NOVELSUncategorized

TARAYYA 25-26

Page 25
Haske writers association +
 Zama tayi tareda rafka tagumi cikin zullumi da rashin sanin madafar tunaninta
Abu ‘daya tasani shine tana

tsananin qaunar rumanah kamar itace ta haife musamman a yanxu datake hango soyayyarta mai tsanani a idanuwan Maheer ‘dinta saidai duk wannan qaunar da yardar zata rushe tazama qiyayya da tsana mai tsanani idan sirrin rasuwarsu asma’u da bulama ya bayyana ga rumanah abinda bazatasoba kenan. 3

Qarfe goma da mintuna goma sha biyu suka farka yatashi zaune tareda tayarda ita zaune yana gyara mata gashinta daya barbaje.
Kallonsa tayi tareda sakin kasalallen murmushi
Ya shafi gefen fuskarta tareda bude baki yace,
Yaya?
Lumshe ido tayi cikin laushin murya tace,
Yayi sauki yanxu banajin ciwon kan.
Lumshe ido yayi tareda jinjina kai kafin yakalli agogo yace,
Ya salam” yana sauka daga kan gadon.
Tare suka shiga toilet din dakinta sukayi wanka Wanda yadaukesu dogon lokaci sbd tsayawa shiririta.
Koda suka fito kan cinyarsa ya zaunar da ita tana goge masa ruwan jikinsa yana kallon gashinta dake ‘digo masa ruwa sbd wasan dasukai acikin bathtub yasa dole suyi wankan tsarki.
Riqo hannunta dake goge gashinsa yayi tareda Shafo gashinta har zuwa fuskarta ya zarce cikin towel dinta ya shafo cikinta dake lafe yana kallonta cikin wani irin yanayi da galabaita da zuciyarsa ke ciki.
Daqyar ya bude baki cikin wani irin taushin murya yace,
I have something precious inside you so daga yanxu bazaki sake ganin albinon malaminkiba sbd gudun daukar jajayen ido da qaton baki. 4
Murmushi zancensa yasa tasaki tareda zare hannunta taci gaba da goge masa gashi batareda tace komaiba.
Sake riqe hannunta yayi yana tsareta da ido yace,
I will miss this smile dakikeyi danki hanawa suhailat mijinta. 2
Kallonsa tayi gabanta na faduwa sbd jin sunan suhailat yasatajin faduwar gaban ta sunkuyar dakai tareda tashi daga jikinsa ta dauko hand dryer ta jona tafara busar masa da gashinsa mai tsananin laushi.
Shidakansa ya shiryata cikin pink gathered neck top da black straight skirt ta Sanya black hula ta fito ta nufi dakin sa ta dauko masa kayan dazai saka takawo masa yasaka suka fito palon hannunta na cikin nasa tanata 6anbare hannunta amma takasa ahaka yajata har gaban ammy dake sintiri a tsakiyar bedroom dinta tana ganinsu tasaki murmushin qarfin hali tana qarajin tausayinsu dan ko ayanxu datake ganin yanayinsu bama zasu iya rabuwa da junaba saidai duk soyayyarsu qila basuda rabon hada zuria sbd bazata so rumanah ta zamto itace zata fara haifarwa  maheer namijiba gwara dai wata kokuma suhailat duk da itama bazataso wani Abu yasametaba saidai so sone amma sonkai yafi. 2
Cikin kulawa tace,
Rumanah yajikinki?kan yadaina ciwo ko?
Kai ta daga tana sake janye hannunta amma Sam kamar bashine riqeda hannunba.
Abinci sukaci a dining ammy madai hartafi rumanar jin kunyar abinda maheer din kemata kuma ko ajikinsa tamkar bashine yakeyiba. 1
Daqyar sukaga sungama ammy tarigasu barin gurin tana girgiza kai sbd batasan haka ‘danta yake ‘dan duniyaba. 1
Ammy na barin gurin takallesa kamar zatayi kuka yazuba mata ido tareda sakin wani miskilin murmushi kafin ya miqe tsaye ya ranqwafa yayi kissing kanta yace,
Ki kula.
Ya fice yana duba agogon hannunsa sbd lokacin tafiyarsa yayi sosai.
Bayansa tabi da kallo hawayen datake riqewa suka gangaro tasa hannu ahankali tashare tareda miqewa ta nufi dakinta ta zauna bakin gado sai kawai siririn kuka ya kufce mata. 1
Yini tayi adaki kwance bayan sallah babu abinda ke tayarda ita ko abinci yau ammy daki tasa aka kai mata sbd ta fahimci halinda take ciki na tafiyar maheer ‘din.
