Bakar Inuwa

BAKAR INUWA 9

        Fitowar Hibbah da aka haɗa da jami’ai biyu zasu mata rakkiya zuwa gida yayi dai-dai da isowar Yaya Abubakar da Yaya Muhammad station ɗin. Tana ƙyalla ido a kansu ta kwasa da gudu garesu. Jikin Yaya Abubakar dake gaba ta faɗa tare da fashewa da kuka.
        Shima rungumeta yay yana mai rintse idanunsa da suka kaɗa sukai jajur. Yaya Muhammad ya ƙaraso garesu da sassarfa shima. Dafa kanta da yayine ya sata barin jikin Yaya Abubakar ta rungumeshi shima. Cikin son danne nasa ɓacin ran ya saki murmushi yana ɗagota da shafa kanta. Hannu yasa ya shiga share mata hawaye. “Kukan ya isa haka nan, ba gamu tare da ke ba”. Ya ƙare maganar da sake sakar mata murmushi mai kwantar da hankali.
       Yaya Abubakar da shima ke ƙoƙarin ganin ya shanye tasa da muwar ya ce, “Bara naje zanyi magana da su”.
     Da sauri Hibbah ta riƙo hannunsa tana girgiza kanta. Cikin sanyin da basu santa da shi ba ta ce, “Yaya karka je. Ka barsu kawai babu abinda sukai min”.
            “Karki damu, ba wani abu bane yanzu zan fito”. Yay maganar da zare hannunsa cikin nata yana shafa kanta. Kama hannunta Yaya Muhammad yay shima ya buɗe mota ya sakata, tare da ɗaukar goran ruwa ya miƙa mata. “Sha ruwa ki wanke fuskarki ina zuwa”.
    Hibbah na ƙoƙarin dakatar da shi bai jira cewarta ba ya nufi cikin station ɗin shima. Jitai kamar ta fasa ihu, dan gani take kamar shigar tasu na nufi jami’an zasu riƙesu su sanarma duniyar ƴan ta’adda ɗinne su.
         Ganin an shafe kusan mintuna a shirin tai yunƙurin bin bayansu, sai dai tana buɗe motar suna fitowa kowannensu ransa a ɓace. Ta sauke ajiyar zuciya da yin sagade tai tana kallonsu har suka ƙaraso. Yaya Muhammad ya sake kama hannunta ya sata a motar sannan ya zagaya ya shiga shima. Yayinda Yaya Abubakar ya zauna mazaunin driver.
         
      Suna fara tafiya kiran Ammar ya shigo wayar Yaya Muhammad. Kamar bazai ɗaga ba sai kuma ya ɗaga ɗin. Da ga can Ammar ya fara magana cikin ɗacin murya. “Yaya kazo gida dan ALLAH akwai matsala. Hajiya mama da Abba na nan sun taru akan Ummi harda Junaid. Nayi magana kuma ta dakatar dani. Wlhy zanma Haƙilu (Abba) dukan mutuwa sai dai Ummi ta tsinemin. Har wannan shegiyar tsohuwar ba raga mata zanba dan mahaifina ta haifa ba ni ba.”
        “Ammar!!”
Yaya Muhammad ya kirayi sunansa a tsawace jin zai yanke kiran shima jikinsa na matuƙar rawar ɓacin rai.
        Tuni Ammar ya riga ya katse kiran baima jisa ba. Yaya Abubakar da duk yaji komai ya ƙara ƙarfin gudun motar, cikin ƙanƙanin lokaci sai gasu a ƙofar gidan. Tun a waje yay fakin, gaba ɗayansu suka fita da sauri zuwa ciki. Dan tun da ga waje suna jiyo kururuwa da ihun Hajiya Mama da Momy.
         A harmutse suka iske gidan. Ammar da Junaid na kwasar uban dambe. Sai dai duk da kasancewar Junaid yaya ga Ammar hakan bai hana Ammar hayewa saman ruwan cikinsa yana duka ba tamkar ALLAH ya aikosa. Mahaifiyar Ammar ɗin da suke kira Momy taje ceton ɗanta Ammar ya bata mahangurɓa a muƙamuƙi. Tuni ta koma gefe jikinta na matuƙar rawa.
         Abba da hajiya mama kuwa tuni suna a wani lungu maƙale dan su ne Ammar ya fara fafara Junaid ɗin ya maresa. Shine faɗan ya juye a tsakaninsu. Da ga cikin lungun Hajiya Mama keta fama kwaɗa ihu da kururuwar Ammar zai kashe mata jika. Yayinda Abba ke a rikice ga tsoro, yana son zuwa ɗakko waya ya kira ƴan sanda yana tsoron fita Ammar da ya juye musu kamar wani mayunwacin zaki ya gansa ya dawo kansa.
      Ummi ce kawai akan Ammar tana ƙoƙarin janyesa tana kuka amma ta kasa, dan gaba ɗaya ya juye mata tamkar ba Ammar ɗinta ba. Ya koma ainahin sunansa na ALIYU ZAKI.
         
