BAKAR INUWA 13

Wata irin muguwar hajijiyace ta fara ɗibar Ramadhan. Dan dama can shi bayason ihu, musamman idan yana akan gaɓar bacin rai tuni ake samun matsala kansa ya nema juyewa saboda tsananin yanda ƙwalwar kansa ke kasa ɗaukar tashin hankali mai shallake tunani. Lokacin da yana yaro idan hakan ta faru ansha cemusu yanada aljanu ne masu ƙarfi sosai. Sai dai basu taɓa yarda ba dan su sam basu cika ɗaukar waɗan nan abubuwan da muhimmanci ba (kamar yanda kowa yasan ɗan boko🙏🏻), sai dai hakan baya hana duk lokacin da abu ya faru makamancin matsalar ta biyo baya Anne ta zauna tai masa addu’a a ruwa da saman kansa har sai ya samu nutsuwa sannan. Amma abin mamaki zai iya yini yana ajiyar zuciyar wannan ɓacin ran, ko kuma ya yini a ɗaki yana barci. Sannan sai ya haɗa kwanaki biyu zuwa uku baiyi magana da kowa ba. sai dai ya samu wajen ruwa ya zauna, ba kuma zaici abinci ba duk da kasancewar sa ma’abocin son abinci sai Anne ta takura masa shan abu mara nauyi kamar su fura yogurt, fresh nonon shanu ko na raƙumi da makamantansu. Dan yana tsananin son madara da dukkan nau’ikanta a rayuwarsa. Bayan aurensa da Amnah idan ransa yay irin wannan ɓacin yakan hucene a kanta ta hanyar yin tarayya da ita yanda zata jigata har sai an kwantar da ita a asibiti abinka da sikilla. Dan likitocin kance ko mai lafiya akaima irin wannan kamun babu shakka zataji a jikinta balle Amnah ɗin. A duk lokacin da fushin ya sauka yakan shiga damuwa idan ya kalli yanda ya fiddata hayyacinta. kai wani lokaci ma har saida akai mata ɗinki tsabar lamarin Ramadhan yana bukatar addu’a🤦🏻. Amna kam tana jin jiki da shigar Ramadhan irin wannan yanayin, sau biyu yana sakata ɓarin ciki. da tana raye na tabbatar zatace hakan shine mafi girman tashin hankali a rayuwar aurenta da Ramadhan ɗin, shiyyasa duk wani fushinsa take gujewar wanzuwarsa a karan kanta.
Yanda ya fara juya kai jijiyoyin na tashi sama da maƙogwaronsa dake kai kawo a wuyansa, gashin kansa na mimmiƙewa yasa Bappi fahimtar mike shirin faruwa. Yasan Ramadhan bazaice komaiba, dan shi mutum ne mai tsananin tsoron saɓama iyaye, shiyyasa daya dage akan bazai dawo NAYA ba a shekaru biyar ɗin nan abun ya basu mamaki matuƙa, dan duk rintsi baya ƙetare maganarsu.
Da sauri Bappi ya girgizama Alhaji Basheer kai yana miƙewa ya riƙo hannun Ramadhan daya fara ƙoƙarin ɗaga ƙafa yana jujjuya kansa cikin tafukan hannunsa daya riƙe kan nasa. Tuni idanunsa sun rufe ruf saboda wata baƙar hajijiyar da yake gani falon na juya masa da wani irin shegen gudu.
Babu abinda ke maimaita kansa a kwakwalwar Ramadhan da zuciyarsa sai “Ramadhan!! Nace ka fita a gidan nan yanzun nan!. Bana son sake ganin wannan fuskar taka!!”. da Pa ya faɗa.
“Zan tafi Pa, bazan sake nuna maka fuskar nan ba nayi alƙawar…..”
“Shut up!!”.
Bappi ya faɗa da ƙaraji shima yana katse Ramadhan ɗin bayan ya fisgosa ya zube a saman kujerar kusa da shi. Juyawa Alhaji Basheer Taura yay a fusace yabar falon, shi kansa wani irin jiri-jiri na neman fara ɗibarsa. Sai hakan yasa yakejin yana tafiya tamkar akan iskar dake kaɗawa har zuwa sashen nasa. Bai iske gimbiya Su’adah ba. Da alama taje shirin barci. Dan haka yay kwanciyarsa, koda ta shigo bayan kusan mintuna talatin da kwanciyarsa bai motsaba. Hakan yasa tai tunanin ko yayi barcine. Sai kawai taja bargo ta lulluɓa masa bayan ta rufe wasu a murafan windows ɗin dan iskar ta fara yawa.
WASHE GARI
Da mamaki kowa ya tashi yaga Ramadhan a gidan. Sai dai a yanayin da yake na hawa saman dokin zuciya yasaka bakin yaran gidan rufewa ruf. Dan ko kallonsa kayi bakaso sake ganiba fuskar tamkar zatayi aman wuta😜.
Gimbiya Su’adah ce kawai ya iya tankama tambayarta itama a taƙaice, dan ita firgitama tayi da ganin nasa. Har zuciyarta na raya mata kodai da gaske Ramadhan ɗin nada aljanune wai?.
Ko amsa ɗaya bata samu daga tarin tambayoyin da take jera masa ba, sai ma miƙewa yay yana sanar mata cewar zai koma America.
“America!”.
Ta maimaita da yanayin ruɗani da tashin hankali. ita dake murna ɗanta ya dawo gareta kuma. Kafin ta sake cewa wani abu yayo waje. Dan dama a bedroom ɗinta ya sameta kasancewar ta duba an kammala shirya abincin breakfast na Pa tazo dan ta shirya, sannan taje ta tadashi a barcin daya ɗan koma na safe bayan dawowarsa masallaci.
Har ya fice a sashen baki ɗaya bata dawo hayyacinta ba. Dan da alama sumar tsaye tayi kawai.
★
“Shiga mota muje”.
Bappi ya faɗa idonsa akan Ramadhan daya fito daga sashen iyayen nasa a wani irin yanayi. Duk da alamu sun nuna yayi wanka ya canja kaya hakan bai hana fuskarsa bayyana yanayinsa na jiya ba. Sanye yake cikin wani tattausan tissue yadi da basai ance komai game kallo ba wajen hasashen irin kuɗin daya lasa na sayensa dana ɗinkinsa. Duk da simple style ne a jikinsa hakan bai hana bayyanar tsadarsa da fitar ɗinkin ba a bisa ƙyaƙyƙyawar ƙirarsa ta mazantaka da ƙuruciya ba, ga shi baƙi sai farar fatarsa ta sake haskawa. Babu alamar sumar kansa ta samu gyara yau tsabar yanda ta hargitse, sai dai hakan bai hana ƙyawunsa bayyana ba harma ya ɗauka hankalin wasu mutane koda ba kowaba.
A tunaninsa airport ɗin zasuje, kamar yanda ya sanarma Bappin yau zai koma bayan sun fito da ga sallar asuba. Dan haka babu musu ya shige inda M. Adamu ya buɗe masa kusa da Alhaji Hameed Taura (Bappi). A wata jiƙaƙƙiyar mota data gama haɗuwa. A tsammaninsa ƴan kayan buƙatarsa dake cikin bag an riga an fiddo masa tuni………✍
Tofa ina Bappi zai kai mana wannan young tiger ɗin mai kama da barkonon noman ranin😎🏃?.