Da daddare ma kasa bacci tayi harsai kusan asuba ya saceta koda ammy ta leqo taga bacci takeyi bata tadataba sbd tasan balallaine tasamuyin bacci da daddare ba.
Koda gari ya waye sosai guraren qarfe goma ammy tadawo ta tararda ita cikin wani zazzafan zazzabi nan hankalinta yafara tashi musamman yanda jikinta yayi wani mugun zafi banda amai babu abinda takeyi
Ganin abin na girmama yasata sanarda s salma nan aka kirawo Dr faduwa tazo tadubata tareda fara mata pregnancy test dan karta maganin da baikamacetaba awon farko ciki ya tabbata nan ammy taqara shiga damuwa ga farin ciki ga fargabar abinda zai iya zuwa yadawo. 3
Magani tarubuta tareda Wanda zaita tasamu dan bacci kota huta daga aman.
Kallonta ammy tayi bayan fitar Dr faduwa tasauke ajiyar zuciya tareda mata sannu cikin tsananin kulawa da qaunarta.
Abinci ammyn tasamu taci daqyar kafin tayi sallah tayi wanka ta kwanta wani sabon baccin yayi gaba da ita.
Tunda yatafi bata sake lafiya ba sosai ciwo ya kwantarda ita komai taci baya zama cikinta
Duk inda hankalin ammy yake ya ninka tashi drip kuwa tasha ledoji qarshemadai daina samata ruwan akayi.
Batasan ‘daga masa hankali kokuma shiga haqqin suhailat shiyasa bata fada masa saidai duk yanda taso tare alamarin fin qarfinta yayi dan yanxu wata biyu da tafiyarsa ga mamakinta cikin harya fara tasawa gashi har lokacin ko zaman arkiqi bata iyayi koyaushe akwance take. 1
Gyara zama tayi ta fuskanci Dr faduwa cikin nutsuwa da damuwa tace,
Yanxu wata hudu kenan cikin yake?
Abinda scanning dina yabani kenan”” dr faduwa tafada tana sake kallon takardar scanning din. 1
Cikin tsananin damuwa sultana takalli Dr fadwa tace,
Inason axubarda cikin tunda yaqi bata lafiya wuyardatake sha tayi mata yawa banason wani Abu yasameta tunda mijinta baisan dashiba. 5
Kallonta Dr tayi cikin nazarin zancenta sbd tanaga idan anyi hakuri duk wannan wuyar zata wuce duk da itama tana tsananin tausayin rumanah din.
Cikin nutsuwa tace,
Inaga tunda haryakai wata hudu aqara hakuri idan yakai wata bakwai duk wannan wahalar zata rage sosai.
Girgiza kai ammy tayi cikin damuwa tace,
Acire kawai shine abinda nakeso yanxu. 2
Kallonta Dr tayi cikin nazari kafin ta bude jaka ta fiddo takarda ta rubuta allura tace aje yanxu akawo zatayiwa rumanah din sai zuwa dare idan ciwon mara yataso idan tafara zuba sai akai mata ita asibiti.
Cikin qanqanin lokaci ammy tasa akaje aka kawo allurar nan suka nufi dakin rumanah dake kwance tana baccin datasamu yadan dauketa.
Yawu masu ‘dacin damuwa da wasi wasi ammy ta hadiye cikeda tsananin tausayin rumanah dakuma takaici da baqin cikin abinda zatayi 1
Bude ido rumanah tayi cikin wani irin laushin ciwo suna hada ido da ammy
Ammyn tayi saurin sunkuyar dakanta sbd tasan haqqoqan rumanah bazasu barsuba komai daren dadewa saidai idan har zubar mata da ciki shine abinda zai kare mata ita daga masifar mineelik to ashirye take data ringa zubar mata da ciki idan tasamu. 3
Cikin tausayawa Dr ta kalli rumanah tace,
Sannu rumanah,
Allura za’ai miki kisamu ‘dan qarfin jiki.
Murmushi qarfin hali tasaki daqyar tareda ‘dan muskutawa tabada bayanta cikin nutsuwa tasoka mata allurar tayi mata tana mata sannu. 2
Saurin barin dakin ammy tayi sbd hawayen dake qoqarin ciko idanuwanta
Cikin tsananin sanyin murya takalli Dr faduwa data fito dakin tace, 3
Awa nawa allurar zatayi kafin cikin ya lalace yafara zuba sbd……..
