BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 31 to 40

*Walahi ni ba kowa bace, ni ba komai bace, Allah ne gatana????????????????????*Walyn ta zaro ido, rai bace ta ce” zan datse harshen ki idan kika kuma kiran mijina da gwarzon ki!

Aisata ta ce” da kuwa na ji dadin yin makota da ke, da zan gani idan kema da ya kilace zai saka ki a kaso dan kin zalinci wani! 

Walyn ta tsareta da ido, a hankali ta ce” zan biya ki, ki fada min kar lokacin da aka bamu ya kare ,

Aisata ta ce” na sani kina da damar iya biyana aiki, dan ni mai nema ce, ina nema kamar me, kudi baya isata, da yana isata da na tsaya da sirikin ki kawai! 

Walyn ta ja tsaki ta ce” lokaci!

Aisata ta ce” kar ki damu, yau ai akoy lokaci isashe ,

Walyn ta kuma tsareta da ido, ta ce” me zai rage ki dan kin fada mani? Kin san dai kin haramta wa wardugu tunda kika kwonta da ubansa! 

Aisata ta lumshe idannuwanta, a hankali ta lashe lebenta na kasa, rage murya ta yi kamar zataiwa Walyn rada ta ce” *Ke ba fa kowa ke da haram ba*,

Walyn ta daki table din ta ce” zaki fada mani ko ba zaki fada mani ba?

Har sai da hankali ya kawo kansu inda wani soja ya karaso yana tambayar lafia? 

Nan Aisata ta kalamance shi da”Oga ba komai,

Juyawa ya yi ya koma, Aisata ta dubeta da kyau ta ce” kina tunanin na taka farar kafata na je wajen Boka dan tsibu dan ya malaka min saurayi? Kina tunanin aikin boka ya malaka min mazaje biyu ?

Walyn ta ce” kin gane, ni fa ba yarinya karama bace, kuma na san bariki ki ka yi ! Dan haka kar ki bi min ta wannan hanyar ba gyara mu zata yi ba.

Aisata ta ja rigarta kadan, hakan ya baiwa saman mamarta damar fitowa sosai, ta ce” *kin ga malamaina*

Walyn dake kallonta ta yi dariya tana girgiza kai ta ce” ba dai Warsuguna ba, Wannan abin bai isa ya ja ra.ayin namiji mai sunna namiji ba! 

Aisata ta ce” haka ya fada maki? Ko irin zaman da kike yi da shi? 

Walyn ta ce” ba sai ya fada mani ba, haka ne, Wardugu kamili ne, girman kansa ba zai bar shi bama ya lura da wani abin jikin yar bariki! 

Aisata ta bushe da dariya har tana rike ciki, nunata ta yi da yatsa ta kuma kecewa da dariya, sai da ta yi mai isarta ta ce” lale kin rako mata, ina mai baki albishir din in dai kallon da kike masa kennan ki farka tun kafin ki kuma jaza mana wata yar balakin da ta fi mu ta karbe mana Gwarzon mu! 

Walyn bata ce mata komai ba, sai duban kin raina min wayo da take mata,

Aisata ta tsagaita tana duban Walyn ta ce” Walyn Wardugu, ba kowace mace ce ta san kofar boka ba, koda kina jidana da na yi bariki dan na fita da d’a na kuma dawo kan uba , ina mai tabatar maki ba boka ne ya tsaya min ba.

Ya zan zo cikin wannan wajen mai fitar da wari ki saka ni gaba kina yi min rainin wayo? Walyn ta fada,

Aisata ta juya idannuwanta ta ce” kar ki yi garaje, zuwa gidan yari rubutu ne wanda Allah ke kadara shi, diyawa a wajen nan basu taka basu karya ba….

Walyn bara ki ji wani abu….: du namiji na duniya yana da abinda idan ya ganshi a gabansa yakan ji ya rasa dabararsa, 

Wani namijin mace mai kissa, mai kisisina, mace mai kyan dan maciji ke tafia da imaninsa, wani namijin mace mai adini mai rufe jikinta, mai mutunta kanta ke tafia da imaninsa, wani namijin yana son mace mai halaya irin na yan bariki ce zabinsa, wanin mace mai kyau ko muguwa ce zasu taka rawar, wanin yana son mace mai shiru shiru, wanin yana son mace mai kamar maza irin mai kafkaf da ita, wani baya jure gannin mace a cikin yannayi na abin tausayi…zaki ga ya fada tarkon kaunarta, wani farar mace ce zabinsa, wani kuwa *bak’a*, ke wani duka biyun yana so….tambayar a nan shi ne *Sai ka karanci mutun kake gane waye shi harma ka tabo wajen da ba zai jure ba, da kansa zai nuna shi sai kai*, 

