Bakar Inuwa

BAKAR INUWA 11

     Police station ɗin da aka kai Ammar suka nufa. Tun shigowar su Yaya Abubakar wasu a cikin ƴan sanda suka shaidashi saboda aiki ya taɓa haɗashi da wasu a cikinsu. Amma duk da haka sai ya nuna musu i’d card ɗinsa. A zabure sauran ma suka shiga gaishesa. Aka kuma masa iso ofishin ogan wajan.
       Tun a shigowarsu ya shaida Yaya Abubakar ɗin. Amma sai ya maze abinsa. Yaya Abubakar ya cije lip ɗinsa dan akwai ƴar tsama a tsakani. Sai dai yana sama da shi. Cikin nuna bai damu da basarwar tasa ba yay masa bayanin kansa. Tare da buƙatar a bashi Ammar.
       Cikin yatsine fuska ɗan sandan yace, “To yallaɓai idan ku matsayinku na manya kuna haka su kuma wanda basu da dangi ƴan sanda kuma fa? Laifi ƙaninka yay aka kawosa nan, sai kuyi haƙuri mu gama tattara bayanai akansa mukai maganar kotu kamar zaifi”.
      Sosai Yaya Abubakar ya kafesa da ido. Sai kuma ya saki wani lalataccen murmushi yana miƙewa dan yasan wannan tsarin da ga Abba yake. “Wanann basirar ba taka bace. Amma ga saƙo ka bama wanda ya tsara maka ya kuma biyaka. Ya kiyayi ranar maida murtani dan zata kasance mai ɗaci da tsauri. Ya kuma bar raina allura dan itama ƙarfe ce. Duk randa zuri’ar Aliyu Hamza gwarzo sukaji a ransu zasu maida murtani TAKUN SAAƘAR bazai masa ƙyau ba. Wannan hanunka mai sanda ne”. Yaya Abubakar ya ƙare maganar cike da gargaɗi.
     Murmushi Yaya Usman yayi. Dan bai taɓa zato da tunanin yaya Abubakar ɗin nasu ya iya zaro zance haka na. Koda suka fito da kansa yasa a kaisa cell ɗin da Ammar yake. Shine ya amshi key tun daga kanta ya buɗesa da kansa.
       Wani irin kallo ya tsaya yanama Ammar da yaci uban duka. Da alama ma ba’a jima da dukan nasa ba, dan duk sabbin raunuka ne a jikinsa dake fidda jini. Komai baiceba a lokacin sai kama hannun Ammar ɗin daya taso da sauri yana tambayarsa “Ina Ummi take?” yayi. Bai amsa masa tambayarsa ba sai da suka iso kantar. Ya duba ƴan sandan wajen da sukai tsuru-tsuru cikin kaushin murya yace, “Su waye sukai wannan aikin?”.
    Kallon kallo aka shigayi. A matuƙar tsawace yace, “Ba magana nake ba ne?!!”.
           Zabura duk sukayi har tsirarun mutane da sukazo belin ƴan uwansu da masu kawo abinci. Cikin rawar murya wani ɗan sanda yace, “Yallabai wlhy ba laifinmu bane sakamu akayi”. Ya ƙare maganar a hankali cike da raɗa saboda fitowar ogansu da ga office dan jin tsawar da Yaya Abubakar yayi.
       Takarda Yaya Abubakar ya fisga ya jefama ɗan sandan da yay maganar. “Ina son duka sunayen members na ƴan sandan dake a station ɗin nan. Wanda sukai wannan dukan kuma sunayensu su kasance a ware”.
     Wani busashshen yawu ya haɗiye da ƙyar yana ɗaukar takardar. Jikinsa sai tsuma yake ya shiga zano sunayensu ɗaya bayan ɗaya. Bayan ya kammala cikin girmamawa ya mikama Yaya Abubakar ɗin. Uffan baice masaba ya amsa tare da jan hannun Ammar da Yaya Usman ya riƙe ta ɗayan gefen suka fice da ga station ɗin.
        Ko a mota ma babu wanda yay magana dan zuciyar Yaya Abubakar takai ƙololuwar ɓaci game da lamarin Abba. Asibitin suka wuce da Ammar shima. Ba ƙaramin tashi hankalin su Yaya Muhammad yay ba ganin dukan da akaima Ammar. Hibbah kuwa kuka ta fashe musu da shi tare da zuwa ta rungume Ammar ɗin.
       “Wash ALLAH auta zafi”.
Ya faɗa cike da shagwaɓa saboda jin ta ƙankame masa hannunsa da yake da tabbacin ƴan sandan sun ji masa ciwo. Saurin sakin hanun nasa tai tana sake fashewa da kuka. Ya kai hannu bisa kanta ya dafa yana murmushin ƙarfin hali. “K karki maidani kamar ba namijiba mana. Bakisan dukan ƙarfi ya ƙara min ba ma”.
         A yanda yay maganar ya saka su Yaya Umar yin murmushi suna girgiza kansu. Hibbah kuwa kukan ne ya sake kufce mata.
       Yaya Umar ne ya kaisa akai treatment ɗinsa da bashi magunguna. Sauran abincin da Hibbah taki ci suka matsa masa yaci da ƙyar shima. Dan sai da Hibbah ta dinga basa a baki yau babu faɗa. Bayan ya kammala yasha magungunan da aka bashi. Duk yanda sukaso yaje gida ya huta yaƙi, yace shima sai yaga fitowar Ummi.
          Sha’awa yanda suke ƙaunar junansu ya bama doctor Bilal. dan haka ya bama Ammar ɗin shawarar yazo office ɗinsa ya kwanta to har komai ya kammala sai a tashe sa. Nanma da ƙyar ya amince bisa umarnin yaya Muhammad. Haka dai ya miƙe yana tura baki Hibbah na masa gwalo.