Wani wawan jiri taji yayi mata muguwar diba tana kallon qofar palon saida Dr ta riqota tareda juyawa itama sukai ido biyu dashi tsaye yana kallonsu babu mai iya gane yanayinsa acikinsu shiya mugun tayarda hankalinsu.
Manage wlh ciwon kai ke damuna yau.
#mamuhgee
Page 26
Haske writers association???? +
Dan Allah daga yanxu yanzu idan kasan labari baya maka dadi zaifi idan zaka daina bi sbd wata maganar batada dadi kuma kowane marubuci idan harya fara rubuta labari to shi yasan saqon dayake son isarwa kuma idan har  mai karantawa yayi hakuri ahankali zai riqa fahimatar abinda akeson isarwa dan haka pls mu riqa sanin maganar dazata fito bakinmu,
Nidai nasan abinda nake rubutawa idan kasan baka iya magana mai dadiba to zaka iya tsayawa daga nan sbd bazanso kaci gaba dabiba dan abinda zaizo agaba. 14
Not edited.
Ammy ya qureda idanuwansa dasuka mugun qara sanyata damuwar abinda tayi muryarta na rawa takira sunansa daqyar.
Ya lumshe idanuwansa yasake kallonta Dr faduwa na ganin haka ta sulale ta fice dan ita ko kallo bata ishesaba.
Gaban ammy yaqaraso ya tsaya cikin wani irin yanayi na tsananin 6acin rai da bata ta6a ganinsa acikiba yace,
Bantaba samun tarba irin wannan ba ko sakin fuska babu bare murmushinki da murnarki.
Da mamaki ta kallesa da sauri zuciyarta na qara tsinkewa dan kuwa abinda take hangowa acikin idanuwansa ta tabbarda yajisu.
Murya cikin sanyi da tsananin damuwa tace,
Maheer nasan kaji komai amma dan Allah inaso ka fahimci manufata tayin hakan dan nikaina ba’ason raina nayi hakan ba wlh zanfi kowa farin cikin ganin rumanah ta haifa maka ‘yaya saidai I can’t risk her life…….
Oh please ammy karki fara kawo maganar risking life anan sbd babu Wanda ya isa yahanawa bawa shiga qaddararda Allah ya dora masa,
Ammy  kinsan meyasa kuke wahala da masifar mineelik haryansu shine sbd kuna sake qarfafawa abin ne,
Meye alaqar ‘yayana da wannan tunanin naki dazaki min haka?
Meyasa zaki rabani da abinda ko hannuna bai shigaba?
Shin ammy ina iliminki da saninki yayi dazakiyi tunanin namiji zata haifa bayan bakida masaniyar hakan…… 4
Cikin ‘daga murya da takaicin abunda ke faruwa ayanxun tace,
Kana tunanin ina nuna kamar nasan zata haifi namijine shiyasa nayi hakan?
Amatsayina na uwa nayi hakan sbd sanin matsayin dazata hau idan ta haifi namiji Wanda kasan mezata zama idan harta zauna wannan matsayin musamman da jinininta bai zamto na sarautaba saitafi wainda suka gabata zama baraza da abin fargaba……
STORY CONTINUES BELOW
Cikin tsananin baqin ciki ya katseta da cewa,
Rumanah har abada bazata ta6a hawa wannan kujerarba koda ta haifi namiji koda hakan na nufin ni nakar6i mulkin zan karba ni nazama masifar…… 2
A tsawace tace,
Ka riga karasa wannan damar ta zauna throne ‘din mineelik tun lokacinda kace baka karbi magajin mineelik ba dan haka ko kanaso kabaka ayanxu atarihince ‘dankane yanxu yakeda cikakken ikon karbar mulkin mineelik kuma kafin ya girma mahaifiyarsace kawai takeda ikon bawa duk Wanda taga damar riqon qwaryar mulkin ‘danta idan kuma taso ta itace dakanta zata…….
Idan angansu kenan a mineelik ‘din…yafada zuciyarsa na qarasa daukar zafi.
Itama cikin zafi tace,
Wannan ne baka isaba sbd labarin cikin na isa a kunnen sultan bazata qara ko kwana biyu ba’a mineelik ba dan haka zabi ya rage naka kodai acire wannan cikin kodai rumanah ta rasa rayuwarta amatsayin rumanarta……
Ayau da wanine agabana bake mahaifiyata ba da bazai sake ko minti ‘daya da kansa a gangar jikinsaba,
Zuciyarsa tariga tagama ‘daukar wuta bazai iya cigaba da maganaba ya wuceta ya nufi dakin rumanah dake kwance lamo tanaji mararta na murda mata ahankali saidai ko wani qwaqwaran motsi bata iyayi saidai jikinta dayayi mummunan sanyi hakanan takejin maraicinta na taso mata. 2
Qamshinsa taji yashiga hancinta ahankali ta bude idanuwanta dasukai laushi takalli qofa tagansa tsaye cikin yanayin dabata ta6a ganinsa ba ta lumshe ido sbd tasan idanuwanta ne kawai ke ganinsa sbd zuciyarta tasamu sukuni.
