Bakar Inuwa

BAKAR INUWA 16

      Bappi ya ajiye wayar yana duban Ramadhan dake gefensa yana shan furar da Bappin kesha shima, tun wayar farko da yayi Anne ta tambayi lafiya ya mata bayani, amma duk da Ramadhan ɗin na’a wajen ko tari baiyiba, furarsa kawai yake sha yana sarrafa lap-top ɗinsa kamarma baya a wajen.
          “Ramadhan!”.
Bappi ya kirashi a hankali.
     Ɗago nutsatstsiyar fuskarsa yayi mai ƙarancin hayaniya yana kallon Bappin, kafin yace wani abu Bappi ya taresa da faɗin, “Tashi muje ka kaini TK hospital”.
        Tuni ɗan sakewar fuskar tasa ya ɓace, sai dai kuma babu damar yin gardama, dan shima Bappin ya tsuke tasa fuskar. Cikin marairaicewa ya maida dubansa ga Anne tamkar zai fasa kuka.
      “Ni miye nawa kake kallona. Koni nace ka kainin?”.
    Ɓata fuska ya sakeyi da janye idanunsa, batare da yace komaiba ya kashe lap-top ɗin ya miƙe, jacket ɗinsa baƙa mai ƙyalli dake ajiye saman kujerar gefensa ya ɗauka ya ɗora saman baƙin wandonsa da baƙar t-shirt, yanda t-shirt ɗin ta kama jikinsane yasa ƙyawunsa da yanayinsa na mutum mai tu’ammali da motsa jiki ya bayyana. Sosai sumar nan tasha gyara yau sai ƙyalli takeyi. Ɗan corridor ɗin dake hanyar bedrooms ɗin Anne ya nufa, ya buɗe wani ƙaramar drawer na glass da aka saka domin ado kawai ya ciri key batare daya duba na wace mota ya ɗauka ba. Dan duk keys ɗin motocin da suke amfani dashi anan sashen nanne wajen ajiyarsu.
     “Furar fa!?”.
Anne ta tambaya lokacin da Ramadhan ɗin ke ɗaukar p-cap ɗinsa zai ɗora saman kai, dan yasan Bappi sai yayi magana akan gashinsa.
       Hular ya gyara ta rufe masa fuska sosai, ciki-ciki yace, “Na ƙoshi”.
    A yanda yay maganar Anne tasan a ƙufule yake, dama yaya lafiyar giwa. Tunda akai masa zancen mulkin nan da aure ƴar sauran fara’ar fuskar tasa ta ɓace ɓat duk da shi ba mutumne miskili ba, maganarce dai sai ya zaɓa da wanda yay niyyar yi saboda jin kansa da yay gado gurin uwa. Gaba ɗaya a kwanaki biyun nan daga gaisuwa babu ruwansa da kowa a gidan. Gashi kuma Ramadhan yayi mugun tsanar driving a rayuwarsa, ita da Bappi ne kawai ke shigar masa hanci akan ya tuƙasu ko yanaso ko bayaso. Amma daya tuƙa mota ya gwammaci ma ya hau mashin, shiyyasa mashina ɗinsa kusan uku a gidan.
      Duk da yanda yaga bayan motar daya ɗakkoma key tayi ƙura haushi ya hanashi komawa ya canjo key. Sai Alu ya ƙwalama kira akan yazo ya fidda masa ita daga runfa. Lokacin da Bappi ke fitowa cikin jallabiya dan bai canja kayaba hula kawai ya sanyo saboda yamma ce garin yayi luf da alamar hadari. Ramadhan dake amsar motar a hannun Alu ya miƙa hannu ya buɗema Bappin gefensa, dan yasan in har shine zai tuƙasa a mota baya zama baya.
     Koda Bappi ya shigo komai baice masa ba ya ɗaura belt tamkar yanda Ramadhan ɗin ke ƙoƙarin saka nashi, dan shi ƙa’idarsa indai zaiyi tuƙi baya ƙin saka belt ɗin, dan mutum ne mai tsananin son bin doka koda ace sauran ƴan ƙasa na mata riƙon sakainar kashi.
         