_★★★_

   
          Duk yanda yaso yin shirin barci ya kwanta hakan ya gagara. Sai fama kai kawo yake a cikin ɗakin, abubuwa da yawa zuciyarsa ke raya masa game da matakin da ya kamata ya ɗauka a kanta. Inhar zata iya kai masa hari ta samesa a ƙanƙanin lokaci. To wane irin shiri kenan zatai a gaba dominsa? Lallai dole ne yasan ita ɗin wacece? Mi kuma ta taka ne haka?. Shin sakata akai? Kokuwa yin kanta ne?.
      Waɗanan jerin tambayoyi suketa faman masa kai kawo a zuciya da hanashi nutsuwa. Shiri ya canja saɓanin pyjamas da ya kamata ya saka sai yasa wasu kayan daban. 
        Yaransa na falon zaune har yanzu suna sha’aninsu sai ganinsa sukai ya fito. Mamakine ya kamasu dan duk zatonsu ya kwanta.
       “Boss da matsala ne?”.
Salisu ya faɗa cike da girmamawa.
     Kansa ya girgiza masa yana ƙoƙarin ɗaura agogonsa. Sai da yaje gab da fita a falon yace, “Zanje wani waje ne, wani yazo ya rufe gidan”.
         Saurin miƙewa Khalid yayi duk da tambayoyine fal bakunansu amma babu damar yi, dan ya nuna baya buƙatarsu. Su ko saboda trianing da suka samu da ga garesa da kowanne irin yare yay magana ko yay nuni suna fahimtar kayansu.
      Koda ya wuce Khalid ya dawo zaman tattaunawa sukai, amma sai basu gano komaiba, dan haka sukai jigum-jigum……


