Uncategorized

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 11 to 20

“Hello Dad.. au assalamu alaikum”.

Murmushin Dad ɗin ne yabayyana cikin wayan kafin yace

“Kai dai baza ka dena halin nan naka ba ko?”

“Sorry Dad na manta ne, but ai na gyara ko?” Yayi maganar a shagwaɓe

Still Dad murmusawa yayi yace

“Auta kenan, Mom ɗin ka tariga ta gama ɓata ka, kana yin abu sai kace ƙaramin yaro”.

Murmushi Khalil yayi yana shafa kan sa yace

“Dad ai ku kaɗai nake ma wa, coz a wajen ku ni har yanzu yaro ne”.

Dad yace “to gobe da safe kafin kawuce office kabiyo gida ina neman ka”.

“Dad lafiya kuwa?”

“Lafiya lau My Son, sai dai in ka zo zaka ji, kar kuma kace min ka manta kashanya ni jiran ka”.

“Tom Dad, insha Allahu zan zo”. Khalil ɗin yafaɗa cike da girmama wa

Daga nan sallama suka yi Khalil ya’ajiye wayan sa yaci gaba da aikin sa.

[9/17/2020, 7:20 PM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*

                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*

_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuƊahirah*????

         *F.W.A????/*

“`ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH“`

_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._

*SADAUKARWA*

_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*

“`NAFEESAT

LABARIN DEEBIZAH

JARUMAI

RAYUWATA

NUSNIM

BUTULCI

SO MAI ZAFI.“`

.

     *CHAPTER 23*

*TOMORROW MORNING*

Khalil ne zaune a parlour’n mahaifin nashi yana sauraron abinda yake faɗa mishi

“Ibrahim har yanzu dai bakasan zurun ba ko? Tun yaushe nayi maka maganar aure but har yanzu shiru babu wani motsi da kake yi”.

Ɗago kan sa yayi yana kallon Mahaifin nashi, be yi tunanin wannan maganar ce tasaka yakira shi ba, kuma ko kaɗan be shirya ma hakan ba

“Ina jin ka tunda ka bari sai na tambaye ka, yanzu kasanar dani wacce yarinya ce kake so don mugaggauta nema maka auren ta?”

Shiru Khalil yayi yana sad da kai ƙasa

“Kayi shiru kuma?” Dad yatambaye sa yana kallon sa

“Uhm Dad ni har yanzu ban sami wacce nake ƙauna ba”.

“Ohho nagane me kake nufi Ibrahim”.

Cewar Dad yana kaɗa kan sa, sannan yaci gaba da cewa

“But nasan maganin ka tunda naga kamar har yanzu baka yi hankali ba, tun yaushe muke wannan maganar da kai amma dayake baka ɗau maganar ta wa da wata muhimmanci ba shine ka shashantar dashi, yanzu gashi har Sameer yana da yaro kai kazauna kana son kazama tuzuru, to na baka nan da lokacin da zaku gama wannan shari’an, katabbatar ka sami matar aure idan ba haka ba ni da kai ne, kana ji na?”

Dad ɗin yaƙarike maganar yana riƙe kunnen sa tare da kallon sa

Ɗan turo baki gaba yayi kana yagyaɗa masa kai

“To tashi katafi, Allah yamaka albarka”.

Ciki-ciki ya’amsa yamiƙe yafita daga parlour’n, girgiza kan sa Dad yayi yana ɗaukan Jaridan da yake karantawa yace

“Wannan yaron in ba haka nayi maka ba, to naga alaman ba auren ne a gaban ka ba, in ba ma rashin wayau ba ya zauna har War haka be yi aure ba”.

Shi kam Khalil daga fitan shi ɗakin Mom yashige, tana zaune a gefen gado tana gyara drowan ta data hargitsa tana neman sarƙan da zata saka, yashigo fuska a turɓune hannun sa cikin aljihu, ɗago kai tayi tana kallon sa, sai da takaranci yanayin sa kafin tace

“Yah ya Me yafaru ne? Me Dad ɗin naka yafaɗamaka naga fuskar ka ta sauya?”

Ahankali yatako yazo kusa da ita yazauna kafin yasoma magana ciki-ciki

“Wai Dad ya bani nan da bayan gama Shari’a na da Alhaji Mubarak in fito da mata, sai kace neman matan sauƙi ne dashi”.

Murmushi Mom tayi tana riƙo hannun sa ɗaya da yaciro su daga aljihu yaɗaura saman cinyoyin sa yadunƙule su

“Haba My Son ya zaka ga laifin Dad ɗin ku? Ai ni inaga ya baka lokaci sosai tunda ba yau yasaba maka maganar ba?”

