BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 61 to 70

Haka walyn ta yi gum da bakinta, domin ita dai bata iya rarashin miji wai dan ta yi masa laifi komai girmansa kuwa,

Wannan laifinma da ta tafka masa, ta bi ta hanyar da baya iya ja an maidota, da baya kulata ta kuma bi ta hanyar da koke koke an yi masa tsawa, hakan ya sa ya dawo kulatan aman da nashi takun, domin idan zai yi aurataya da ita sau dubu sai ya saka roba , yana gamawa yake tashi ya bar mata dakin koda nasa ne, baya irin na da ya rungumeta a jikinsa,

Karara nisa ya shiga tsakanin su, wanda du macen arziki ta lira da irin nisan nan tsakaninta da mijinta toh fa hankalinta zai tashi ta shiga neman hanyar sulhu da gyaran abinda ya hadasa haka, aman ina, ta ci gaba ne da bibiyar dukan motsinsa, tana kaiwa du wata mu.amalarsa da mace izgili, ta ci gaba da yawon bukukuwanta, ta ci gaba da kawance da kawayen banzan da basu zauna suka baiwa cikinsu bama bale su yi tunanin gyaran aure wai har a je ga biyayar miji,

Ita dai ta fito a ganta, mawaki ya waketa, ta koma gida gida ta tarar da miji ya leleta, (Anya kuwa? Abin da kamar wuya gurguwa da auren nesa),

Haka ya gama ya sauka ya fito daga dakin da tawul a kugunsa ya nufi bayin falonsa, 

Juyawa ta yi saman bed din abinta tana mai jin wani iri a jikinta dan zafi, ta jima sosai kafin take mikewa ta fito dan tafia dakinta, nan ta gansa zaune saman cafet ya lumshe idannuwansa,

Tsai ta yi ta tsura masa ido, 

Tunda suka yi aure ya kasance cikin tsaf tsaf, ko dan sun raba bangare suna haduwa lokaci zuwa lokaci ne? Ba zata ce ga ranar da ta ganshi da kazanta ko ta tarar sumar kai ce ko saje bale jiki,

Yana da kula da adininsa, baya wasa da sallah da ibadun da yake a bayanne da wa.inda yake yi a boye,

Yana da fitina, rigima, tashin hankali aman fa idan an shiga hanyarsa, tabas bashi da saurin hadiye wulakanci ko.na waye, aman yana da kawar da kai, abinsa ba zai hada ka da shi ba, uwa uba mijinta tsarare ne, Allah ya yi halita mai nitsa zuciya , ko a cikin kawaye idan aka tashi maganar dogon yaro ga fari ga farin jini ga yayan banki sai an fara ajiye masa gaisuwarsa kafin a hangi wani dan tafe yake da zamaninsa, sai dai kash zuciyar nan tasa na tayar mata da hankalinta, zata so ya zama yanda take son ya zama, da ta yi ihun ta more miji,

Kafa ta saka ta fice a falon , bata wani damu da irin zamansa, da dalilin zaman ba, ita dai abinda ta saka a ranta zatana zuwa ta kawo masa kanta, ya samu nitsuwar da ba zai dubi wata y’a da wannan muradin ba, sauran zata ji da su , dan ita dai ba aikin fari take ba na baki ba, tana kwashe salarry kafin a yiwa ma.aikatan gwanati biya, tana shiga babar mota tana zuba zinaria ta saka shada, damuwarta Wardugunta, zako ta ci uwar uban du wata mai rawar kan da zata rabar mata miji!

Basa zama a kwanakin nan,

Shirye shirye suke tun karfinsu,

Ba wai wani yawon kaiwa yan mata cati ko wani gayace gayace ba, aa siyaya ne suke a hankali na abubuwan da zata bukata a gidan miji inda matar mahaifin Alhinayett ke saka su a hanya da zuciya daya tana mai basu kyawawan shawarwari,

Ayya kam ta hakura da jajen ita gaskiya a bar fitar mata da y’a gannin fitar da y’ar nata na kawo ci gaba ta hanyar kara iya mu.amala da mutane kala daban daban da take gani a wajen siyaya ne, a saloon, da wajen gyaran jikin da Alhinayett ta biya suke zuwa tare a yi masu dan kuwa itama tsale ta yi ta dire kan tana so ,

Sukan tsalake kwana biyu basu fita ba, idan aka ce zasu fita kuwa Ayya kanta har mamakin itin tsararen shirin da y’ar tata ta koya,

Ta iya saka kaya masu saka jiki a nutsuwa, ta fi nacewa atampopi dinkunnan dogayen rigunnan zamani masu tsari irin na yayan yan gayu ba masu fitar da tsiraici ba,

Wani sa.in takan zurmuka hijab dinta a saman shigarta mai kyau da birgewa, wani sa.in kuwa sai ta yafa dan gyalenta ,

Idan ka ganta ba zaka taba kawowa ta taba aure ba, hakan ya saka du fitarsu sai ta samu mai tayawa dan ba karya dorinar kyau ne da ita ga dorinar ado, kaya saka su kawai take su yi mata das ba ciko ba acuci ko daya.