Walyn kallonta kawai take,

Aisata ta ci gaba” mijin ki dan ra.ayi ne, gwarzona ya bani wahalar da wani namijin bai bani ba , kyauna, zubina, yannayin rayuwana na saka shi fadin”Aisata ke matar kilacewa ce, ki yi zamanki a gida zan zo na dauke ki na mayar da ke matata. kafin na samu kansa na jigata.da kuka da komai ya furtan kalmar so, domin na kai karar tsohon saurayina wajensa inda na biya mutumin ya yi min dukan tsiya, ke dai na takaita maki sai da na zama tamkar kaska, du inda wardugu yake ina nan, da naci da taimakon aminiyarsa ya furtan kalmar so…

Sai dai abin haushi du irin yanda muke soyaya da shi idan na nuna koda shan minti ne a dan zaga sai ya fatatake ni, 

A ranar da na tube zindir a gabansa sosai na kusa cin masa wani tsinanan abokinsa ya shigo dakin domin ke shaidan ba abinda baya hasawa , kwana dakin wardugu na kusan cinma burina nan na fahinci irin zaman da ake tsakanin matar Marahut da shi,

Ayya ta kasance mace mai tsafta, ta iya girki, tana yiwa mijinta biyaya ….sai dai na sha na fito tsakiyar dare falon su na kunnuwana su tsinkayo min rigimar ba zata bashi ba, ta gaji da ayyuka ya bari sai da safe! 

Wani wal wal wal ta yi da idannuwanta ta ce” *Walyn ba.a matsa lamarin nan, idan aka tashi a yi kawai!*,

A lokacin da na gama gane Ayya ba zata aminta na auri farin cikina ba, na dauki damarar itama sai na cusa mata bakin ciki , kuma ko da kwaya sai na kwonta da d’anta! 

Walyn ta ce” shi Marahut din asiri ki kai masa ko?

Aisata ta ce” na fada maki ban san wannan ba!

Walyn ta rafka tagumi ta ce” fada mani yanda kika tarwatsa su , mai yiwuwa na yarda da labarin wai Wardugu ba asiri ki kai masa ba.

Aisata ta buda bakinta zata fada mata kennan aka zo aka ce ya isa haka sun jima suna hira domin dai Aisata harkar kwaya ya kaita kaso, ido a kanta yake dan kar a kawo mata har gidan kaso…

Haka Walyn na ji na gani ta fito ta kama hanyar gidanta ba tare da ta samu komai ba! 

Alhinayet ce zaune tare da saurayinta, malamin university ne, saurayi ne domin bai taba aure ba, bazabarme ne baki dogo , hira suke cikin nishadi nan yake shaida mata yana son turowa,

Alhinayet ta fada masa zata fadawa abanta tukunnan , abinda ya ce in sha Allah.

Haka suka gama hirar su ya mike ya yi mata salama ya shige motarsa ya tafi,

Mikewa ta yi ta je cikin gidansu , 

Shiryawa ta yi ta saka dogon hijab dinta blue, ta dauki bakar leda ta je wajen mamansu , wato matar mahaifin su ta shaida mata zata je ta kaiwa Agaishat hijaban

Adu.a ta yi mata kafin take fita ta shiga motarta ta tayar ta nufi gidan Ayya………….

Aghali ya zo garin Niamey ne dan duba gininsu da ake yi a unguwar cité laraba, 

Ya gama abinda ya kawo shi aman ya ki tafia bisa bukatarsa na Wardugu ya siyar masa da mota , sun tsayar zai shigo ranar lahadi wato gobe baya aiki sai su fita su je ya gani……

Soyaya suke a nitse, a hankali yake koya mata mecece soyayar ma wace a kulun sai sun gama bitar zai jefo mata tambayar” Agaishana, shin kina jin du abubuwan da na zana maki a kaina?

Dariya take yi a fili sai tace” ni yaya Mu.azam gudun fankan dakin Hane mai aiki kawai ke saka zuciyata gudu, ka ci gaba da koya mani na san zata yi gudun wata rana idan na ganka

Yakan tsareta da ido ne kawai , bai san me zai da ita ba, soyaya ai shigar farat daya take yi, shi da yake so ya kai kudirinsa wajen Ayya kan a aura masa ita da wuri? Kai ba zai wani jira har ta kamu da sonsa ba, zata so shi a zaman da zasu yi, shi kam yana kwadayin zama da ita a rayuwa….

Docter Mariam ce tsaye tare da shugabansu ta asibiti, kanta duke kuka ne take har jikinta na bari ta ce” nima marainiya ce docter, a lokacin da na zo wajen nan shi ya tarbe ni, ya ciyar da ni da aljihunsa, kafin na tsaya da kafafuwana shi ne komaina, tun a lokacin nake mugun son sa, ba zan yafewa kaina idan ban je na dawo da shi ba, ki taimaka mani ki sama mani takardar nan na roke ki,

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button