BAKAR INUWA 14

★★★★★★★★
Tun kan su ƙarasa asibitin Isma’il yay ƙoƙarin kiran doctor Bilal. Cikin sa’a kuwa ya ɗaga dan mutuminsa ne. Bayani yay masa cewar gasu a hanya tare da mara lafiya su zam cikin shiri. Dr bilal yace babu damuwa sai sunzo.
Cikin mintuna kalilan kuwa suka iso asibitin saboda uban gudu da yake zugawa a hanya. Kamar yanda yay fata sun sami su Dr Bilal na dakon isowarsu. Babu ɓata lokaci aka shiga da Ummi ciki.
Kuka sosai Hibbah keyi da son binsu, badan yaso ba ya riƙo hannunta yana ƙoƙarin dakatar da ita. Sai dai taƙi ta nutsu, dole yay mata yanda yasan zata nutsun, ya jawota jikinsa ya rungume. Da ƙarfi ya rumtse idanunsa zuciyarsa na wani irin bahagon gudu.
Itako Hibbah tuni ta ƙara lafewa tana wani irin kuka mai ban tausayi, dan gaba ɗaya ma ta mance a jikin wa take. Sai da ƴar nutsuwa ta fara zo mata ne sakamakon kiran wayarsa da akayi tai azamar janye jikinta. Komai baiceba shima. Sai ƙoƙarin ciro wayarsa da yay a aljihun wandonsa. Ita kuma ta koma kan kujera ta zauna tana cigaba da kukanta da add’ur ALLAH ya bama Umminsu lafiya.
Yaya Umar da yaga miss call ɗinsa bayan fitowarsu massallaci ne ya kirasa. Dan haka yay masa bayanin da bazai ruɗar da shi ba. Koda ya yanke kiran sai ya shiga kiran sauran suma.
★★
Cikin mintuna kalilan yaran Ummi suka gama hallara a asibitin. Gaba ɗaya hankalinsu a tashe yake. Sai dai sunata ƙoƙarin lallashin Hibbah da ke kuka sosai har yanzu. Harda su amai. Ga zazzaɓi mai zafi ya gama lulluɓeta matuƙa.
Fitowar Dr bilal ya sasu maida hankalinau garesa. Cikin son kawar da damuwarsu yace, “Ku kwantar da hankalinku babu wata matsala mai yawa insha ALLAH. Dan yayi ƙoƙarin kawota asibiti akan lokaci. Sai dai ku kiyaye dan ALLAH kar yazam muna tufƙa ana warwarewa.”
A take nutsuwa ta saukar musu. suka shiga jerama Isma’il godiya tamkar zasu ɗaukesa su goya. Shi dai ransa a dagule yake da takaicin Abbansu, dan shi baisan ba mahaifinsu bane.
Sun cigaba da dakon jiran farkawar Ummi da aka sakama ƙarin ruwa a asibitin har wajen sha biyu na dare da aka basu sallama saboda Alhmdllhi komai normal, amma sai Dr Bilal yace su barta anan ta ƙara hutawa har sai gobe idan ALLAH ya kaimu da yamma. Duk sun gamsu da bayanin nasa. Dan haka sukai masa godiya da fitowa dan su tafi gida Hibbah da zata kwana da ita tare da Nurse tayo musu rakkiya.
Har sannan Isma’il na tare da su. Karan farko a tarihi da Hibbah ta dubesa cike da girmamawa da idanunta kumburarru. “Yaya Isma’il mun gode sosai. ALLAH ya bada ladan zuminci. Yanda ka jikan Ummin mu, kaima ALLAH ya baka ƴaƴa da zasu jiƙanka. Ya ƙarama Abbanka lafiya da tsahon rai mai amfani, ya jiƙan Umma”.
Ba karamin ratsa zuciyarsa addu’ar tata tayi ba. Ya kafeta da ido har sai da Yaya Umar ya zunguresa sannan ya sauke ajiyar numfashi da sakin murmushi. “Nagode sosai auta. ALLAH ya karama Ummi lafiya ya albarkaci rayuwarki. ALLAH ya baki miji na gari”.
Cikin jin daɗi yayunta suka amsa masa da amin. Itama tattausan murmushi da bata taɓa masaba a yanzu ta saki tana juya baya alamar taji kunya da addu’arsa ta ƙarshe. Su Yaya Usman suka ƙyalƙyale da dariya Ammar na tsokanarta. Bata kulashi ba dan yau batajin yin faɗa Ummi bata da lafiya.
Tun a asibitin suka rabu da Isma’il. Shi yay gida suma suka wuce gida. Inda tunkan su shiga sukaji labari a bakin maigadi cewar Abba ma na asibiti. Ya fadi ne a bakin ƙofa da alama yaji ciwo a kafafunsa. Hakama goshinsa da bakinsa sun fashe yanata zubar da jini ma.