      Kuka Hibba ta fashe da shi ganin yanda Yaya Ammar kema Junaid dukan mutuwa. Sai jini ke fita ta hancinsa da baki amma yaƙi sakinsa. Da ƙyar Yaya Muhammad da Yaya Abubakar suka iya haɗuwa wajen ɗagasa da ga kan Junaid ɗin. A hakanma sai famar turjewa yake yana nuna Junaid cikin gargaɗi.
           “Duk iskanci da kukejin kun iya da rashin mutunci muma mun iyasa. Ba tsoronku bane yasa muke barinku kuna taka mana mahaifiya yanda kuka gadama. Son yin biyayya a gareta da ga taka mana birkin da take na barinku kawai ke dakatar damu. Amma idan har kun isa wani ya sake nuna nata ɗan yatsa a gidan nan ya gani in ban karya shi ba na tauna ƙashin. Wlhy hatta waccan annamimiyar tsohuwar bazan bari ba, sai na ida ƙille ƙafafun nata ta koma gurguwa ta gaske…….”
         Kuka sosai Ummi keyi tana kiran sunan Ammar amma yaƙi yin shiru. Su Yaya Muhammad suka turashi sashen nasu da ƙyar suma rayukansu duk a jagule.
       A dai-dai wannan lokacin ɗaya da ga cikin ƴammatan gidan ta dawo. Horn tayi mai ƙarfi kamar yanda suka saba. Da sauri mai-gadi dake maƙale yana kallon duk abinda ke faruwa da ga windown ɗakinsa shima ya fito domin buɗe mata gate ɗin. Sai dai shima har cikin ransa yaji matuƙar daɗin dukan nan da Ammar yayma Junaid. Dan duk wani cin zarfi da akema mahaifiyar su Ammar ɗin a gidan akan idonsu ne tun da ƙuruciya.
       A guje Ameera ta danno motarta cikin gidan kamar yanda ta saba. Sai dai hango su Abba akan Junaid da ke kwance kamar ya mutu ya sata saurin taka birki tamkar ba’a cikin gida ta ke ba. Fitowa tai da sauri. Ta zaro idanu sosai cikin ƙaraji na rashin tarbiyya take tambayar miya samu Junaid ɗin?.
           Abba yay saurin ɗago Junaid ɗin da numfashinsa ke fita da ƙyar yana faɗin, “Kinga maza buɗe mana motarki mu kaisa asibiti shine mafi muhimmanci yanzu. Sauran bayani ƙyaji da ga baya dan anzo gabar da yaƙin duniya na uku zai fara tashi a gidan nan.”
       Zata ƙara magana Hajiya mama ta katseta a tsawace. Baki ta murguɗa mata da yin fari da idanu sannan ta nufi motar tata Abba da mai-gadi biye da ita ɗauke da Junaid da gaba ɗaya jini yayma fuskarsa faca-faca………..✍

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button