Kallon ta yayi yace

“Mom kwanaki ne fa suka rage? Meyasa bazai ƙara min zuwa nest year ba?”

Hannu taɗaura a saman kan shi tana shafa baƙin gashin sa da yasha gyara yakwanta luf gunun sha’awa tace

“Wai to menene na tada hankalin ka ne Son? inace Kai ɗin me farin jinin ƴan mata ne, duk wacce kazaɓo acikin matan da suke son ka da gudu zata aure ka, ko acikin Family ne sai kazaɓa ɗaya kaga hakan ma sai yaƙara mana ƙarfin Zumunci, don ban faɗa maka bane kwanaki ma Hajja Mero tazo har nan, takawo min maganar ƴar ta Shukra, me zai hana a haɗa auren ku tare, kaga in ka amince kawai sai in Kira ta in sanar da ita, cikin lokaci ƙanƙani sai ayi komi a gama ko ba haka ba?”

Kwaɓe fuska Khalil yayi yace

“Wai menene haka Mom, ya na kawo miki magana don ki rarrashi Dad yaƙara min time kuma kike mayar da hannun agogo baya? Ni in rasa ma waɗanda zan aura sai yaran nan da basu da kunya, kullum idanun su a tsatstsaye kamar zasu cinye mutum, ina Allah yakyau wlh”. Yaƙarike maganar kamar yaga abin ƙyama

Dariya Mom tayi tace

“Ban da abin Auta to menene laifin su? Kuma menene laifin wanda ke son ka, in ma kana tunanin sun yi maka yara ne ai naga hakan kuka fi so yaran zamani, kuma sun fi daɗin zama ai, zaka ji daɗin zama dasu wlh”.

“To ni Mom bance miki Ina son yara ko manya ba, Ni kawai har yanzu ban ga wacce nake ƙauna bane, and Mom kuma ki dena maganar yaran nan ma kar suji su ce zasu raina ni”.

Mom tace “to shikenan na daina Autana, yanzu dai katabbatar ka samo matar da zaka iya zama da ita tun kafin Dad yazaɓo maka”.

Marairaice fuska yayi yana faɗin

“Yanzu Mom baza ki roƙe sa ba?”

“Kasan halin Dad ɗin ka, in yariga yaba ma mutum dama kasan bazai saurare shi ba, don haka kawai kayi abinda yace maka, but insha Allahu dai zan yi masa magana yaƙara maka lokacin yanda zaka samo min suruka me kyau da hankali kamar kai, wanda take ƙaunar ɗana kuma takula min dashi sosai”.

Murmushi Khalil yayi yace

“Mom kenan, to amma dai bari ince ameen”.

mom dariya tayi tana jan kumatun sa tace

“Ja’iri kawai, kana so kana kai wa kasuwa ko?”.

Shima dariya yayi kawai yana sosa kan shi

“To tashi kaje kar kayi late da yawa, kaga har 08:00am. Ta kusa”.

“Ok Mom”.

Sai da yayi mata peck a cheeks ɗin ta kafin yamiƙe yayi mata sallama yafice, har yakusa isa ƙofar da zai fita daga Parlour Nazeefa tafito daga kichen riƙe da plate a hannun ta, tana hango shi takira sunan shi

“Yaya”.

Har yariƙe handle ɗin ƙofan yajuyo yana kallon ta, saurin ɗauke kan ta tayi daga kan shi ganin kallon da yake mata, ita kan ta batasan me zatace mishi ba takira shi, sai dai kuma bataso yatafi batare da ya ganta ba, ko da magana ce yahaɗa su

“Ina kwana Yaya”. Tace dashi tana ɗago kan ta takalle shi

“Lafiya, ya jiki?”

“Alhamdulillah Yaya”.

Fita kawai yayi batare da yasake furta ko kalma ɗaya ba, ita kam murmushi tasaki tana jin daɗi a ranta, juyawa tayi tanufi ɗakin ta.

Lokacin da ya’isa yayi parcking yafito, ahankali yake tafiya har ya’isa office ɗin sa, har yakama handle ɗin ƙofan zai murɗa sai yakalli setting office ɗin Billy dake rufe, taɓe bakin shi yayi kawai yashige office ɗin sa yamayar da ƙofa yarufe, ahankali ya’isa jikin window yana saka hannu ya yaye cooten ɗin, gyara tsayuwan sa yayi yasanya hannayen sa cikin aljihu yana ƙure waje da idanu, a zahiri titi yake kallo but a baɗini tunanin mafita yake yi, tsawon mintuna yana wajen kafin yataka yanufi kujera yazauna, buɗe computer’n sa yayi, sai kuma yadunƙule hannun sa biyu yaɗaura a haɓar sa yaci gaba da tunanin sa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button