nata ga yanda jikinta ya jijiga ya jijigo ne ya saka shi kawar da kai yana astagafari dan kuwa matar da batai idar sakin mijinta ba kalonta haka ai ba kyau????

Dan zama ya yi yana tunanin ya shiga ne ko kawai ya yi tafiarsa?

Wata zuciyar ta fada masa Wardugu Ayya fa mahaifiyarka ce, kuma indai kere na yawo, zabo na yawo watarana an hade, dan haka ka je! 

Ayya dake zaune tana kallon tv, a lokacin wajen karfe takwas da rabi na dare ne,

Sai jin kukan y’arta ta yi da ganinta ta fado da gudu ta fada jikinta ta kankameta tana rizgar kuka,

A rikice Ayya ta shiga kokarin tashi da ita tana fadin” Agaishat? Agaishat? Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, Agaishat ke ce? Lafia ? Ke da wa kuka zo? Me aka yi? Ina mijin naki? Ina wardugun? Ke?

A daidai lokacin Wardugu ya shigo yana tafia a hankali ya karasa saman kujerar zaman mutun guda ya zauna yana dubansu yanda ta makalkale Ayya da irin yanda Ayya ta rikice sai tambayoyi take tana duban wardugun,

Kamar daga sama ta tsinci maganarsa, koma tace kamar saukar mari, ya dan ja iska yana duban Ayya ya ce” *Ya saketa ne*,

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button