BAKAR INUWA 15

Chapter Fifteen
………Kamar yanda doctor Bilal ya faɗa a ranar suka sallami Ummi tare da sharuɗan da za’a kiyaye game da lafiyarta. Su Yaya Abubakar sun amsa masa tare da tabbatarwa. Wannan ɗin ma akasi aka samu kawai. Da ga haka sukai masa godiya suka tafi da sanyin idaniyarsu gida.
Koda suka isa gidan babu wanda yayma Ummi zancen Abbah, hasalima su sun manta ma. Hidimarsu suka cigaba da yi hankali kwance har dare. Sai da zasu kwanta ne Ummi taji shirun gidan yayi yawa take tambayar Hibbah data maƙale a ɗakinta zata kwana. Bargo Hibbah taja har saman kanta tana sake bajewa a gadon na Ummi. “Ummi nima ban saniba. Ƙila sunje ƙauye ne”.
Shiru Ummi tai tana nazari, tasan Momy ko kowa zaije ƙauye ita dai bazataje ba. Hakama ƴammatan ƴaƴanta. Hajiya Mama da Abban ne kawai suke zuwa, suma idan aikin sharrinsu ya tsikaresu, kuma Abba ma ai bai jima da dawowa ba. Ajiyar zuciya ta sauke da kauda zancen a ranta itama ta kwanta tare da kai hannu ta janye bargon da Hibbah tasa har saman kai.
Duk yanda Ummi taso yin barci gagararta yayi, sai ma dulmiyawa da tai a ƙololuwar duniyar tunani da neman mafita. Taja tsahon lokaci tana ƙullawa da kwancewa kafin ta sami mafitar da take addu’a da fatan ta zame musu alkairi ita da zuri’arta.
Da asuba bayan sun idar da salla Ummi ta dakatar da Hibbah da ga barcin da take ƙoƙarin komawa gado tayi. Cike da shagwaɓa ta lafe a jikin Ummin tana faɗin, “Wayyo Ummi ALLAH barci nakeji, kinga yau weekend ne babu makaranta sai islamiyya, su Yaya bazasuje aiki ba na san suma barcin zasuyi”.
Murmushi kawai Ummin tayi, zuciyarta najin tausayin autar ta bisa hukuncin data yanke akan lamarin duk ƴaƴanta a daren jiya. “Muhibbat!”.
Ta kirayi sunan Hibbah dake lumshe idanu babu wasa. Idanu Hibbah ta buɗe tana kallon Ummin, dan yanda ta kirata da cikakken sunanta babu wasa tasan ƙwarai magana ce mai muhimmanci.
“Na’am Ummi”.
“Tambayarki zanyi?”.
“To Ummi, ALLAH yasa na sani”.
Numfashi Ummi taja da kafe Hibbah da ido. “Duka yayunki babu mai neman aure ne dama?”.
Ɗan jimm Hibbah tai alamar nazari. Kafin tace, “Ummi wai kina nufin sunada ƴammata?”.
Kai Ummi ta jinjina mata kawai.
Hibbah ta ƙyalƙyale da dariya tana kwantawa ta ɗaura kanta a cinyar Ummi. “Uhm ai Ummi fa dama tun kwanaki nakeson na baki labari Yaya Umar ya gargaɗeni. Wai so suke suyi miki surprise ne. Kinga Yaya Muhammad yana da budurwa, Maimunatu (Kausar) ɗin gidan Sheikh Aliyu Abdul-Ra’uff Maina abokin Daddyn mu, mai islamiyyarmu kuma ɗiyar kawarki…….”
Wani irin farin ciki da sanyi ne ya lulluɓe zuciyar Ummi lokaci guda. Ta katse Hibba cike da zumuɗi. “Da gaske Tanee?”.
“Wlhy kuwa Ummi. Kin dai santa babu ruwanta ga hankali, kina zuwa gidansu, suna zuwa nan gidan kinsan tarbiyyarsu. Gata malama a Islamiyyar tamu. Akwai wani dabino da zam-zam da zuma da Yaya Muhammad ya kawo miki kwanaki na rantse itace ta bada a baki. Amma yace idan na faɗa sai ya fasan baki.”
Yanda Hibbah ta ƙare maganarne ya saka Ummi ƙyalƙyalewa da dariya. “Kai Mamana har yanzu dai ke sakara ce ALLAH, basai ki gayamin a sirri ba. Sam baki biyo mai sunanki ba. To Abubakar fa?”.
Cikin dariyar zancen Ummi Hibbah tace, “Tab na Zahidah kenan.”
“Wannan Zahidah ta gidan Auntyn ku Kulu dai dana sani?”.
