Bakar Inuwa

BAKAR INUWA 15

      Yau da yamma Hibbah na makaranta ta fito class cike da gajiya da yunwa. Fatanta kawai ta samu motar komawa gida da wuri dan su Hafsat tuni sun wuce saboda ba department nasu ɗaya ba. Su kuma yau duk lecture ɗin safe sukayi. Ita kaɗaice tayi na yamma.
          Ta samu da yawan ɗalibai dake ta tutsutsun shiga motar da duk tazo wucewa. Dan haka tai gaba saboda kanta dake ciwo. Cikin sa’a kuwa tana matsawa gaban sai ga wata taxi ta faka gabanta. Batare da tunanin komaiba ta afka ciki bayan ta sanarma direban inda zai kaita, shi kuma ya faɗa mata kuɗin. Ko ragi bata nema ba dan buƙatarta kawai taje gidan da wuri. Saboda tana tsoron abinda zaije ya dawo ne musamman akan dangin Abbansu dake cike da gidan nasu dubiyar Abba. Dan zuwa yau da yake cika kwana uku jikin nasa da sauƙi.
      Ƴan can asalin kauyensu ne sukazo mota guda duba shi. Sai dai hakan ya bama Ummi mamaki da su kansu, dan sam da ga Abba har hajiya mama bason mu’amula da ƴan ƙauyen sukeba yanzun. Shiyyasa har ƙasan ranta takejin akwai wata a ƙasa da suke ƙullawa.
        Wasu hawayen tausayin Ummi da su kansu ya cika mata ido. bayan hannu tasa ta share tare da kwantar da kanta jikin sit ɗin ta lumshe idanu ko kanta zai sassauta sara mata…….

         Ummi nacan na dakon jiran dawowar Hibbah itama, dan yau da kanta ta soyama Hibbar wainar filawa da tasan tana matuƙar so. Yayinda can ƙasan ranta ke cike da fargabar taruwar dangin mijin nata da nata a gidan. Dan tasan akwai abinda suke ƙullawar da gaske. Sai dai kuma ta saka a ranta komi zasu ƙulla insha ALLAHU ta gama shirya musu a wannan karon. dan itama tun a jiya data fita ta gama tsara komai akan makomar ƴaƴanta. Nasu kawai take jira yanzu ta ɗora da ga inda ta tsaya. 

