BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 41 to 50

Allah ya sauke su lafia, du kuwa da irin yanda Agaishat ta jigata domin har amai ta yi a lokacin fa jirgi zai tashi da irin yar jijigar nan da yake kafin ya mike da tafia, sannan a lokacin saukarsa wannan kasan da abubuwan ciki ke yi suka saka shima ta yi tamakar ta sume,Mu.azam na kule da ita , tausayinta yake ji, khadija ce ke kiran yan matan nan na jirgi da ta ga zata shiga wani yannayi , su ke zuwa su bata kulawa har jirgin ya sauka,

Agaishat dai na mamakin irin halin shariyar da Mu.azam ke nuna mata idan suna tare da Khadija, tun bata gane komai ba har ta gane sai dai bata nuna ko a fuska ba,

Ko wajen sauka shi ne gabansu su kuwa suna biye da shi a baya inda Agaishat ta zama ta karshe

Kanta ne ta ji yana juya mata lokacin da ta ganta cikin tankamemen aeroport din *Paris*

A hankali ta sada kanta dan ta lura du idan ta daga kan ta ga irin tsaruwar garin ne hankalinta ke tashi,

Fitowa suka yi inda manyan motocin taxi ke laye, da yawa an yi kiransu je, daidaiku ne suka zo wajen dan radin kansu

Wajen motar suka nufa , nan Mu.azam ya juyo gannin Khadija bata biyo su ba,

Budewa Agaishat ya yi ta shiga ta zauna inda Direban ya saka akwatinta bayan motar,

Wajen Khadija ya nufa yana son sai ya karanci fuskarya aman ta ki bashi dama,

Yana zuwa hannayenta ya kama yana dubanta ya ce” ba zaki biyo mu ba? 

Murmushi ta sakar masa ta girgiza kai ta ce” ku je da matarka, nima zan dauki wata taxi din, zan leko ka, ka kular min da kanka nan da kwana hudu zaka dawo asibiti ka kwana biyu bisa kulawar docters kafin a shiga aiki da kai,

Murmushi ya sakar mata ya lakace hancinta ya saki hannayenta ya juya ya nufi motar inda sai a lokacin Agaishat ta kawar da fuskarta gefen madubin motar

Satar kallonta ya yi, sai a lokacin ya ji wani nauyinta, rabonsa da ya yi wani maganar nutsuwa da ita tun da Khadija ta sauka a gidan Ayya, 

Kwarai Ayya ta yi masa mutunci ta nuna komai ba komai ba ta hanyar kawar da kanta ta kuma karbi bakuwarsa duda tsanar akidar kawance tsakanin mace da namiji da ta yi kuwa, sannan koda suka tashi tafia ta yi masa gargadi nasiha kamar yanda iyayensa zasu yi masa, sai dai kuma ta nanata ya rike amanar baiwar Allah,

Gabansa ne ya ji ya fadi, amanar Agaishat ya karbo fa, amana ya karba, anya kuwa haka amana ta ce?

A hankali ya mika hannunsa na hagu ya dora saman cinyarta , wanda ke nuni da yana son kara kusancinsa da ita,

Agaishat ta juyo ta dora tsararun irannuwanta saman hannunsa, daga nan bata kai dubanta sama ba ko dan kar idannuwansu su shaku da juna, sai ta kawar da kanta ta mayar bakin titi tana kallon hanya da mamakin irin tsarin garin da irin shigar mutanen garin

Bai dauke hannunsa ba, bai kuma yi mata magana ba har suka karaso kofar wani gida 

Daga kofa raga ne na karfe baki, haka ya ja jakar tana biye da shi tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki har ya saka cod din kofar gidan nasa suka shiga,

Fulawowi ne a gidan, ba wani tankamemen gida bane , dan madaidaici ne tsarare, 

Matatakalar suka hau suka shiga ainahin falon gidan,

Plat ne, ba bene, dakuna kwaya biyu ne sai katon bayi da kicin mai girma da tsari da wajen buga game, kujeru farare kar ne a falon sai dan table fari, tv tankamemiya jikin bango sai wajen da ake kuna wuta dan dakin ya dau zafi , sai ac biyu a iya falon

Kofar ya mayar ya rufe ya saki akwatin nata nan,

A hankali ya juyo yana takowa inda take tsaye kanta na kallon kasa,

Yana isowa ya kama hannayenta yana yi kata kallon kurullah, 

Jin ya jima bai yi magana ba ta dago a hankali ta sauke tsumamun idannuwanta cikin nasa,

Fuskarsa ya shagwabe ya jata zuwa saman kujera mai zaman mutun biyu ya zaunar da ita,

Kusa da ita sosai ya zauna yana so sai ta kara yi masa kallon da ta yi masa aman du yanda ya so ta kiya,

Muryarsa ya kimtsa ya ce” kin daina so na????, me ya sa kika daina so na?