Alhinayett na lure da irin kokarin da mahaifinta ke yi, dan haka ta kwatanta zuwar masa da shawarar tana da yan kudadenta a banki, idan ya amince ra kawo ya kara ya yi mata gadon, sai dai ya yi murmushi ya ce” Alhinayett, ke dai Allah ya yi maki albarka irin dawainiyar da kike da mu baki daya, aman ba zan amshi kwandalarki ba, zan yi kamar yanda na yiwa kannun ki, ki je kudaden ki ki kara abubuwan nan naku na zamani na gayu ,

Haka ta mike ta yi godiya ta fito, itafa tausaya masa take domin nauyi ne ba kadan ba a kansa, gashi da y’aya mata masu cikuluftun yau a sayi kaza gobe a sayi kaza, gashi dangi na kauye du a kansa suke, ta so ya karba ko ba komai zai rage wasu abubuwan aman ya kiya gashi aure har sauran sati biyu,

Zuwa ta yi dakinta ta tsala wanka ta saka abayarta baka sannan ta daura nikaf a fuskarta ta fito ta yiwa yan gidan salama kan zata je wajen gyaran jiki da karbo dinki da kai wasu dinkunnan, wai a nan du irin tarin suturun da take saya ne , lefe an ce sai gobe za.a kawo,

Tuki take hankalinta kwonce a yar karamar motarta ta nufi gidan su Wardugu dan dauko kawalin nata wace take kanwa a wajenta kuma kawar shawara dan a duniya nitsuwa da hakuri Agaishat ya saka ta aminta da ita,

Tana tsayawa ta bude ta fito sai jin karan shigowar messages ta yi a wayarta rututu,

Dakatawa ta yi ta bude pos dinta ta ciro wayar inda ta maida hankalinta wajen tagar Agaishat tana hangen ko zata ganta ta nuna mata ta zo fa,

Tana buda wayar ta shiga, wata sabuwar number ce ta Niger, dan haka ta shiga cikin messages din,

Hotunnan ne , hotunnan gadaje, kujeru, table din tv, na tsakar daki, na cin abinci, show glass, kowane da katon tambarin katon butik din da ake siyar da su, irin kayan wajen nan ne,

Murmushi ta yi tana fita a wajen ta ayanna a ranta yo wannan ko gidanmu za.a siyar ba zai kai kudaden wadinnan kayan ba, ni me ya kai ni? 

Murnushi ta yi ta shiga gidan,

Ai kuwa ta shirya cikin wata doguwar rigar atampa A yi mata dinkin mai dogon hannu aman a bude sosai dan kuwa du hannun ya cinye sauran atampar,

Ta yi daurin dan kwalinta da irin carto din nan baki, ta dan fitar da yalwatacen gashin kanta daga kasan dan kwalin,

Kunnenta dauke da yan kunayen azurfa mararsa nauyi da fadi sai dai tsayi,

Hannunta dauke da dan zobe karami na azurfar shima,

Fuskarta ba wata kwaliya sai dan kwalin da ta saka sai lebenta na kasa da ta shafawa dan jan baki kalar ja aman ta murje shi ya kasance kadan ne ya fito a jikinta,

Kamshi take bazawa ta dora kafarta ta dama saman ta hagu tana dan kadawa ta cuno baki wai Ayya ce ke fadan bata son saka takalma masu dan tsayi ita kulun sai plat kamar wata tsohuwa wanda ko ita Ayyan na saka mai tsayinta idan ta yi ra.ayi, dan haka ta karbe katon hijab din da ta dauko da takalmin ta koma ta dauko mata wani mayafi fari kal mai shara shara da takalma masu dan tudu farare da pos fara kar mai igiya yar doguwa ta dawo tana fadan sai kace wata datijuwa ta wani kinsima hijab kulun kulun? Ke da nake so kema na wanke ki abina na maki aure mai sunnan aure? 

Alhinayett ta yi dariya tana kallon yanda ta daura takalman a kafarta tana cuno baki ta dauki pos din ta saka wayarta a ciki kafin take juyawa wajen Ayya ta sakar mata murmushi ta ce” Ayyana, ni ba zan yi auren ba, na hakura da auren, kin ga ba kin mini auren ba aman na dawo maki? Kawai mu yi zamanmu ,

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button