        Ilai kuwa hasashen Ummi yayi dai-dai, dan tana tsaka da wannan tunanin akai kiranta sashen Abba ɗin. Hijjab ta saka har ƙasa ta tafi. Tun a falo Maomy ta sakar mata wani habaicin da ya tsaya mata a rai. Sai dai batace komai ba ta ƙarasa falon Abba.
        Su kawu Bello ta samu da wasu a dangin Abban. Sai hajiya mama. Bayan ta gaishesu ta nema waje ta zauna duk da ba dukansu suka amsa ba. 
            A gadarance Kawu Ayuba ya fara bayani. “Hasiya basai mun sake ɓata lokacin tisa magana ba. Nasan kema tunda kika ganmu anan kinsan zancen. Kamar yanda su Yaya Ballo sukazo kwanaki akan maganar auren ƴaƴanki da yaran wajen Alhaji Halilu yanzu batun saka rana ne ya tashi. Saboda tsabar halacci da hangen nesa irin nasa yace kawai tunda munzo dubasa a saka. Shi baya wani bukatar ƴan kunji-kunji tunda batun tuwona maina akeyi. To a yanzu haka dai ga kayan saka rana nan ma duk ya saya dan yace shine uban anguna shine na amare, kuma koma bai faɗa ba dama shine, tunda tun suna kananunsu shiketa wahala akansu. Koda kuwa mahaifinsu na raye shine mai bada auren nasu ai dama. Basai na jaki da nisa ba. Yanzu haka dai an yanke ranar aure wata biyu kacal. Batun kayan aure na akwati da kukeyi anan binni duk yace zaiyi baya buƙatar komai da ga yaran nan. Ita kuma Muhibbatu tunda kun saka yarinya ta nuna bata bukatar wannan haɗin, da azo ta bijire bayan auren kota illata yaro kawai za’a fasa. Za’a bata shi wanda ta kawo ɗin ALLAH ya basu zaman lafiya…..”
      A firgice Ummi ta dago ta dubi Abba. Wani shegen murmushi ya sakar mata tare da kashe mata ido ɗaya. Zatai magana yay saurin katseta cikin marairaicewa. “Hakan ai shine yafi kwanciyar hankali Kawu Ayuba. Kaga da alalata zuminci gara dai abi komai a sannu zaifi. Kuma ita mace ce. Banason a cuta mata akan abinda bataso. Dan yarinyace mai hankali da nutsuwa. Duk da damuwar da Junaid ɗin ya shiga nace ya haƙura kawai tunda tana da zaɓinta. Kuma zaɓin nata ma naga mutumin kirkine sunansa Muhammad Shuraim. Ɗan gidan Alhaji Aliyu ne mutumin kirki. Inajin kunyar ma nace bazan bashi jinina ba”.
        Harga ALLAH Ummi ta shiga ruɗani, ta kuma ji ɗan sanyi ta wani fannin. Dan tana mamakin ta yaya shi Abban yasan da zancen zuwan Iyayen Muhammad Shuraim ɗin? Kodai su masu kawo kuɗinne sukai mistake ɗin zuwa nan kawo kuɗin maimakon gidan Sheikh Aliyu Abdul-ra’uff Maina? Lallai akwai abinda bata sani ba. Dan akwai manufa da dalilin yin hakan ga Abba, saboda halin makircinsa da ta sani. Hakanan salin alin bazai hana ɗansa ba ya bama wani………
          “Wannan shaiɗancin dai nasan ita ta kitsashi. Duka yarinyar nawa take da tasan wani bijirema zaɓin iyaye. Ni wlhy dan Halilun yace a barta ne da baza’a bari ba. Sai dai idan an aura mata Junaidun ta mutu”. Sababin Kawu Bello ya katse ma Ummi tunaninta.
      Cikin makirci Abba ya amshe da faɗin, “A’a kawu bello ba’ayi hakaba ai. shima wnanan ɗin mutumin kirki ne wlhy. Dan yamafi Junaid nagarta. Muyi fatan ALLAH yasa haka shine yafi alkairi”.
     A take duk ƴan falon suka shiga yabon Abbah da jinjinama ƙoƙarin sa, Ummi kam anata zaginta wai bata da godiyar ALLAH akan ƙoƙarin da Abban keyi tun bayan rasuwar mahaifin su Ammar. Tare da yi mata gugar zana na habaicin asalinta.
     Ita dai uffan batace da su ba. Hasalima hankalinta ya rabune gida biyu. Duk sauran bayanan da suka cigaba dayi sai tama koma bata fahimtar komai. Jinsu kawai dai take da kunne da binsu da ido har aka tashi a taron ko nace suka sallameta.

       Koda ta fito a sashen taso zuwa gidan malam sai dai gudun abinda zaije ya dawo da fitar tata yasa ta haƙura. Dan haka tai kiran numbar wayar matarsa da yake ƙawarta ce suna zuminci sosai duka biyun. Sai dai tasan uwargidan Maimunatu yanzu haka tana Oman da autan gidan dake karatu acan.
     Bugu biyu Malama Jiddah ta ɗauka. Bayan sun gaisa da ɗan barkwancin ƙawaye Ummi take tambayarta ko Malam na nan kuwa?.
        Malama Jiddah tace, “Eh yana nan, sai dai yana tare da kamar baƙin da naji kunyi magana ranar zasuzo yau ɗin. Lafiya dai ko?”.
        “Tofa, kaji wani kuma ruɗanin. Umm Muhammad! Lafiya dai ba lafiya ba. Akan baƙin dama na kirasa ban samu ba……” (Komai Ummi ta zayyane mata da ya faru yanzun anan gidansu).
         “Bara muga baƙin su wuce to sai na sanar masa. Duk da dai inaji a raina ko duk shine ya tsara hakan dan mijin nan naki sai da siyasa ake iya kamasa a hannu. Ya riga ya zama mai fuska biyu inba ka saniba babu mai cewa zai iya sheɗancin da yake zubawa shi da uwarsa Umm Abubakar. Amma ki kwantar da hankalinki dan ALLAH, ALLAH yana tare damu”.
        “Shikenan Umm Muhammad ALLAH yay mana jagora. A gaishe da yaran sai na jiki”.
     Sallama sukai da ga haka zuciyar Ummi fal waswasi da saƙe-saƙe.

______

             Ido Hibbah ta buɗe a ɗan yanayin razana saboda barcin da ya figeta. Gabanta ya faɗi lokacin da idanunta ke kaiwa waje ta windown motar da aka sauke gilashi baki ɗaya. Mazaunin direban ta kalla tana haɗiyar yawu da ƙarfi saboda bushewar da maƙoshinta yayi lokaci guda. Tai saurin ɓalle murfin motar ta fito domin tabbatar ma kanta inda ya kawotan fa ba anguwarsu bane……………✍

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button