A hankali ta juyo da dubanta wajensa, kurawa fuskarsa ido ta yi, a ranta ta ayyana, ai bamu kai ga gane menene so din ba aka daura auren mu, a fili kuwa sai ta kifta idannuwanta da suka fara cika da kwallah,

Murmushi ya yi ya ce” ki yi hakuri Agaishana, kar ki yi fushi da ni, na san kina da tarin tambayoyi aman ki yi hakuri ki bar su a wajenki har sai lokacin yin su ya yi , ki sani ina son ki ba zan daina son ki ba, ina gannin girmanki ina daraja ki a rayuwana, ban aure ki dan cutarwa ba,

Wani sanyi ta fara ji a ranta , nan da nan ta ji ta fara manta shaku da rudannin da ta shiga dalilin nesanta kansa da ya yi da ita kwanakin nan, (kar ku ga laifinta, baki daya a duhu take), 

Dan murmushi ta sakar masa aman batai magana ba, 

Mikar da ita ya yi ya ja hannunta suka nufi daki…………????

                       *Timiya*

Wasa wasa sai da Anna ta wuni ta kai tsakiyar dare wajen karfe biyun dare ta wani irin kwala karan da ya firgita yayanta dake zagaye da ita ta aniya amsa kira tamkar ana kiranta , fadi take” *Na.am, Na.am, Na.am?*, 

Kuftaya ta shiga yi da dukan mai kokarin riketa, idannuwanta rufe suke ruf tana ihun amsa kiran da basu san mai kiranta ba,

Digarin da Sarki ya bari ya kula da lafiar Gaishata dake ta faman nakuda tare da Jakadiya har zuwa lokacin bata haihu ba gashi da ta dora masa kuka sai da aka sakata cikin kurakura aka kawota gidan Annar, haka suka wuni har gashi rabin kwana zar suna fama ne ya shigo da sauri jin hayaniya,

Fitikar kwan da ya kunna ce ya kara masu haske a dakin da ta wajensu , subahanallah shine abinda yake ambata gannin irin yanda suka kasa tareta ga kuma Gaishata sai murkashi take tana kuka gashi kusa da ita suke jakadiya sai tarewa take kar a fado mata,

Gannin ana iya fado mata a samu matsala ya saka shi saurin shiga dakin ya je suka hadu su uku suka kai Anna kasa inda Jakadiya ta shiga fadin ya taho ya taho,

Da sauri Dogari ya mike ya kama Anna da ta fara dan yi lakwas ya cicibeta su kai waje domin ya gane Gimbiyar sarkinsa zata haihu ne,

Nishin Gaishata da nishin Anna du tare ne, cikin ikon Allah Gashata ta haihu lafia ta sako yaronta har Jakadiya ta yanke cibi ta dauke uwar da ta fado ta nade a zanin Gaishata bayan ta dora mata yaron saman cikinta ta aniya kimtsata tana ta murna,

A galabaice Gaishata dake lumshe ido tana budewa na ni.imar nakuda ???? ta kallo jakadiya, murya a disashe ta ce” Annata?

Jakadiya ta ce” Allah ya ja da zamaninki kar ki damu in sha Allah da sauki, ai dogarin nan dan gidan cheik Ne, baban almajiri ne gayacan sunai mata adu.a,

Sosai suka dukufa suna yiwa Anna du adu.o.in da suka iya inda shi kuwa dogari ya dauro Alwallah ya zo shima da ruwa a kwanon kwano ya zauna ya shiga karanto mata manyan adu.o.in karya sihiri, na rukuya kai harma da na tsari duka yana tofeta da shi kuma yana tofawa a cikin ruwan,

Mikawa Mariama ya yi ta shafa mata gaba daya jikinta suka ci gaba da adu.o.in ,

Wasa wasa sai da garin Allah ya waye domin kuwa sai da aka kirayi salar asuba Anna ta ja wata irin ajiyar zuciya ta yi wata irin mika kafin take zabura ta ce” *Ayya, Ayyana, wani abu zai rufe min ido, wani abu Ayya* (kar ku manta tubawa ke kiran Mama da Ayya, wace Ayya xce haka? Shin Anna ta dawo hayacinta?))))

        Kadan ne

*☀IDAN RANA TA FITO WRITER’S ASSO????*

 ____________________________________________

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button