Kasancewar da ga Hibbah har Isma’il basuyi musu bayani ba sai basu kawo komai a ransu ba suka ɗauka tsautsyine kawai. Addau’ar samun lafiya sukai masa suka shige. Dan ba’ai musu tarbiyyar son ganin lalacewar wani ba koda ace maƙiyinsu ne.
____________________
A ɓangaren Abba kam da ƙyar aka iya ɗagasa da ga inda Isma’il ya taɗesa. Bakinsa duk ya fashe da goshinsa daya daushi kwalliyar tsitstsigen baranda. Hakama kafafunsa da alamar yayi karaya ko targaɗe. Dan ko takasu baya iyayi ma. Hasalima a sume aka ɗaukesa da ga gidan zuwa asibiti saboda jinin da yayta kwararwa kafin Junaid yazo da mota su fita da shi zuwa asibiti.
Su hajiya mama babu wanda yasan ainahin abinda ya faru da Abban suma. sai dai kansu ya ɗaure matuƙa ganin da ga shi sai boxer kayan da ya fito da su a hannu sabida ihun Hibbah yashe a gefe. Sunma rasa yaya zasu fasalta al’amarin musamman da likita ya tabbatar musu kafarsa ɗaya ta samu karaya da hannunsa. Ɗayar kuma tsagewar ƙashi ce ga ciwon goshinsa dana bakinsa da yay wanu zundun-dun uwa an saki shantu.
Hajiya mama ta hana ai masa gyaran karayar wai sunada mai gyaran gargajiya zaizo da ga kauye. Sai a jirasa yana hanyar tahowa. Tun yamma ake jiran mai gyara har dare ya tsala bai iso ba. Haushin abinda Hajiya mama tai musu su kuma likitocin sunce bazasu taɓa ƙafar ba har sai wanda tace ɗin yazo ya gyara masan. Duk roƙon da Momy taita musu sunce bazasuyiba wlhy.
WASHE GARI
Da safe acikin su Yaya Abubakar babu wanda yabi takan zancen duba wani Abba. Da dai su Ammar suka kammala yin breakfast suka gyara gida sai suka runguɗa asibiti wajen mahaifiyarsu. Sun isketa zaune Hibbah na shafa mata mai saboda wanka da tayo.
Ta dubesu cike da tausayi da begen ƙishirwar murmushinsu. Duk wanda ya gaidata sai ta kamo hannunsa ta shafa kansa tana ƙoƙarin haɗiye hawayenta.
“Ku daina fushi da Umminku kunji”.
Ta faɗa cikin damuwa da ƙunar da takeji a cikin zuciyarta. Komai basu iya cewa ba sai dai dukansu sunyi ƙasa da kawuna ransu fal tausayinta. Musamman Yaya Muhammad da yasan wani yanki na labarinta batare da itama ta sani ba, shima Abbansu ne ya sanar masa kafin ya rasu. Ya kuma tabbatar masa ya faɗa masane saboda wataran yasan kunnensa zaiji gorin da za’aima mahaifiyarsa kar zuciyarsa ta ɗauki wani abun daban. Shine ya fara jan numfashi da ƙyar da dubanta yana ƙoƙari haɗiye hawayen da suka ciko masa ido.
“Ummi baki mana laifin komai ba. Amma dan ALLAH a wanan gaɓar munason jin wani abu game da ke. badan bamu yarda dake bane. Sai don son sanin minene dalilin da yasa duk basa ƙaunarki?. Mi kikayi musu haka da zafi? Miyasa kika yarda kika auresa bayan shiɗin kanin Abbanmu ne? Mai fuska biyu ga mutane”.
Murmushi ta saki mai kuna da kai hannu ta shafo kan Yaya Muhammad. “Muhammadu Aminullahi zan faɗa muku insha ALLAH. Da zaran munje gida yau zakuji komai”.
A take fuskokinsu suka nuna jin daɗin zancenta. Dan danan suka ɓalle mata hira kamar yanda suka saba a baya. Itako sai murmushi take zuciyarya na kara sanyaya da ɗunbin sonsu da kaunarsu.
Dr bilal ne ya shigo, bayan sun gaisa yace suje waje zasu ɗan ƙara duba Ummin suga ya ya komai na tafiya normal. Sun masa godiya tare da fitowa su duka. Duk anan ƙofar ɗakin suke zaune Hibbah nacin abincin da sukazo da shi. Kamar ance ta ɗaga kai sai idanunta karaf akan Zahidah da Hafsat, Muhammad Shuraim biye da su.
