BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 11 to 20

Gaba ɗaya sukayi dariya, yayinda shi Khalil ɗin murmushi kawai yayi yana shafa kan sa
Hakima tace “Abida ɗauko mishi Aamir”.
“Tom Aunty”.
Miƙewa tayi tawuce ciki, ita ma Hakima tashi tsaye tayi tana faɗin
“Bari nakawo maka abin motsa baki Mijin”.
Khalil yace “No kibar sa kawai na hutar she ki”.
Sameer yace “waɗannan ledojin fa? Menene aciki kakawo mana?”.
“Shopping ɗin My Son ne”.
Hakima tace “to mun gode”.
Lokacin Abida tafito riƙe da Aamir a hannu takawo mishi, hannu yasaka ya amsa wanda har hannun su yana gogan juna, shi be ma lura ba yaron kawai ya’amsa, yayinda ita kuma Abida taji wani iri ajikin ta hakan yasaka tasaki murmushi tana jin farin ciki, yau rana ta farko jikin mafi soyuwa a cikin zuciyarta ya haɗu da nata
Bayan yagama ganin yaron ma sai tamiƙo hannu don yaba ta, but sai yamiƙe yaje yamiƙa ma Hakima yana faɗin
“To ni tafiya zan yi, sai kuma na sake kewayo wa”.
“Da wuri haka?” Cewar Hakima bayan ta amsa yaron
Amsa mata kawai yayi ataƙaice, daga nan suka yi sallama suka fito tare da Sameer, sun kai wajen mintuna 30 atsaye wajen motan Khalil suna tattaunawa kana yashiga motan sa yatafi.
Yana tafiya a cikin motan sa ya kawo anguwan su, zai sauka kan titi yaji Motan tayi faci sakamakon taka ƙusa da tayi, tsaki yaja yana ɗan murza hannun sa a sitiyarin motan, yajingina kan sa jikin kujeran yana kallon saman motan, tsawon mintuna yana nan ahaka kafin yaji hon a bayan sa, hakan yasaka yaɗago kan sa yana kallon motan dake bayan sa ta mirror, siririn tsaki yaja yana mayar da kan sa yalumshe ido, motan ce tazo dai-dai setting shi kana tazuge glass ɗin motan tana kallon shi
“Kana neman taimako ne?” Tafaɗi hakan cike da sanyin murya
Ɗago kan sa yayi yakalle ta, ita ce dai budurwan da sukayi karo kwanaki kuma yaganta cikin t.v, sai yagyaɗa mata kai a hankali still yana kallon ta, murmushi tayi masa don ita tariga da tagane sa hakan yasaka tatsaya
“Ok why not kazo narage maka hanya in babu damuwa fa”.
Murmushi yayi mata kana yafito daga motan yarufe, sai da yaciro wayan sa yayi ɗan gajeren text yatura kafin yanufi motan nata yashiga, taja suka tafi.
_Ku ƙara yawan Comments plzzzzzzz_ ????????????
[9/17/2020, 11:04 AM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
“`NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.“`
_Wannan shafin naku ne duk wani masoya littafin Brr. Ibarhim Khalil, ku ji daɗin ku_????????????????????????
.
*CHAPTER 22*
“Anan zaki sauke ni”. Yafaɗi hakan yana nuna mata setting gidan sa
“Laa kace kusa da juna muke ma”. Tace hakan lokacin da tatsayar da motan
Kallon ta yayi yace
“Really?”
Murmushi tayi itama tana kallon shi tagyaɗa masa kai
“But ban taɓa ganin ki ba ai? Kuma ina yawan ganin wani matashin saurayi yana fitowa gidan”.
“Eh ai ni bana ƙasan ne, ina can Maleysia ina karatu, sai kwanan nan nadawo”.
Gyaɗa kan sa yayi kana yace
“Ok thanks for your help me”.
“Babu damuwa, yiwa kai ne ai”.
Sai kuma tamiƙo mishi hannu still da murmushi a face ɗin ta tace
“Zamu iya zama friends?”
Kallon hannun nata yayi sai kuma yakalle ta, sannan yagyaɗa mata kai batare da yamiƙa mata hannun ba, janye hannun nata tayi tana yarfe shi tace
“Oh sorry” nayi tunanin ko maleysia muke”. Tafaɗi maganar tana waro idanu
Hakan yasaka shi murmushi batare da yace komi ba, yabuɗe motan zai fita
“Aff baka sanar dani sunan ka ba?” But ni sunana Kausar Ali Aliyu, and You?”
Tafaɗi maganar tana ƙure shi da idanu
“BRR. IBRAHIM KHALIL”. Yayi maganar ataƙaice shima yana kallon ta
“Wowwww! Nice Name, zan ji daɗin abota da kai kenan coz ni ƴar Jarida ce”.