“Eh wlhy Ummi. Amma yace karsu faɗama kowa sai ta gama makaranta. Nima basusan na ganeba a ɓoye sukeyi”.
Nanma dariyar farin ciki ce ta bayyana akan fuskar Ummi. Har ranta zaɓin Yaya Abubakar da na Yaya Muhammad sun mata hundred percent. Hibbah ta cigaba da faɗin, “Shi kuma Yaya Umar Nafisa ce nasan kin sani dama. Yaya Usman kuma Hafsat itama kin sani. Zakin ki kuma babu kasuwa har yanzun”.
Sosai Ummi taji matuƙar daɗi, dukkan damuwarta sai ta gushe a lokaci guda. Taji ƙwarin gwiwa bisa ga abinda take shiryawa. Dukkan fargabarta ta gushe. A ɓangaren muhalli bata da matsala da yaranta, duk gine-ginensu sai dai ƙarashe. Dan suna fara aiki suka haɗa hannu wajen fara ginin filin da taketa tattali da kaffa-kaffa domin su. Burinta ita da mahaifinsu yanda suka tashi kansu a haɗe su cigaba da rayuwa a waje guda. Shiyyasa koda ya sai filin sai ya damƙashi hannun amininsa kuma malaminsa har sai da suka fara aiki ya basu. Shiyyasa har yanzu Abba da Hajiya Mama basusan da zancen ginin ba……..
“Ummi inje in kwanta?”.
Hibbah ta katse mata tunani. Shafa kanta Ummi tai tana murmushi. “A’a ban gama da ke ba. Dan banji ita autata tana da saurayi ba ko a’a?”.
Da sauri Hibbah ta ɓoye kanta tana dariya. “Kai Ummi ni banda wani saurayi. Nifa bazanyi aure ba muna tare mutu karaba”.
“Tab, to auta an taɓa haka kuwa. Muma ai munason zaman gidanmu aka ɗakkomu aka kawo mu naku gidan muka haifeku.” Ummi ta faɗa tana dariya.
“Ni dai bazanyiba ALLAH Ummi. Banason nesa da ke da su Yaya. Indai zanyi aure sai dai mutafi tare ko mijin yazo ya zauna a gidanmu to”.
Dariya sosai Ummi keyi, irin wadda ta jima batayi ba a rayuwarta. Tanee ɗinta kayan shirme da wauta kenan. Da ana haka da ƴaƴa da yawa na tare da iyayensu ai.
Tashi Hibbah tai da gudu ta haye gadon Ummi ta kudundune a bargo ita a dole kunya ta kama ta. Ummi da ke dariya tace, “To shikenan ai ke baki da matsala tunda Junaid ɗan gidan nan ne sai kiyi zamanki tare dam……”
“ALLAH Ummi bana sonsa. Da na auri mugun nan gara na mutu”. Hibbah tai saurin yaye bargon idanunta na cikowa da hawaye. Yayinda fuskarta ke nuna tsananin tsoro da tsanar Junaid ɗin da Ummi ta ambata.
“To shikenan naji. Amma ai kina son Isma’il ko?”.
Idanu Hibbah ta zaro waje a firgice. “Wane Isma’il ɗin Ummi?”.
“Mai zuwa nan gidan mana”.
“Ni dai wlhy a’a Ummi. Shi yayana ne dan ALLAH kibar faɗa.”
“Oh ALLAH, ke kuwa Tanee wa kike so a rayuwarki? To ko wanda yazo dubani a asibiti jiya? Muhammad Shuraim ko?”.
Baki Hibbah ta turo amma batace komai ba. Ummi ta cigaba da faɗin, “Tanee kinga shima alamunsa sun nuna mutumin kirki ne nutsatstse. Ina ƙyautata masa zaton alkairi insha ALLAH. Amma zansa ai bincike a kansa inhar kina son nasa”.
Kwanciya Hibbah tai ta juyama Ummi baya. “Ni Ummi ALLAH ya cika iyayi. Gashi baida fara’a. ga shishshigi ”.
“Duk shi kaɗai?. To lallai tunda kika iya gano waɗan nan kina sonsa kenan, zaki kuma auresa”.
Da sauri Hibbah taja bargo da cewa, “Nifa Ummi a’a baiminba. Sai naje China na dawo zanyi aure”.
“Tanee wannan mafarkinki ne. Amma ban fidda miki ran zaki cikashi ba idan kinyi aure mijinki ya kaiki da kansa”.
Shiru Hibbah tayi dan an taɓo mata inda kuma bata son. Itama Ummi sai bata sake tankawa ba ta cigaba da hidimarta da lissafin ƙullawa da kwancewa.