Uncategorized

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 11 to 20

Ahankali tasoma buɗe idanuwan ta tana rufewa har sanda tabuɗe gaba ɗaya idanun tana kallon rufin ɗakin, ta ɗan jima ahaka tana son tuno abinda ke faruwa kafin komi yadawo ƙwaƙwalwan ta, dasauri tazabura daga kwancen da take tatashi zaune tana kallon tsararren Palon da yagaji da haɗuwa, idanuwanta akan Nura yasauka da shima yake yashe ƙasa da alamun dai shi be dawo hayyacin sa ba, a gefe da gefen sa kuwa wasu mutane ne manya dasu su biyu sun tsaya a kansa, sai kuma tadawo da ganin ta gefen ta dasauri, nan ma wasu mutane biyun ne kusa da ita, da alama gadin su suke yi”Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.. ina ne nan?”. Ta faɗi hakan ne a fili tana jin zuciyarta na tsinkewa, don tasadakar gidan cin kai ne aka kawo su

“Gidana ne”.

Taji maganar ya doki kunnin ta, dasauri tajuyo tana wurwurga idanu, nan kuwa idanun ta yasauka akan sa, yana zaune saman kujera ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya yana sakin murmushi, daga shi sai farar singlate da gajeren wando me ruwan ƙwai da iyakacin sa gwiwa, gefen sa kuma da akwai mutum ɗaya dake tsaye yana gadinsa, wani irin bugawa zuciyarta tayi kamar zatayi tsalle tafaso cikin ƙirjinta, take wani irin tsoro yashige ta har batasan sanda tawaro idanun ta waje ba tana kallon shi, still yana murmushi yace

“Barka da zuwa turaka ta Amarya ta, yau dai gaki cikin gidana abinda nadaɗe ina fata da buri kenan”.

Ahankali yatashi yanufo ta har zuwa gaban ta kafin yadakata yana ƙare mata kallo, sai kuma yasoma zagayeta yana tafa hannun sa, wanda duk taku ɗaya da yake yi tana ji ne kamar yana tafiya da bugun numfashin ta, sai da yagama zagaye ta sannan yazuƙuna agaban ta yana kallon cikin idanun ta da tatsayar akan sa ko motsin kirki takasa yi, sosai ganin shi yayi tsananin firgita ta har tana jin komi na jikinta ya dena aiki, murmushi yasaki yana faɗin

“Yau dai na baki mamaki ko? Baki zatan zaki iya zuwa hannun Haris cikin sauƙi ba?”

Sai kuma yasaki dariya yaci gaba

“Dama nace miki zan kafa tarihi cikin rayuwan ki, zanyi miki abinda har kimutu bazaki taɓa mantawa dani ba, to ga ranan tazo, yau duk zan huce wahalan da kika bani, kin bani wahala sosai Babyna”.

Yaƙarike maganar yana kai hannun sa saman fuskarta yashafo gefen face ɗinta, kafin yacire hannun dasauri yana zuba murmushi

“Ohh kince in dena taɓa ki ko?” Uhmmm saboda na taɓaki kika cire hannu kika wanka min mari ko? To yau kuma bari inga wani hukunci zaki min, kin san me?”

Yatambaye ta yana matso da fuskar sa kusa da nata, sai lokacin tasami daman motsa jikin ta, dasauri taja baya tana girgiza mishi kai, nan da nan hawaye suka cika idanun ta suka soma zubowa, cikin rawan murya tace

“Don Allah.. don Allah na roƙe ƙa kayafe min, wlh bazan sake ba dan Allah kayi haƙuri”.

Dariya yakece dashi yana zama dirshan a ƙasa yace

“Da wuri haka? Taya kike tunanin mayunwacin zakin da yadaɗe yana farautan abincin da zai ci, yau ya samu sai kuma yasaki abincin yatafi?” Sam wannan ba me yiwuwa bane, yau sai nacika Burina akan ki Halwa, yau zan yi maganin ishin ruwan da nadaɗe ina fama dashi cikin raina, yau zan cire duk wata sha’awan ki dake damuna”.

Riƙo hannun ta yayi yana son jawo ta jikinsa, tayi saurin ja baya tayunƙura tatashi aguje tanufi wajen Nura da har yanzu yana nan kwance, girgiza shi tasoma yi cikin kuka tana faɗin

“Yaya Nura dan Allah katashi, katashi kataimake ni dan Allah Yaya”.

Dariya Haris yakwashe dashi, dai-dai lokacin da Nura yabuɗe idanu yana jin kukan Halwa yayi saurin zabura yana kallon ta, saurin shigewa jikinsa tayi tana faɗin

“Dan Allah yaya kataimake ni zai raba ni da mutuncina, dan Allah yaya karka bari yacin ma burin sa kataimake ni”.

Tasake fashewa da kuka har da su majina, gaba ɗaya duk tagama tsorata, shima sake riƙo ta yayi yace

“Kiyi shiru Halwa babu abinda zasuyi miki kinji, idan har ina raye babu abinda zai same ki kidena kuka”.