Cike da ƙosawa da surutun ta yasaka ƙafarsa awaje zai fice still tasake faɗin
“Am baka ji ba?”
Yajuyo yana kallon ta fuska a haɗe tare da nuna gajiyawar sa, ita kuma sai tayi murmushi tace
“Sorry na takura ka, dama zance ne kagaishe min da Madam kafin nashigo”.
“Wa yace miki ina da mata?”
Yafaɗi maganar yana ficewa gaba ɗaya yataka yatafi batare da yajira amsar ta ba, ita kam babu abinda take yi sai murmushi, sosai Guy ɗin yaburge ta, ko kaɗan bashi da rawan kai irin samarin zamanin nan, sai da taga shigewan sa sannan ta tada motan tanufi bakin Gate ɗin gidan su tadanna hon da ƙarfi.
Shi kuma daga shigan sa gidan yamiƙa ma Gate Man keeys ɗin motan sa in Drever yazo yabashi, sannan yashige cikin gida, bayan yayi wanka ya kintsa cikin ƙananan kaya yasake fitowa yanufi masallaci, sallan asar yayi yadawo yazauna nan parlour yana danne-dannen waya, tsawon 1 hour yana wajen kafin yamiƙe yanufi kichen, Coffee yahaɗa yafito yazauna yakunna t.v yasanja channel zuwa MBC Action, abinda yake so kuwa ake yi wato wrestling, haka yakafa idanun sa akan kallon yana yi yana spping Coffee ɗin, sai da aka gama yamiƙe yanufi kichen ya ajiye cup ɗin yashiga ɗaki, ahankali yabuɗe ɗakin da yake aikin sa yazauna kan kujera, yajanyo Lapton ɗin sa yasoma aiki.
……… …….. …….. …..
Asalin Alhaji Abdurra’uf Abdullahi da Hajiya Hajara fulani ne kuma mazauna garin Katsina, Alhaji Abdurra’uf wato Dad shi irin baƙaƙen Fulanin nan ne na daji masu yawo wannan garin zuwa wancan garin, yayinda Hajiya Hajara wato Mom ita kuma irin fararen nan ne waɗanda kallo ɗaya kayi musu zaka gane su ɗin Fulani ne, Babban Family ne dasu, lokacin da su Dad suka zo Garin Katsina dashi da iyayen shi Mahaifin Mom ne yabasu mazauni a nan gidan su, zuwan sa gidan ne kuma yasoma karatu har matakin degree, da sannu da sannu suka saba da ƴan gidan har suka zama tamkar Family ɗaya, kuma alokacin ne Soyayya me ƙarfin gaske yashiga tsakanin Dad da Mom har suka yi aure, Allah ya albarkace su da yara biyu duk ka Maza Sameer da Ibrahim Khalil, kuma daga kan su basu sake haihuwa ba.
Rayuwan Sameer da Ibrahim Khalil sun yi shi ne cikin gata da ƙaunar iyayen su har zuwa matakin da suka girma, kuma sun yi karatun su ne a ƙasan Gamerny har zuwa sanda suka gama suka dawo, shi Sameer ya karanci Doctoring ne fannin ƙashi, shi kuma Ibrahim Khalil ya karanci BARRISTER
A tare Sameer da Khalil suka ƙera gidan su, sai dai ba anguwa ɗaya bane, Lokacin da Sameer ɗin yayi aure shima Khalil yace “bazai zauna a gidan su ba” shine yakoma sabon gidan shi, shekaru kusan biyu kenan da faruwan hakan.
Wannan shine taƙaitaccen tarihin su.
***** ****** ******
*TWO WEEKS AGO*
Da dare wajen ƙarfe 09:00pm. Khalil ne zaune a cikin Garden ɗin gidan sa, gaba ɗaya wajen haske ne yamamaye wajen tamkar rana don baza kace dare ne ba, yana sanye cikin wasu kaya riga da wando three qweater tamkar na sanyi, red colour ne irin dack ɗin nan, sun bala’in yin masa kyau sosai, kan sa babu hula sai gashin sa da iska ke ta kaɗawa, gaban sa kuma ɗan ƙaramin table ne ya ɗaura Lapton ɗin sa akai, gefe ɗaya kuma glass cup ne da Fruits a cikin plate, aiki yake yi time to time kuma yana ɗan kurɓan Black tea ɗin, wayan sa dake ajiye ne tasoma ringing yaɗan tsayar da aikin yakalli wayan, ganin sunan Dad ya fito raɗo-raɗo a screan ɗin yasanya shi saurin ɗauka yana peacking call ɗin tare da karawa a kunne