Bakar Inuwa

BAKAR INUWA 7

            Ɗakin da ke ajiye da na’urori masu ƙwaƙwalwa aka kai Hibbah. Inda suka sami mutane kusan goma sha uku a ciki. Kai tsaye wajen zama aka nuna mata alamar dama ita ake jira. Zama tai tana haɗiyar zuciya. Batason yin aikin saboda gargaɗin Yaya Abubakar. A gefe kuma batason a cutar mata da ahali akan abinda basu ji ba basu gani ba. A wani gefe na zuciyarta kuma nason yi kodan abinda mutanen suka nema yi musu jiya har ga Hafsat da ciwo.
           Waya irin ta jami’an tsaro aka ajiye a gabanta. Tare da kunna ƙaton tv irin na office ɗin data baro da shima ke a jikin bango. Hoton yayunta da rahotannin da aka shirya na karya dan tsoratar da ita suka bayyana.
    Ta sauke idanunta dake cike da ƙwalla a hankali bisa computer ɗin gabanta.
       “Ki nutsu wajen yin aikin da zai ƙuɓutar da ƴan uwanki zama criminals zuwa taurari ta sanadinki, ko kiyi sakacin yin aikin da zai dusashe haskensu da ga taurari zuwa criminals ta sanadinki.”
    Mutumin ɗazu ya faɗa cikin tabbatarwa da murya mai kaushi.
     Kai kawai ta jinjina masa tana maijin wani ɗaci a zuciyarta da taurin zuciya. Sai da tayi addu’a a cikin zuciyarta kafin ta fara aikin cike da ƙwarewa. Kasancewar ɗazun dama ta binciko a inda suke sai yanzu batasha wahala ba duk da wannan Computer ɗin nada matuƙar tsaro fiye da tasu ta makaranta.
           Da wayar gabanta ta dinga amfani wajen yin magana da jami’an da suka fita operation ɗin tana sanar musu hanyoyin da zasu bi har zuwa location ɗin da agogon data jefama masu power bike jiya yake. Hakan shike nufin tabbacin samun su inhar agogon na tare da su basu farga sun yadda ba…….

\★/★\★/★\★/★\★/★\★/★\

                 Anguwar jahje street, anguwace mai ƙarancin rashin hayaniyar jama’a kasancewar ta ɗauke da manyan gidaje na masu hannu da shuni. Ko da rana ka shigo wannan anguwa zaka sameta tsit tamkar halittun da ke a cikinta basa numfashi. Akan samu ƙarancin gittawar ababen hawa da na mutane masu tafiya a ƙafa sai dai jefi-jefi. Shima hakan tafi kasancewa a ranakun hutun ƙarshen mako ko hutun ranakun ma’aikata da kan gitta.
          Sabo da rashin sakewarsu da juna yasa bazasu iya tantance kansu ba dan rayuwa ake ta babu ruwan wani da wani. Idan kaga magana ta shiga tsakaninsu sai idan ALLAH yasa ka fito maƙwafcinka ma ya fito ai gaisuwar hello hi shikenan kowa ya shige sabgar gabansa.
           A cikin gida mai lamba 110 matasan samari ne da shekarunsu zai iya kaiwa ashirin da biyar zuwa da shida, harma mai da bakwai za’a iya samu. Gaba ɗayansu bakwai zaune suke a ƙayataccen falon gidan mai matuƙar girma da ƙawa ga mai kallo. Su dukansu kowa harkar gabansa ya ke yi. Wasu na kallon ƙwallo, wasu na daga gefe suna sarrafa wayoyin hannunsu.
Ɗaya da ga cikinsu ya nutsu wajen sarrafa waya. Sai dai a hakan hira kan shiga a tsakaninsu musam akan kallon ƙwallon da mutum huɗu suka fi maida hankali a kansa.
        Wani mahaukacin horn daya nema harmutsa kwaƙwalensu da ga gate ya sakasu miƙewa a rikice gaba ɗayansu suna ambaton Master!!. Biyu da ga ciki suka shiga tattare ledojin dattin da sukai ciye-ciye tare da gwangwanen maltina da coc.. Ɗaya ya fita a guje domin zuwa ya buɗe masa ƙofar falon da ke rufe da security.
          Buɗe ƙofar yayi dai-dai da isowarsa cikin takun ƙasaita da tabbatar da shiɗin fa ya isa. Sanye yake cikin baƙin wando jeans da baƙar t-shirt. Sai dai ya ɗora jacket baka itama a samanta batare da ya ja zip ɗinta ba. Sam ba’a ganin fuskarsa, sakamakon hular jacket ɗin dake har saman kansa, ga norse mask da baƙin google toshe da idanunsa. Ƙafarsa ma sanye take cikin baƙin takalmi.
     Cikin zafin nama da ALLAH yay masa yasa hannunsa da ke sanye cikin safar hannu ya matsar da wanda ya buɗe masa ƙofar ya shigo cikin falon.
      Hakan ya kara tabbatar musu da babu lafiya, dan kowa bai kalla a cikinsu ba ya nufi wata ƙofa a hargitse.
     Kallon juna sukayi cike da tsoro, cike da ƙarfin hali ɗaya da ga cikinsu yace, “Brothers babu lafiya fa”.
       “Tabbas babu lafiya Khalid. Akwai abinda ya saka Master a wannan yanayi…..”
     Maganar tasa ta kakare a maƙoshi saboda fitowar wanda suke kira Master. Cikin wata irin murya mai amo da nutsuwa ya fara magana da faɗa. “Ina kayan da kuka fita aiki da su jiya?”.
      A tare sukai rige-rigen nufar ɗakunan barcinsu. Babu jimawa sai gasu suna dawowa ɗaya bayan ɗaya da kayan a hannu. Na’urar bincike da ke a hannunsa ya shiga kangawa jikin kayan. Akan jakkar Habib ta tabbatar da zarginsa. Ya fisgi bag ɗin da sauri yana zazzage dukkan abubuwan da ke a ciki, sannan ya ɗaura na’urar akan kayan. Saurin daukewa yay ya sake maidawa akan jakar. ƙaramin fuskar agogo mai kama da flower dake manne a jiki ta fara kawo jar danja tana ɗaukewa. Yay saurin fisge agogon da dudu-du girmansa bai wuce girman ficika ba. Numfashi ya fusga da ƙarfi, hakama sauran yaran nasa duk sai da sukai ajiyar zuciya. Dan abinda sukaga ya cire ɗin ya tabbatar musu wani ya kafa musu tarko ne ba tare da sun farga ba.
           Batare da yace dasu komai ba ya nufi na’urorin dake acan gefen falon an katangesu da glass na ƙawa daya zamewa falon baki ɗaya ado. Cikin wata na’ura ya saka agogon, bayan kamar sakan biyar ya cire ya fito ya nufi waje. Yana fita suka shiga kakkauda duk wani kaya suna maida shi a salon da zai basu kariya dan da alama yau ta ƙwaɓe.
       Baifi mintuna uku da fitarba sai gashi ya dawo. Hanyar ƙofar da ya nufa ya sakasu binsa da sauri suma dan sun kammala kauda dukkan abinda ya kamata su kauda ɗin. A kuma dai-dai lokacin sukejin ƙarar buɗe gate ɗin gidan alamar wanda suka sami nasarar bibiyar tasu sun iso. Sun kumafi ƙyautata zaton ƴan sanda ne abokan TAKUN SAAƘAr su………….✍

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button