               ★
  
   Tunda motar ta shigo Doctor Shamsu ya fahimci su bappi ne, sai ya zare jikinsa da ga wajen hayaniyar ya nufesu. Shine ya buɗema Bappi ƙofa ya fito, zai risina domin gaisheshi Bappi ya hana ta hanyar riƙo hannunsa. Cikin kunya da girmamawa Dr. Shamsu ya yarda suka gaisa, kafin yace, “Ranka ya daɗe sun riga sun tara mutane, ina ganin muje daga ciki sai na shigo da su”.
      Bappi baiƙi hakan ba, dan daga inda yake yana hango yanda M. Dauda da abokinsa ke zazzaga masifa ga mutane da securitys ɗin asibitin zagaye da su. Wasu na musu kallon mahaukata wasu na dariya, wasu najin daɗin abinda sukeyi na yaɓa magana ga Alhaji Hameed Taura.
      Ramadhan da baida niyyar fitowaba sai ya kwantar da kujera ma abinsa ya lumshe idanu tare da ƙara ƙarfin a.c dan garin yay luf-luf dayin dumm alamar hadarine, sai ɗan zafin ya bada yanayin jinsa a cikin jiki kawai.
        
      Da ƙyar Dr. Shamsu ya lallaɓa su M. Dauda zuwa office ɗinsa. Sai dai duk wani iya shegen da suka shigo da shi suna cin karo da fuskar kamala ta dattijon arziƙi Alhaji Hameed Harith Taura ya gudu. Cikin ɗan rawar jiki suka zube a ƙasa tun daga ƙofar office ɗin. Ɗan murmushi yay musu yana girgiza kansa. “A’a haba kutashi ku ƙaraso Please”.
      “Ranka ya daɗe nan ma ya isa”.
Suka faɗa cikin haɗa baki.
   “Bazai yuwu ku zauna anan ba, kuyi haƙuri ku ƙaraso.”
         Dole suka miƙe domin cika umarninsa. Bayan sun zauna Bappi ya tura musu ruwa da lemon da Dr. Shamsu ya ajiye masa. Suna ƙwaɗayin sha sunajin kunya, dan haka suka dai daure da ƙyar suka haɗe yawunsu na ƙwaɗayi. Hannu Alhaji Hameed ya miƙa musu, nan ma suka shiga nannoƙewa sai da yay da gaske suka yarda suka bashi nasu hannayen suka gaisa. A zukatansu sai yaba laushin hannun wannan tsoho suke, koda yake gidan kuɗine fa da kansa.
         “Alhmdllhi Doctor ya kirani yaymin bayanin komai game da zuwanku nan, kuyi haƙuri ba’a hanaku shiga gareta bane dan baku isaba, kawai dai saboda tsaro ake taka tsantsan, gashi kuma bamu da tabbacin abinda kuka faɗa ɗin…”
      “Wlhy ranka ya daɗe ni mahaifinta ne, ama ɗauka hotona a nuna mata”. M. Dauda ya faɗa cikin zillo yana katse Bappi.
     Murmushi Bappi yayi, dan shima dai yaga yanayin jini, sai dai taba data cinye M. Dauda ɗinne ya ɓadda ainahin kamanin nasa da Raudha.
     “Ai bama sai ankai ga nan ba. Yanzu bara muje ɗakin kawai”.
    Kafin ma Bappi ya miƙe su har sun fice, ya ɗan girgiza kansa yana murmushi dan dariya suke bashi. Suna abune tamkar wasu firgitattu………..✍

https://arewabooks.com/chapter?id=629a77b967809ad6daab2109

Chapter 13

BAƘAR INUWA…👇🏻

Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Please
Follow me
Share
Comments akan abinda ya shige maka duhu.

     _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_

YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form ɗin kamar haka: –

Enter your name: (Cikakken sunanki)

Enter your mail: (Email ɗinki)

Enter an username (Sunanki)

Enter your password: ( misali 12341234)

Confirm password: (misali 12341234)

Sai a taɓa Sign Up shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

Continue with Google – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

Register – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

AREWABOOKS LINK kai tsaye

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine.

MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER

+234 903 177 4742

Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button