     Alhmdllhi ƙarfe goma aka fiddo Ummi da ga ɗakin theatre cike da nasara. Bayyana muku irin farin cikin da su Yaya Muhammad suke ciki ɓata lokaci ne. Basu sami damar ganinta ba dan an miƙata ɗakin hutu ne. Sai dai bayanin da Dr Sageer yay musu na narar aikin ya saka zukatansu nutsuwa. Har suka amince da shawararsa ta tafiya gida dan ba’a bukatar kowa tare da Ummin sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu.
          Basuyi wani zaman ɓata lokaci ba suka tattara suka wuce bayan an tado Ammar da zazzaɓi mai zafi yayma ligif saboda dukan da yaci. Sosai tausayinsa ya bayyana bisa fiskokinsu. Sai dai komai basuce ba bayan Hibbah da ke ta jera masa sannu kamar zatai kuka. Kaɗan-kaɗan ta ɗaura hannunta a goshinsa.
       Suna gab da zuwa gida ya bige hannunta data ɗora masa a karo na babu adadi. “K dalla kin isheni, ga hannunki da sanyi”.
     Baki Hibbah ta tura gaba. Cike da tsiwa ta murguɗa masa baki da faɗin, “Oh dama ka samu na damu da kai zaka min wani iyayi”.
        “To waya aikeki? Uwar iya mai cinikin iya”. Ya faɗa yana gyara kwanciyarsa jikin kujera.
      Murmushi Yaya Usman da ke kusa da su yayi yana girgiza kansa kawai. Dan inda sabo sun saba gani. Anjima kaɗan kuma kaga sun koma hirar arziƙi. Kafin awa ɗaya ta rufa sunyi faɗa sau biyu.
        Cikin jin haushi Hibbah tace, “Idanma kaga na sake kulaka dan ALLAH ka tsine min Yaya Ammar”.
          Baki Ammar ya taɓe da faɗin “ALLAH na gode maka na jefar da ƙwallon mangwaro na huta da ƙuda”.
       “Yaya Usman ka ganshi ko?”. Ta faɗa kamar zatai kuka.
        “Ya isa manta da lamarinsa auta. Ko sannu karki sake masa har ya warke”.
         “Ai baran masa ba ko Yayanmu”. Tai maganar da dungurin wajen ciwon da ke a hannunsa. Ƙaramar ƙara ya saki yana bige mata hannu dan yaji zafi. Ta ƙyalƙyale da dariyar mugunta. Ranƙwashi mai shegen zafi ya bata wanda ya saka bakinta rufewa ruf, sai kuma ta fashe da kuka.
        Yaya Abubakar da duk yake jinsu da ga gaba ko kallo basu ishesa ba. Sai ma waya da ya ɗauka yay kiran maigadi ya buɗe musu gate. Koda suka shiga cikin gidan tsitt yake alamar jama’ar cikinsa harsun ƙwanta. Kusa da inda Yaya Muhammad yay parking shima yayi gab da sashensu.
    Hibbah da ke kukan ranƙwashin da Ammar yay mata ta fara fita domin kaima Yaya Muhammad ƙara tunda Yaya Abubakar bai bada fuska ba.
      “K zoki wuce ciki ki kwanta”. Yaya Abubakar ya dakatar da ita dan bayasan wani dogon magana a yanzu. Yasan kuma indai Hibbah ce bataƙi su kwana ana shashanci ba. Baki ta tura gaba sim-sim ta nufi sashensu.
     Yaya Muhammad yay ɗan murmushi yana kallon Yaya Abubakar ɗin. “Siddiq yau fa gaba ɗaya ka zama masifaffe. Kasa duk auta ta firgita da kai”.
        “Tana da cika ciki ne wani lokacin”. Yaya Abubakar ya bashi amsa yana kashe motar. Yaya Ammar yace, “Dama hakan kowa ke mata da mun huta da shegen ƙiriniyarta tamkar ƴar mage”.
      Kusan duk sai da sukai ƙaramar dariya. Da ga haka suka shige makwancinsu kowa ya nufi ɗakin barcinsa.
        Hibbah ma da ta shiga tanata zunɓure-zunɓure shirin barcin tai tana kunkunin wai dan anga Ummi bata nan kowa ya tsaneta. Gobe a asibiti zata kwana bazata biyosu su cinye ta ba.
         Da ƙunkunin dai harta kammala shirin barcin ta kwanta bayan tayi addu’a. Sai kuma a lokacin tunanin duk abinda ya faru a wannan yini ya shiga dawo mata. ALLAH dai ya taimaketa barci barawo yaci galaba akanta batare data shirya hakan ba.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button