TAKUN SAKA 41

*_Chapter Forty o…………*_WASHE GARI_*
Da asuba Hibbah ta rigashi tashi, dan cikin barci ya dinga jiyo motsinta a bayi. Tashi yay da ƙyar yana ambaton sunan ALLAH. Alhmdllhi jikin ya masa daɗi, dan magungunan da yake sha sun matuƙar taimaka masa. Koda ta fito kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta. Shima baice komai ba ya mike zuwa bayin yayo alwala. Koda ya fito shine yaja musu sallar, yana lure da
yanda Hibbah taƙi yarda ta kallesa bai nuna ya damu ba. Bayan sun idar tana ƙoƙarin miƙewa ya riƙota ya zaunar a jikinsa. Kanta ta kauda gefe tana ƙoƙarin haɗiye ƙwallar da suka ciko mata idanu. Hijjab ɗin jikinta ya cire, tare da riƙo fuskar tata cikin tafin hannunsa ya juyota garesa. “Nikam wai har yanzu ba’a huceba”. Yay maganar yana ɗaura kansa bisa goshinta”.
Duk yanda taso ƙwace fuskar tata hakan ya gagara. Dole ta nutsu waje guda, gashi tanason yin magana amma babu dama. Ta tabbatar datayita kusancin laɓɓansu zai iya sawa ya haɗu da nasa.
Fahimtar hakan da yayine ya sashi ɗaura laɓɓan nasa saman nata ya ɗan sumbata. Sai kuma ya janye goshinsa yana kallonta da ƙyau. Duk yanda yaso su haɗa ido ko tayi magana taƙi. Sarai ya fahimci borin kunyane kawai. Dan haka ya saketa yana murmushi.
Zumbur kuwa ta miƙe tabar wajen, har tana cin tuntuɓe da ƙafarsa.
“Ni dai kar amin asarar ɗan tayi na”.
Ya faɗa cike da shaƙiyanci yana binta da kallo. Cikin tunzura baki gaba ta haye gadon taja bargo ta rufe har kanta tana ƙunƙunj. Duk da dariyar dake son kufce masa dai ya danne abinsa baiyi ba. Sai ma ya miƙe shima ya hau gadon dan barci yake son ƙarayi. Hibbah data ƙudundune waje guda tai saurin buɗe idanunta a tsorace. Zata miƙe ya riƙota yana daidaita fuskarsu waje guda. Yatsansa ya ɗaura saman laɓɓanta ya shiga zagayawa dashi a hankali. Tsigar jikintane ya fara tashi amma sai ta danne taƙi nunawa.
Cikin ƙasa da murya sosai tamkar mai raɗa yace, “Mikike faɗa da banaji?”.
Hannunsa ta ɗan ture daga bakinta tana kumbura bakin kamar zatai kuka, “Ai dai ALLAH ya sani bance komai ba”.
Ganin zata juya masa baya tana maganar yay azamar tareta, laɓɓansa ya matsar gab da nata yana wani narke idanu, “Ni nasan kince ai”.
Kafin ta samu damar cewa wani abu ya rufe bakin nata, cikin shauƙin dake ɗibarsa ya shiga aika mata da sumbata a nutse data saka zuciyarta shiga tsoro harta fara tsuma. Duk da yaji a yanda jikin nata ke ɓari bai saketa ba ya cigaba da abinda yake har sai da ya tabbatar tayi laushi. Hagitsatstsun idanunsa da suka kaɗai sukai jajur ya ɗago yana kallon fuskarta, idanunta dake hawayen tsoron ya sumbata da jan nannauyar ajiyar zuciya.
“Nasan ni mai laifine a gareki ta kowacce fuska Muhibbat, sai dai inason kisani kece kika faramin laifi.”
A karon farko Hibbah ta buɗe idanunta ta kallesa, ga hawaye shaɓe-shaɓe. Sai kuma cikin sauri ta sake maidawa ta rufe, dan batason ganin idanun nan nasa da fuskar nan ta yaya Isama’il da ya saka, ga matsananciyar kunyarsa dake matuƙar cizon ranta da ɓargo. Batare da ya damu ba ya tura yatsun hanunsa cikin gashin kanta da sake matsota jikinsa. “Inason ki nutsu a yau kisan kowanene Muhammad Shuraim (Master). Asalin sunan shine Isma’il Aliyu Hikima”.
Cikin sauri Hibbah ta sake buɗe ido har yawu na sarƙe ta. Ganin ta miƙe zaune shima ya miƙe, ruwan dake a bedside ya ɗakko ya ɗora mata a baki. Babu musu tasha tana kallonsa tamkar idanunta zasu zubo a karon farko wajen kallonsa.
“Tabbas Isma’il shine sunan, kuma shine a gabanki yanzu haka da fuskar zahiri bata bogi ba Muhibbat.”
Wani irin bugawa ƙirjin Hibbah ya sakeyi. Cikin rawar jiki da son ƙin gaskatawa takai hannunta saman fuskarsa tana rumtse ido. Sake buɗe idon tai da sauri taja baya jikinta na sake ƙarfin karkarwa. “M….master kana nufin kaine Yaya Isma’il?”.