Muryan Haris ne yacika wurin

“Kai kuriƙe min shi da Allah”.

Ai kuwa nan da nan mutanen nan gaba ɗaya sukayo kan su suka damƙo Nura suka rirriƙe shi, shi kuma Haris yafinciko Halwa dake ta faman rusa kuka kamar ranta zai fita, sai roƙon sa take yi tana faɗin

“Don Allah don girman Allah kaji tausayina karka raba ni da mutuncina, wayyo Allah don Allah kayi haƙuri kataimaki rayuwata wlh ni marainiya ce”.

Dariya yake yi yana jan ta yanufi wani ɗaki da ita, Nura kuwa sai son ƙwacewa yake yi yana faɗin

“A’a dan Allah karkayi kaƙyale ta, dan Allah kasake ta”.

Garam haka yaji ƙaran kulle ƙofa da Haris yayi, runtse idanuwan sa yayi yana jin wasu hawaye na kwaranya a idanun sa, tsananin tausayin ƙanwar sa ce yakama shi

“Meyasa?”

Yafaɗi hakan a fili yana sake runtse idanun sa da ƙarfi jin ihun ta dake shiga kunnin sa

…… …… ……. …….. ….

Tana zaune saman gado ta ƙudundune jikinta cikin hijabin ta, ta haɗa kai da gwiwa tana wani irin kuka na fitan hankali, kuka take yi sosai tana sake matse kanta da ƙafafunta waje ɗaya, ji take yi ina ma Allah yaɗauki ran ta a yau ɗin, ko kaɗan bata fatan tasake minti ɗaya cikin duniyar nan

Buɗe ƙofan ɗakin akayi, Nura ne yashigo idanuwan sa ƙyarr akan ta, ahankali yasoma takowa zuwa wajen ta yana jin kukan ta na shiga masa har cikin ƙwaƙwalwa, sosai kukan nata ke taɓa masa zuciya, koda ya isa hannu yasaka yadafa kafaɗan ta, sai taɗago dasauri tana kallon sa da idanuwanta da suka gama rinewa sukayi jawur sai tsiyayan hawaye suke yi, dasauri tasaka hannu biyu tariƙo ƙafafunsa tatusa kanta ajikin sa tana sake fashewa da wani irin kuka me tsuma ran me sauraro, ahankali yaɗaura hannun sa saman kan ta zuciyarsa cike fal da tausayin ta, so yake yi yararrashe ta amma ko kaɗan yakasa buɗe baki, be san da wani kalma zai fara ba, ita kuwa sake tusa kanta take yi cikin kuka da ba’a jin muryan ta sosai tace

“Yaya.. Yaya ya cuce Ni, ya cuce ni Yaya ya gama da rayuwata, ya raba ni da martaba na na ɗiya mace, yaya ya gama dani wlh ya gama dani, wayyo Allana nashiga uku na lalace”.

Kuka tasake kecewa dashi tana buga kanta saman ƙafafunsa, dasauri yariƙe ta yana tallabo fuskarta yace

“Ki dena kuka Halwa, kidena kuka dan Allah, kukan ki na taɓa min zuciyata, dan Allah kiyi shiru kitashi mutafi kinji”.

Girgiza kan ta tasoma yi cikin kuka tace

“Yaya ina zani? Ina zani da wannan abun kunyan? Ina kake so naje yaya? Dan Allah yaya katafi kabar ni anan, katafi kabar ni zan kashe kaina ne, bani da sauran wani farin ciki cikin rayuwan nan, wlh Yaya mutuwa zanyi, zuciyata zata buga, dan Allah yaya kakashe ni nahuta..”

Saurin ɗaura hannun sa saman bakin ta yayi yana kallon ta yace

“Ki nutsu Halwa dan Allah, kinsan me kike faɗa kuwa? Ni Yayan ki ne kuma zan rufa miki asiri, babu wanda zai sani wlh har Mama, nayi miki alƙawari kuma zan aure ki, nasan abinda kike tunani kenan, Halwa babu wanda zai ji kitashi mutafi gida dan Allah”.

Daƙyar yalallaɓa ta tamiƙe, yana riƙe da ita suka fito palow da babu kowa ciki, ɗaukan mata takalmanta yayi yace “tasanya” babu musu tasaka har lokacin hawaye take zubar wa, fitowa suka yi cikin gidan, wajajen babu wasu gidaje da yawa, don haka sai da sukayi tafiya sosai sannan suka kawo bakin titi, Halwa bata iya tafiya sai da taimakon Nura, gaba ɗaya ajikin sa take ya rungume ta ahaka suke tafiya, basu jima da tsayuwa ba suka sami napep suka hau, a ƙofar gida yasauke su suka fito suka shiga gidan, a cikin zaure Nura yadakata yana kallon ta yace

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button