Qarasowa yayi baice komaiba ya dauketa cak ya nufi qofa da ita ya fito ammy dake zaune palon ta rafka wani mugun tagumi cikin tsananin damuwa da zullumi
ta miqe tana kallonsa yazo yatsaya gabanta cikin danne halinda yake ciki yace,
Komawa zanyi idan ta sauka zankawo miki ita. 1
Kafin tayi wata magana ya wuce yabarta da baki bude idanuwanta dasukai jajir suka ciko da qwallan damuwa ganin tun yanxu alamura na neman ca6ewa. 1
Wani babban private hospital ya nufa da ita tun ahanya yasa akai musu booking flight koda suka isa harta fara fita hayyacinta sbd jinin daya 6alle mata sosai.
Cikin gaggawa aka fara dubata dan tsaida jinin dayake suma doctors din asibitin qwararrine yashiga cikinsu dan baibari kowa yataba masa itaba,
Cikin ikon Allah suka samu nasarar tsaida jinin batareda cikin ya zubeba saidai kwata kwata baza’aso taringa babban motsiba sbd anriga antaba lafiyar cikin dole saiya kwana biyu yasake qarfi.
Adakin datake kwance yashiga toilet ya wanke jikinsa tareda canxa shirt sbd sosai jini ya 6atasa.
Sunsamu ticket din da asuba jirgin zai tashi shiyasa yasake mata wasu injections sbd motsin daza’ai da ita
Yana zaune sofa din dake dakin akai kiran asuba ya tashi yayo alwala yayi sallah yana idarwa babu bata lokaci akai rubuce rubucen daza’ai suka nufi airport cikin ambulance ko mintuna ashirin basuyi da isaba jirginsu ya ‘daga.
Da rana tsaka suka isa Georgia direct motar asibitinsa tazo ta daukesu suka nufi asibitin nan aka fara bata sabon treatment likitocin basu zaunaba saida suka sake tabbatarda komai is back to normal.
Baibar asibitin ba saidata farka ta bude idanuwanta dasukai nauyi takallesa tareda lumshe ido sbd ba qwari ajikinta sosai.
Matsowa gabanta yayi yatsaya tareda kallon cikin idonta ya riqo hannunta tareda sakar mata siririn murmushi ahankali ya furta,
Hey yene konjo(my pretty) 1
Kallonsa tayi fuskarta na bayyanarda farin cikin ganinsa dakuma sunan daya kirata dashi.
Da kansa ya dagata yadauketa yakaita toilet yayi mata wanka yacanza mata kaya patients sabbi ya rasa yanda zaiyi ya daure mata gashinta dole yahaqura yabarshi asake yabata tea tasha yabata magani da sauran injection dinta kafin yayi kissing goshinta yafice.
Koda ya isa gida qarfe tara na dare lokacinda suhailat tagansa bude baki tayi tana kallonsa cikeda mamakin ganin jiya yatafi amma yadawo yau bayan batasaka ran dawowarsa da wuriba.
Rungumesa tayi cikin danne mamakinda tace,
Hey welcome.
Rungumeta yayi tareda sakin ajiyar zuciya da 6oyayyan numfashi sbd shikadai yasan halinda zuciyarsa ke ciki ayanxu sbd tabbas yasan akwai rigima agaba saidai bazai ta6a bari rumanah ta Shiga abinda kakannin kakanninsa suka aikatoba koda hakan na nufin shi yafadawa abinda yayi gudu tun qurciyarsa matuqar hakan shine zai kare rumanah da abinda zata Haifa so be it. 1
Bedroom dinsa suka nufa ya tube yashiga wanka itakuma ta nufi kicin tacewa Carolina ayi abincinda akasan maheer din naci.
Daga haka takoma dakinsu amah tasanardasu dadynsu sundawo suka fito da tsallen murnarsu.
Sakin fuska da jiki yayi sosai dan gudun shiga haqqin suhailat ‘din da yaransa saidai cikin zuciyarsa damuwace mai tarin yawa duk da kasancewar cikin ya tsaya damuwa batabar zuciyarsaba musamman dayasan dole zasu koma mineelik sbd ammynsa takoma ‘dakinta badan hakaba bayajin rumanah zata koma mineelik.