Kansa ya jinjina mata yana lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta.
“Na shiga uku ni Muhibbat wane irin rikitaccen mafarkine wannan nake a ciki?. Impossible hakan ta kasance”.
Tai maganar tana ƙoƙarin sauka a gadon. Saurin riƙota yay ta dawo jikinsa. “Shiyyasa nace ki nutsu ki saurareni”. Ya faɗa a cikin kunnenta da wata murya mai taushi tamkar bashi ba. Batare da ya bata damar sake cewa komai ba ya cigaba da maganarsa. “Sunan mahaifina Aliyu……….” tiryan-tiryan ya cigaba da bata labarinsa tamkar yanda ya bama su Ummi. Sai kuma ya ɗora da “A farkon shigata tawagar su Master an taɓa kamamu, lokacin ina farkon shiga aji shida na sakandiri. Tunda aka kawomu police station wani babban jami’i keta kallona har kallon ya gundireni naji haushi. Fahimtar hakan da yay yasashi ɗauke kai yana murmushi. Bansan yaya akai ba bayan kamar awa guda aka fiddani ni kaɗai kuma babu wani bayani. Hakan ya tsayamin a rai, daga baya kuma saina watsar na cigaba da harkar gabana.”
“Bayan na kammala jami’a na kaima wanda ya ɗauki nauyin karatuna result ɗina dan ya gani, tare da sake masa godiya, sai naci karo da jami’in nan da yayta kallona a station, abin ya ɗauremin kai, na kuma sha mamaki amma sai na danne. Yaji daɗi ya kumayi farin ciki a take anan kuma yaymin tayin aiki saboda ganin yanda nake da matuƙar ƙwazo da kaifin basira akan harkar kimiya da fasaha. Babu musu na amsa cikin farin ciki da murna dan kuwa aiki ne na jami’an tsaro. Na miƙe cikin farin ciki zan tafi ya dakatar da ni ta hanyar faɗin, (dakata yarona ai bamu gama magana ba). Komawa nai na zauna ina basa dukkan hankalina.”
“Yarona zaka zama jami’in ɗan sanda amma na sirri, dan haka zakai aiki kafaɗa da kafaɗa ne da mu ƴansanda amma a sirrance batare da kowa yasan wannan ba sai ni. Inada abubuwa masu yawa dake cimin rai da zuciya, sai dai ina matuƙar jin tsoro da shakku akan wanda zan ɗora yaymin. Wannan yasa a randa na fara ganinka a station naji a raina zaka iya. Hakan yasani komawa na biya maka kuɗin karatu dan a cikin idanunka na fahimci da gasken zaka iya. A yau zan sanar da kai wani abu, duk tsahon shekarun nan daka ɗauka kana karatu ina biye da kai, hatta shiga cikin ƴan daba da kakeyi wanda na fahimci kanada wani dalili duk ina sane da kai).”
“Nayi matuƙar razana dajin zancensa. Dan haka na miƙe ina girgiza masa kai. Saurin riƙoni yayi shima yana girgizamin nasa. cikin taushin murya kuma ya shiga lallashina. (Yarona zaka iya, ni na tabbatar zaka iya insha ALLAH. Wannan Master da kake ƙarƙashinsa ko kasan gawurtaccen ɗan ta’addane da muke fako tsahon shekaru. Sai dai a bincikenmu ya nuna yana tare da manya-manyan masu faɗa ajin da ko kamashi mukai munyi a banza zai fito kamar ko yaushe. Daga ƙarshe ma wanda ya kamasan shine zai rasa aikinsa ko rayuwarsa. Jami’anmu sun halaka da yawan gaske a dalilinsa. Sai dai a yanzu haka akwai yarona a cikin yaransa shine duk ke bani bayani game da kai, dan shima ya shiga jikinsa ne domin mana cid. Inason dan ALLAH ka sanarmin miyasa ka raɓu da shi kai?).”
“Ina ganin kima da mutuncinsa. Dan ya ƙyautata rayuwata na samu ilimi a gaɓar dana yanke ƙauna da samun hakan. Dan haka babu musu na zauna na zayyane masa koma na rasa iyayena a dalilin Master da dangin Dattijo Isma’il suka saka. Na kuma tabbatar masa da fansa zan ɗauka dan bazan bar Master ba. Har hawaye sai da yayi domin tausayina. Ya kuma tabbatarmin burina zai cika cikin sauƙi amma saina zama jami’in sirrin da yaymin tayi. Na amince a lokacin. tare da bayyana masa ainahin fuskata ta Isma’il Aliyu Hikima. Yasha amamaki kwarai da gaske, musamman da yaji cewar tun ina yaro nake ɓoye fuskata ta zahiri, bayan iyayena shine na biyu daya ganni a hakan. Hakama da yaji nike haɗa dukkan Mask ɗin wa kaina yaji daɗi ya kuma yabama fasaha ta. Domin abune daba kasafai ake samunsa anan yankunanmu ba.”