Bakar Inuwa

BAKAR INUWA 12

           Ko mintuna ashirin basuyi da shigowa ba maƙwafta suka fara shigowa ƙara yima Ummi sannu. Ciki harda Zahidah da Hafsat tare da iyayensu. Sune suka taimakawa Hibbah wajen gyara gidan tsaf. Suka kuma daura girki. A kitchen ɗinne suka sami damar mata tambayar abinda ya faru ranar game da tafiya da ita da ƴan sanda sukayi.
      Duk da aminanta ne tun ƙuruciya sai bata faɗa musu komai ba yanda ya faru saboda tuno gargaɗi da akai mata akan idan ta fitar da zancen za’a saka mata ƴan uwa a tarko. Ta dai basu labarin iya abinda zata iya. Sosai sukaji takaici har cikin ransu. Nan fa suka shiga labarin rauni da hukumomin tsaron ƙasar nan suke da shi.
       Zahidah tace,  “A kullum ca ake ana aiki amma babu alamar hakan a ƙasa. Shin laifin gwamnati ne ko na jami’an tsaron?.”
       Cikin taɓe baki Hibbah ta amshe da faɗin, “Kema dai ƙya faɗa Zahidah. Ita kullum gwamnati tana faɗar kuɗaɗe da take warewa domin harkar tsaro. Amma su jami’an tsaron kullum ca suke basu da kayan aiki isassu. To wai kuɗinne ba’a warewa? Kokuwa jami’anne basa saye? kasa kuɗin suke a tebir kowa ya dauka kasonsa?”.
       Da tsantsar takaici Hafsat tace, “Duk ma yanda sukeyi ɗin ai akwai ranar tonon asiri. Ranar da babu wani gacci ko mayafi da ya isa lulluɓe tsiyar da aka shuka aka binne. Ranar da za’ai walƙiya muga kowa da ayyukansa”.
     A tare Zahidah da Hibbah sukace, (Insha allahu kuwa).
      Haka dai suka cigaba da tattauna abubuwa da dama har suka kammala girkin suka sake gyara Kitchen ɗin. Koda suka fito ɗakin Hibbah suka wuce dan har yanzu ƴan dubiya nata shigowa. Sai dai bayan maigadi ko karen da ke a cikin gidan har yanzu bai leƙo ba. Dama kuma basuje asibitinba. A cewarsu ai ba’a sanar musu bata da lafiya ba.

            Sai dare samarin na Ummi suka dawo. zuwa lokacin sashen tsit da ga Ummi sai Hibbah kawai. Hibbah ma tayi barci a kujera dan akwai gajiyar asibiti tare da ita. Sai sautin kiɗa dake tashi da ga sashen momynsu Junaid da hayaniyar ƴammatanta. Da alama wani fati sukeyi, duk da dai shan kiɗa a gidan ba sabon abu bane ba dama.
          Sannu Ummi tai musu. Yayinda suka zagayeta kowa nason jin yaya karfin jikinta?. Cike da jin daɗi da fara’a take amsa musu. Kafin tace suje suci abinci kar yayi sanyi. Ammar zai tada Hibbah Ummi ta hanashi.
        “ALLAH ka tada ita sai naci gidanku, ka barmin yarinya ta huta ta gaji wlhy, dan tamace kanta ke ciwo”.
              “ALLAH yasa gaskiya ne Ummi. Ni naga a kwanaki ukun nan wani sabon hankali take ji da shi. Ko ciwonki ne ya sata nutsuwa oho”. Ammar ya faɗa yana dariya.
     Suma su Yaya Muhammad duk murmushi sukayi suna nufar dining.

★★★
     
         Har washe gari babu wanda yazo ya duba Ummi a cikinsu hajiya Mama. Abba dama bai dawoba har yanzun. Ummi ko a fuska bata nuna ta damuba. Haka suma su Yaya Abubakar babu wanda yace uffan akan hakan. Sai ma tarkata Hibbah sukai ta wuce islamiyya tun safe kasancewar yau ɗin weekend ce akwai tahfiz da take zuwa dama har suma kansu.
        Badan taso zuwan ba ta tafi harda ƙwallanta dan taga abokin hamayyarta Ammar yau bazai je ba. Da yake a kafane babu nisa ita kaɗai ta fita. Sai da ta fitane taci karo da Hafsat da Zahidah sun taho biyo mata dama. Gaisawa sukai da tambayar jikin Ummi sannan suka wuce islamiyyar.

       Islamiyya ce babba matuƙa. Dan tun da ga ƴan shekara uku har zuwa saba’in duk zasu iya karatu a cikinta. sai dai su yara da ga shekara uku zuwa ashirin da biyar suna zuwa ne tun safe har yamma. Daga ashin da shidda zuwa har tsoffi suna zuwa bayan sallar azhar har magriba, kuma iya weekend ne kawai. Dan haka su su Yaya Muhammad sai karfe biyu zasuje. Itace dai da Ammar dama ke tafiya tun safe. Ammar kuma yau akwai abinda zaiyi shiyyasa bazai je ba.
        Kamar kowanne sati yau ma sun ɗauki darasi daban-daban har zuwa ƙarfe biyar na yamma da aka tashe su. A ƙafa suka taho Zahidah da Hafsat nata hira banda Hibbah. A yanda suka lura gaba ɗaya ta zama wata shiru-shiru. Kafin faruwar wannan al’amarin a kowane sati sukaje islamiyya sai ta addabi kowa a ajin ko ta takalo faɗa. Su kansu malam sun buga har sun bari, dan mafi yawancin lokaci ƙoƙarin ta ne ke cetonta akan wani tsiyar idan ta tafka.
        Cike da jin haushi Hibbah ta ja tsoki tana tsayawa cak da ga tafiyar da sukeyi. Kallonta Zahidah da Hafsat sukai cikin alamun sonjin lafiya?. Bata tanka musu ba, sai kallonta da ta maida kan motar da ke bin bayansu ta gefen titi tunda suka fito Islamiyyar. Suma su Hafsar ɗin sun lura tun ɗazun, sai dai basu kawo a ransu mai motar su yake bi ba. Musamman da ya kasance ya ɗan basu tazara.
           Domin tabbatar da su ɗin yake bi a bayyane yay fakin dai-dai inda Hibbah da ta cika tai fam da takaicinsa take.
       Cikin takun nutsuwa da cikar haiba ga ma’abocin kallo ƙyaƙyƙyawan saurayi mai tarin kamala ya sanyo kafarsa ƙasa dai-dai yana buɗe ƙofar motar mai baƙin gilashi (tinted glass). Wani shegen ƙamshin turarensa ne ya daki hancunansu tare da sallamar da ke fita cikin ƙasaitacciyar muryarsa mai tarin nutsuwa da sanyi……………..✍

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button