Sosai suhailat ta lurada akwai abinda yake ransa na damuwa duk da abune mai wuya ka iya gane yanayinsa.
Batason tana shiga abinda bai shafetaba musamman yanxu dayakeda wata matar kuma ‘yar ‘dakin ammynsa dan haka shishigi kan abinda babu ruwanta ba nata bane sbd kartajiyo abinda zai sakata damuwa. 1
Fruits kawai yaci koda suka zauna dining kuma harsuka gama bai yiwa kowa maganaba duk da ko yaransa sunsaba da miskilancin daddyn nasu sbd kosu wani lokacin idan abin ya motsa baya iya yimusu doguwar magana saidai idanuwansa dake ladaftar da mutum.
Da daddare koda yakira wayar Dr olie yasanar masada tasamu bacci tundazu.
Kallonsa suhailat dake kwance jikinsa tayi still taqi tambayarsa meke faruwa bayan taji da hospital yake magana batai la’akari da ko ammynsa ceba dayake yasaba da haka take shiyasa bai tsaya tunanin banxa akan hakanba da haka tai bacci cikin jikinsa ya qurawa kyakkyawar fuskarta ido hakanan yakejin tausayinta sbd ba ita yakeji cikin tsakiyar zuciyarsaba,
Bayajin fitar kowane numfashinsa da ita aciki saidai tanada wani irin girma da qima a idanuwansa ta yanda bazai iya barin ta quntatu akan abinda yake tsananin so ba.
Rufe idanuwansa tareda dakin 6oyayyar ajiyar zuciya.
Qarfe bakwai yafito wanka yakalli suhailat data shigo dakin batareda yakalletaba yana gyara gashinsa yace,
Carolina ta hada breakfast na mutum ‘daya a basket and it should be something light.
Kallonsa tayi tana zaunawa gefen gadonsa tace,
Ok amma pls who is the patient?
Batareda yabar abinda yakeyiba yace,
‘Yar ammy.
Da mamaki ta kallesa tace,
Bansan waye haka ba.
Then kibarshi idan anyi discharging nata zaki ganta.
Miqewa tayi tazo gabansa ta tsaya tana kallonsa yana saka rigarsa tace,
Ok zanbika muje tare nadubata ko waye tunda hanyar zuwa office dina ne.
Baice komaiba yagama shirinsa suka sauko tana maqale da hannunsa.
Da gudu su amah dake qoqarin zama a dining sukayo gurinsa yasaki fuska cikin kulawa yayi pecking kowannensu yana cewa,
Good morning to sweets angels.
Good morning to you too daddy””suka fada suna kissing kumatunsa both sides.
Dining suka nufa dukkaninsu sukai breakfast
Shidai daqyar ya iyacin toasted bread one slice da black tea yamiqe
Suma dai dayake sun gama suka dauki school bags dinsu suka fito dukkaninsu Carolina tabiyosu da basket ‘dinda aka shirya breakfast dinda yace.
Motarsu amah daban driver yafara wucewa kafin yashiga Lamborghini dinsa suhailat tashiga yaja suka fice daga gidan.
Koda suka isa asibiti suna shiga reception yatsaya batareda yajuyo gefentaba yace,
Kije room 36 zanzo idan naga dr  Andrew.
Ok tace tareda kissing hannunsa ta wuce da basket din ahannnunta.
Shikuma kai tsaye office dinsa ya nufa.
Tana isa qofar dakin ta tsaya tareda Sauke ajiyar zuciya dukda batasa waye acikiba ta murda qofar tashiga.
Zaune take tsakiyar gadon nurse na gyara mata kanta daya barbaje yana damunta.
Tsayawa tayi tsakiyar dakin qafafunta na rawa gabanta yayi mummunan faduwa ganin rumanah ce,
Ahankali tasauke idonta kan qaramin cikinta daya fito ga wani haske mai firgitarwa dataga tayi.
Fita numfashinta yafarayi dasauri wani irin zufa ya karyo mata amma saitayi saurin kiran sunayen Allah acikin zuciyarta kafin tasauke numfashi mai sanyi tasaki murmushin qarfin hali tareda qarasowa bakin gadon inda rumanah ta tsareta da ido itama numfashinta na fita da sauri amma ganin tasaki fuska yasata qaqalo murmushi tana cewa,
Sannu da zuwa.
#mamuhgee.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button