Babu shiri ta miƙe zaram tana rarraba idanuwa. Tunkan su ƙaraso tace, “Lallai ma! Miya kawoka nan?”.
Furucin natane yaja hankalin yayun nata gaba ɗaya. A tare suka sauke idanunsu bisa kan Muhammad Shuraim da ke sanye cikin ado da kamshi na shadda da keta maiƙo, ga hular zanna da ya murza wadda ta kara masa cikar kamala da kwar jini.
A fusace Hibba ta sake buɗe baki zatai magana Yaya Umar ya harareta. Dole tai shiru tana wani mar-mar da idanu akaikaice tana ballama Shuraim harara.
Shiko murmushi ya saki yana matuƙar jin mamakin tsaurin ido irin na Hibbah. Ya cigaba da takowa a hankali zuwa gaban su Yaya Muhammad da duk hankalinsu a kansa yake suna kallonsa cike da nazari. Duk da zasu iya yin sa’anni da Yaya Umar cikin girmamawa ya shiga gaishesu su duka. Gashi yaki yarda ya haɗa idanu da su shi a dole yana gaban surukai.
Hakan ba karamin dariya da burgesu yay ba. Ammar sai wani ƙara buɗe ƙwanji ake su a dole yayu. Yaya Muhammad ya ce, “To sai dai bamu gane baƙon namu ba?”.
Murmushi Shuraim yay cike da ladabi yana ɗan shafar ƙeya yace, “Yayanmu bazaka sanni ba. Dama ina jiran lokaci ne nazo gareku. Sai dai jin Momy babu lafiya yasa nazo dubata kafin hakan. Sunana Muhammad Shuraim Aliyu. Mai fata da addu’ar samun nutsatstsiyar yarinya mai tarbiyya kamar Muhibbat….”
Wata malalaciyar harara Hibba ta zuba masa tamkar zata fashe dan takaici da haushinsa. Yayinda Ammar dake guntse dariya a kaikaice yace, “Dama dai a tarbiyyar ka tsaya dana yadda. Amma ba Nutsuw…..”
Gwiwar hannu Yaya Umar dake gefensa yasa ya bugesa. Yay azamar rumtse ido da ɗaura hannunsa a wajen yana faɗin, “Wayyo Ya Umar zaka kashe ni”.
Yaya Abubakar kam murmushi ya sakarma Shuraim shi da Yaya Muhammad. Haka kawai su dai Shuraim ɗin ya birgesu matuƙa. Dan haka Yaya Abubakar yace, “Masha ALLAH mun gode matuƙa. Bara doctor ta fito sai mu shiga ka dubata”.
Sosai daɗi ya kama Shuraim, ya shiga jera musu godiya da addu’ar samun lafiya ga Ummi. Su ma su Zahidah suka shiga gaishesu da tambayar jikin Ummi ɗin. Hibbah kam taƙi kulasu suma wai haushinsu takeji sun faɗama Shuraim sirrinta.
Suma basu kulata ba dan sun gane manufarta sarai. Haka ta ringa antaya musu harara suna ramawa har Doctor ya fito suka shiga su duka.
Tunda suka shigo Ummi take kallon Shuraim da ya durƙusa har ƙasa ya gaisheta da tambayar jikinta. Fahimtar ƙarin bayani take buƙata yasa Ammar fara rattafo zance. Sosai murmushin fuskar Ummi ya sake faɗaɗa. Dan har cikin ranta taji ƙaunar Shuraim da samun nutsuwa da shi. Tana kuma fata da addu’ar ya zame musu mafita akan haɗa Junaid aure da Hibbah da ake ƙoƙarin ƙullawa.
Basu wani jima sosai ba yace zai wuce, bayan ya ajiyema Ummi ledan dubiya. Godiya suka sake masa Ammar ya tafi rakasa. Yana ƙoƙarin ficewa Isma’il ke ƙoƙarin shigowa. Baya ya koma ya bashi hanya. Batare da tunanin komai ba Ammar ya gabatar da Shuraim ga Isma’il ɗin. Shima Shuraim Ammar ya gabatar masa da Isma’il matsayin ɗan uwansu. Hakan ya basu damar yima juna kallon ido ciikin ido. Da alama kallon da Isma’il yayma Shuraim ɗin na tsantsar kishi ne da shima kansa baisan yayi ba. Haka shima Shuraim kallon alamar tambaya da tsoron sakkiyar da babu ruwa yayma Isma’il ɗin kai tsaye. Cike da basarwa kuma sai suka saki hannun juna kowa na ƙoƙarin haɗiye abinda ke ransa da cikin idanunsa, kafin su kalli Hibbah a tare Shuraim ya ida ficewa, Isma’il ya karasa shigowa…………✍