Bakar Inuwa

BAKAR INUWA 12

         Koda suka kammala shirin cikin ɗanyun shaddoji iri ɗaya kalar sararin samaniya suka fito, kasa haɗa ido da shi sukayi. Sai satar kallonsa sukeyi ta ƙasan ido, yayinda dariya ke cin ransu a ƙasan zuciya dan shi tashi shigar ta irin marasa jin direbobin nan ce yayi. Da alama da kansa zai tukasu a mota kenan tsabar iya taku. Gaba yay batare da yayi magana ba duk suka rufa masa baya suna ƙoƙarin gimtse dariyarsu.
         Motar bus da zata iya kwashesu ce a waje a fake master nata faman gogewa kai kace driver ɗinne na gaskiya irin wanda suke zuba iya shege a tafa zuwa agege da maraban jos. Dan facemark ɗin dake fuskarsa bata da maraba da ta direbobin da ke tsaka da cin duniya da allura.
          Da kansa ya buɗe musu motar yana harararsu dan ganin kallon da suke masa a munafunce suna murmushi. Sai da suka gama shiga ya rufe yana zagayawa mazaunin driver bayan ya dagama matasan dake zaune a wajen mai shayi anata fira akan abinda ya faru jiya na mayar gwamna hannu. Sai zabga gaddama suke kowa na kare abin son sa. Wasu Master, wasu jami’an tsaro, wasu matar gwamna ɗin. Yayinda wasu ke faman zuba ashariya kai kace faɗa ne ya tashi.
       Murmushi ya saki yana shigewa a motar saboda jin furicin wani da ke faɗin, “Suma jami’an tsaron lusarai ne da zasu zauna mutum ɗaya ya gagaresu. Kawai dai sunyi niyyar barin shegenne kafin suyi ma rayuwarsa walmakalifatu”
     “To ka sani ko aljanine?”.
Wani ya bashi amsa dai-dai master na reverse da motar. Hannu suka ɗago musu wasu na faɗin ALLAH ya sanya alkairi. Dan sun yarda su ɗaurin auren za’aje😂😝.

            Lallai maganar yaran master gaskiya ne. Wannan gida yaji kayan ƙawa da more rayuwa. Shi kansa yana matuƙar son gidan. Dan a cikinsa ne kawai yafi sakewa sosai. Sanann anan ne kawai yake zama da yaransa. Amma duk sauran gidajen ba kullum yake kwana tare da su ba sai yaso.

BAYAN KWANAKI UKU

           Alhamdulillahi jikin Ummi yayi ƙyau sosai, dan tattali iya tattali take samu da ga iyalanta sanyin idaniyarta. Yayinda wasu a cikin ƴan uwa ke tururwar zuwa dubata da jiki.
      Hibba ce take kwana tare da ita, su kuma su yaya Muhammad da sun taso aiki anan suke tarewa har sai 11 suke wucewa gida. Har zuwa yanzun Abba bai dawo ba da ga tafiyar da yay randa akaima Ummi ai. Itama hajiya mama taɗan lafa da fitinarta saboda ƙafarta data motsa, duk da dai su su yaya Abubakar ɗin sunsan wani abun suke ƙullawa basu nuna sun damu ba.
Junaid ma ya dawo gida bayan kwana biyu da yayi a asibiti. Sai dai kuma tunda ya dawo ɗin ko ƙeyarsa basu gani ba, sai sauran ƴammatan gidan marasa kunya. Su kuma ko kallo basu ishesu ba. Dan a cikinsu wai sonsu su Yaya Abubakar ɗin sukeyi.
         Tuni shaƙuwa ta shiga tsakanin Ummi da mutum nan da ya biya kuɗin aikinta kaso ɗaya bisa uku. Dan kamar yanda yaranta ke jurar zuwa kullum safiya dubata haka shima yake zuwa dubata duk safiya. Da rana kuma ya aiko da abinci a kawo mata. Da dare idan ya tashi kasuwa ya shigo da fruits ya sake gaisheta sannan ya wuce. Haka zataita saka masa albarka da masa fatan alkairi akan kasuwancinsa da ya sanar mata yanayi, tare da ma mahaifiyarsa da yace ta rasu addu’a, da mahaifinsa da ke raye.
        Addu’ar da take masa ke sakashi jin daɗi. Da kuma yanda su Yaya Umar suka sake da shi sosai tamkar shima ɗan uwansu ne. Hibbah ce dai da ga gaisuwa bata sake kulashi dan dama ita haka take tana da wahalar sabo duk da rawar kanta. Idan kaga ta sake to tare take da Umminta ko yayunta. Su kaɗaine takema yanda taso.
 
