BAKAR INUWA 6
★♣♠♣♠♣♠♣★♣♠♣♠♣♠♣★
Ummi na zaune a can inuwar mangwaro dake backyard ita kaɗai tun barin Abba sashen nata bayan ya gama shuka mata shika-shikan rashin mutuncinsa da ya saba. Lalle take sakama yatsun hannunta dan ita mace ce mai son jan lalle sosai. Har takai ta koyama Hibbah kasancewar tun tana ƴar ƙaramarta take mata itama.
Kallon wayarta da kira ya shigo tayi duk zatonta ma Hibbah ce. Batai mamakin ganin Zahidah ba, dan tasan Hibbah zata iya amfani da wayar tata wajen kiranta idan tata wayar babu kuɗi. Ɗayan hannunta tasa ta ɗauka wayar fuskarta da Murmushin tuna a yanda Autar tata ta fita cike da tsoron Abba a tare da ita.
“Autan Umminta yaya dai?”.
Ta faɗa dai-dai lokacin da take ɗora wayar akan kunnenta.
“Ummi ba ita bace nice Zahidah”.
Jin yanda muryan Zahidah ke rawa kuma a firgice ya saka Ummi ruɗewa ta shiga jera mata tambayoyi..
“Ummi akwai matsala ne wlhy, yanzu ina capteria muna waya da Hibbah ina faɗa mata ta fito class ina jiranta muci abinci sai wayan ya katse. Ina ƙoƙarin sake kiranta a zatona network ne sai ga wani course mate ɗina yazo yake sanar min ga jami’an tsaro can suna neman sister ɗina. Na tafi domin tabbatarwa kawai na iske harta shiga motarsu sun wuce da ita Ummi. Ni kuma gashi bani da no ɗin su Yaya Abubakar balle na sanar musu shine na kiraki dan ki sanar musu”.
(Hasbinallahu wa-ni’imal wakil) Ummi ta shiga mai-maitawa da sauri-sauri dan jin wani irin yuuu cikin idanunta da kanta. Cikin ƙoƙarin haɗiye tashin hankalin da take ciki ta ce, “Wani laifin ta aikata ne Zahidah?”.
“Ni dai Ummi a sanina bata aikata komaiba wlhy.”
“Shikenan bara na kira Abubakar naji idan yana kusa ko Muhammad”.
“To Ummi”. Zahidah ta faɗa tana share hawayen da suka gangaro mata akan kumatu. A kallo ɗaya zaka fahimci a matuƙar firgice take. Gashi ita kaɗai ce yau dan Hafsat batazo ba saboda ƙafarta.
Hango Yaya Ammar da ke nufota da sassarfa ya sakata tunawa da yana a cikin makarantar shima. A zabure itama ta nufosa.
“Zahidah! Ina Muhibbah?”.
Ya faɗa cikin furzar da hucin hakkin gudun da yayi dai-dai isowarsa gabanta.
Bayanin abinda ta sani da wanda taji a bakin mutane tai masa tana share hawaye. Hankalinsa ya ƙara tashi matuƙa shima. Dan duk tsokanarta bata taɓa kaiwa matakin hakaba, a yanda yaji wai ƴan sanda da manyan bindugu ya matuƙar harmutsa tunaninsa.
Babu shiri ya shiga neman no ɗin Yaya Abubakar, sai dai kuma number busy take nuna masa alamar yana waya da wani kenan ko makamancin hakan. Maida akalar kiransa yayi akan Yaya Muhammad. Bugu biyu ya ɗaga. Ko sallama bai masa ba ya shiga masa bayanin abinda ke faruwa.
Ko tari kasa yi Yaya Muhammad yay. Sai numfashinsa ne dake tafiya a sarƙe tamkar mai ciwon Asthma. Batare da ya iya furta komai ba ya yanke wayar. Kamar jira sai ga kiran Ummi ya shigo masa.
Sam baiyi tunanin taji mike faruwa ba itama. Dan haka yay ƙoƙarin saita kansa dan ganin bai tada mata hankali ba. Sai dai a yanda yaji muryarta tun a sallama ya matuƙar tada masa hankalin. A hautsine ya shiga tambayarta lafiya? Dan ko kaɗan basason tashin hankalinta.
Duk yanda Ummi taso danne damuwar dake a cikin muryarta ta kasa hakan. Cikin gwamewar numfashi ta shiga yimasa bayanin duk yanda sukayi da Zahidah.
Da sauri ya ce, “Ummi dan ALLAH ki kwantar da hankalinki, insha ALLAH zamu nemi idan take bara na nema Abubakar yanzun nan”.
Bai jira cewarta ba ya yanke wayar dan bayason shima ta fahimci rauninsa kai tsaye…………..✍