Bakar Inuwa

BAKAR INUWA 1

    Matashiyar budurwa da zata iya kaiwa shekaru goma sha shida zuwa sha bakwai a duniya ta fito da ga ɗakin da Asabe ta fito ɗazun. Sanye take da dogon jijjab har ƙasa alamar salla tayi. Tana tsananin kamanni da Asabe tamkar tayi kaki ta ajiye. Cikin ladabi da nutsuwa takai duƙe tana faɗin “Abbanmu barka da dawowa? Ansha ruwa lafiya?”.

        “A gidan ubanwa nasha ruwan? ke kuma zaki sake ɓatan rai!”.
      Ƙasa tai da kanta ƙwalla na ciko mata ido, dan tanada zuciya matuƙa, sai dai tana da ƙoƙarin dannewa musamman akan mahaifanta guda biyu da halinsu baida maraba da girman haihuwar ƙasan gada.
      “Kayi haƙuri Abbanmu, dama zance maka nice na amso lemon a wajen jabiru”.
      “Buhun bu*a’uban nan kayyasa (😨🙆🏻‍♀️🙊😆). E lallai na zama ɗan iska haihuwar ƙasan gada kuwa da gaske. To ubanwaye ya aike ki!!?”.
        Yanda yay maganar a tsawace ya sata runtse idanunta da ƙarfi tana haɗe kukan dake neman taso mata. “Kayi haƙuri Abbanmu, babu wanda ya aike ni. Babu abinda zamuyi buɗa baki ne da shi shiyyasa na amso mana, nace masa kaine ka aikoni dan inba hakaba bazai bani ba”.
        Sake maƙurewa yay jikin bango tamkar tsohon ƙadangaren da ciwon sanyi ya buge yake shaƙo ƙamshin mutuwa.
“Ni DAUDA naga haihuwar jaraba jinin ladin ƙasan gada. Niko wai yaushe lalacewata takai har hakane a gidan nan ne wai? K dan uban uwarki har ni zaki laƙawa sheri ina fama da ƙishirwar azumi na? To wlhy ki rubuta ki ajiye sai kinyi nadamar hakan daga ke har uwar taki, dan nasan itace ta aike kin ta noƙe……”
       “Kai Dauda sauraramin. To kodai dama dani ɗin kake bada itan ba da ka haifa? To wlhy ahir ɗinka wahainiyarka ta kiyayi ramata, inba hakaba kaima kasan na fika tsiya da tujara. Ka buga ƙafa kamar na karen mafarauta ka barmu cikin yunwa ga ruwa za’a sha saboda kafi kowa iya babbaku da tujara dan kawai an anso abin nera dubu guda injika shine zakazo tsakar gida gaban magauta da ƴan bani na iya kana zazzage min. To wlhy ina dai-dai da kai”.
      “Tsssss!!!!”
Kakeji wani irin gigitaccen mari mai ƙara da alamar zaiyi ɗan karen zafi ya sauka bisa kumatun budurwar nan dake tsugunne ranta a matuƙar jagule, ta amshi laifin ne dama dan gudun karsu raba halin da suka saba a gaban kishiyoyin mahaifiyar tasu. Amma sai gashi dabarar tata batai ba.
Ta dafe kuncin jikinta na rawa. “Wannan marin na hanani zaman buɗa baki wajen Jabirunne da kikayi ke kuma. Saura na ƙaryar da kikaimun itama. Ke kuma Asabe yanzu banda lokacin mai lokacinki, amma ina nan tafe kanki..” ya ƙare maganar yana nuna Asaben.
      Caraf Asabe tasha gabansa tana mazurai. “Wlhy ka sake taɓamin yarinya sai na rama mata. Kai barfa ganin uwa ban son ta, son kayana nake ras, idan kuma kaji ƙarya sake taɓata dai-dai nake da kai, danni a yanzu nake da naka lokacin. Banda kai dai kana cikin mazan da sai an tsoma kansu a wuta an ɗauraye musu zunibi ka fita baka ko bamu geron kunu ba dan mun samawa kammu mafita kazo har kana tara jijiyar wuya. To bara kaji ni ba matanka bane daka maida sakarkaru, idan kaji ƙarya kuma sake gwada bugunta ka gani, kaima kasan wacece Asabe autar hajiyar birni shalelen bahago dan mai…….”
     Sai kuma taƙi ƙarasawa ta balla masa harara, ganin ya juya fuuuu zai sake ficewa. Taja tsaki da faɗin, “Da ka tsaya mana kaji ko zaka iya latsawa ka kwana lafiya ɗan gidan abun kwari mai yawo da tsinuwar uwa bisa kai”.
        Wani irin kuka budurwar nan da har yau ke duƙe ta fashe da shi. Cikin masifa Asabe ta juyo kanta takai mata shiru dan tasan minene dalilin kuka. “Dan ubanki tashi anan kona huce kaf haushinsa a kanki mara mutunci. Ko dan dai nice jinin asara sai na zauna yana cin zarafina gaban kishiyoyi na masa shiru saboda ga jikar ta-salla wadda ta haɗiyi ƙur’ani dan haƙuri. K nifa bar ganina haka zan iya kakkaɓar daku nai gaba dama tausayinku ne yasa nake zaune a wannan gidan da tsiya taima katutu abincima sai anyi kwarakarsa a maƙwafta dan lalacewa”…………✍️
      

Tofa jama’a bana ina mukazo haka? Ina alƙalamin namu ya kwasomu ya kawo😹😹?.

A cikakken Littafin BAƘAR INUWA kawai zamu samu wannan amsoshin. Naira ɗari uku me kacal, tare da duk zafafa biyar naira dubu ɗaya ne kacal. Karku bari ayi babu ku. Dan bakuga komai ba. Yanzu aka fara sharar filin wasan. Cakwakiyar sai wasan ya kankama😉. Dan duk wanda akayi babu shi ALLAH yayi missing🥺.

Taku
Bilyn Abdull ce🤙🏻*

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button