            Yau ma suna tsaka da tattare kaya dan an sallamesu Ummi zataje ta cigaba da shan magani a gida yay sallama. Sai da Ummi ta amsa da bashi izinin shigowa sanann ya shigo. Hibbah da ke haɗa kayan ko ɗagowa batai ba balle ta nuna tasan da zamansa. Shima kallo ɗaya yay mata ya dauke kansa. Dan har cikin ransa kallon miskila yake mata tunda ba yarda take tai magana a gabansa ba. Ko surutu take da ya shigo take gimtse bakinta.
     Cike da girmamawa ya gaida Ummi da tambayar ta yaya jikinta?. Fuskarta faɗaɗe da murmushi tace, “Alhmdllh yaro na. Ykk ya Abban naka shima?”.
       “Lafiya lau ya ke Ummi, yana ma gaisheki da baki haƙurin rashin zuwansa saboda shima yana ɗan fama da ƙafa ne”.
        “ALLAH sarki babu damuwa ai. ALLAH shima ya bashi lafiya yasa kaffara ne. Yaya iyali ko babu kaima kamar ƴan uwan naka?”.
        Murmushi yayi yana duƙar da kansa ƙasa da kai hannu ya shafi wuyansa zuwa ƙeya. “Ku mana addu’a dai Ummi, ALLAH ya bamu nagari”.
        “To amin. Amma ni bansan mi kukema hange-hangen ba sam. Mutum bazai yi aure da ƙuruciyarsa ba kamar yanda iyayenmu sukai mana sai ya gama tsofewa. Ni ban sani ba ko tsoron matan kuke ji ne wai?”.
         Murmushin sa ne ya sake faɗaɗa sosai yana faɗin, “Ummi tsoro kuma? Kawai dai matan ne sai a hankali, sai ka dage wajen zaƙulo mai tarbiyya gudun dana sani”.
         “Da kuma wanan dan wanan. ALLAH ya baku na gari to”.
     “Amin Ummi mun gode”.
Yay maganar yana duban Hibbah. Da sauri tace, “Ina yini”. Yanda tai ɗin ma harya so bashi dariya. Fuskarsa ɗauke da murmushi yace, “Autar mu ykk ya ƙoƙarin kula mana da Ummi?”.
       A ranta tace, (Kaji ɗan iya). A fili kam sai tace, “Alhmdllhi Yaya Isma’il. Ya Abba?”.
        “Abba yana lafiya, yana ma gaishe ki”.
     Murmushi kawai tai batare da ta sake cewa komai ba. Shima sai ya mike kawai yana faɗin, “Ummi bara naje waje idan kun gama shiryawa sai mu wuce”.
      Zaram Hibbah tace, “Ai ga Yaya Ammar nan zaizo ya maidamu gida a motar Yaya Muhammad. Dama kaje abinka mun gode”.
          Ɗan kallonta yayi na wasu sakanni. “Oh auta, kodai bakison naima Ummi rakkiya na samu lada ne?”.
       Baki ta tura gaba ta dauke kanta batare data amsashi ba.
        Ummi tai murmushi da faɗin, “Kaga manta da ita Isma’il. Tunda kazo ka kaimu kawai shi Ammar ɗin bara na kirasa basai ya amso motarba ma”.
     Godiya yay mata yana ficewa. Hibbah kuma ta hau ƙunkunin ita batason motarsa ya cika shishshigi. Ummi na jinta amma tai mata banza. Sai ma ƙoƙarin kiran Ammar da takeyi a waya akan ya dawo basai ya amso motar ba ga Isma’il yazo.

         Badan Hibbah taso ba Isma’il ya kaisu har gida. Sai dai bai shigaba iyakarsa waje ya juya duk da Ummi tace ya shiga. Haƙuri ya bata akan yana sauri ne zai koma kasuwa.
      Albarka sosai Ummi ta saka masa. Hakama Ammar yayta masa godiya. Hibbah kam dama tuni ta shigewarta cikin gida. Sai Ammar ne ya kama Ummi suka shiga cikin suma. Babu motsin kowa a gidan da alama yaran duk sun fice. Hajiya mama kuma maybe tana barci ko kallon nata na masifa dan bata gajiya da sanya ido a television, shiyyasa jikokin nata har tsiya suke mata akan hakan.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button