BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 11 to 20

Nocking Brr. Tahir yayi yashigo, har yazauna Brr. Khalil be san ya zauna ba, sai da yakaɗa masa hannun sa a setting face ɗin sa tukun yaƙyafta idanu yana kallon shi
“Wai tunanin me kake yi ne har nashigo baka sani ba?”
Ajiyan zuciya Brr. Khalil yayi yana gyara zaman sa yace
“Wlh Dad ne yake son tada min da hankali”.
“Me yafaru?” Brr. Tahir yatambaye sa
“Wai cewa yayi nan da lokacin da zamu ƙarƙare Shari’a nafito da matar da zan aura, ko wa yace mishi na damu da auren yanzu, kawai zai jagula min lissafi wlh”.
Dariya Brr. Tahir yayi kana yace
“Wlh kana bani mamaki Ib, wani lokacin har tunani nake yi ko dai ba lafiyanka ƙalau ba, ni a ganina kai kakeso katakura kan ka but ban ga aibun Dad anan ba”.
“To me kake nufi kenan?” Khalil ɗin yatambaye sa yana ɗaure fuska
“No babu komi, but ni dai shawaran da zan baka kafitar da wata cikin matan da suke ƙaunar ka, ko da kai ba ka ƙaunar ta”.
Khalil yace “kana nufin kenan in yi auren rashin ƙauna?”
“Eh mana tunda har yanzu baka sami wacce tayi maka ba duk acikin matan da suke son ka, ba mamaki kai irin mazan nan ne da basu gane meye so sai lokacin da suka auri matar, sannan alokacin zasu gane sun faɗa tafkin ƙauna”.
Shiru Khalil yayi yana tunani
Brr. Tahir yace “kar ka matsa ma kanka Ib, me zai hana ka amince wa Billy, tunda ita kaɗai naga alaman zatafi dacewa da kai, kuma kai kan ka sheda ne yanda take matuƙar ƙaunar ka, zata iya yin komi sabida kai, don haka kawai kaba ma zuciyar ka dama takoyi son ta kafin zuwan lokacin, idan har kaji zuciyar ka bata kwanta da ita ba zaka iya sauya wa”.
Still dai shiru Khalil yayi yana nazarin maganganun Brr. Tahir ɗin, kuma daga baya sai yace
“Shikenan zan yi tunani akai”.
“Ok”.
Daga nan tattauna wa sukaci gaba da yi kafin Brr. Tahir yatafi yabar shi, shi kuma yaci gaba da aiki har zuwa lokacin tashin shi, ahankali yamiƙe cike da gajiya yatattara kayan sa yafice, a hanya suka haɗu da Brr. Tahir har suka ƙarisa wajen motan su
Brr. Tahir yace “yau baka tambayi mutumiyar ka ba? Kuma kana gani yau ɗin baka ganta ba”.
Ɗan taɓe fuska kawai Khalil yayi yabuɗe motan sa yana shirin shiga, riƙo murfin motan Brr. Tahir yayi yace
“Kenan baza ka tambaya ba ko?”
“To tunda kayi ninyan faɗa min menene kuma sai na tambaya?” Khalil ɗin yafaɗa yana tsare shi da idanu
Murmushi Brr. Tahir ɗin yayi yace
“Gaskiya baka da dama Abokina, in ba ni ba babu wanda zai iya da halinka”.
Harara Khalil yayi masa kamar wani mace yace
“Tunda gani me baƙin hali ko? Dole kace babu wanda zai iya dani”.
Dariya yayi yana rufe bakin sa yace
“Rufa min asiri don Allah wasa nake maka, but seriously Billy ɗin ka bata da lafiya fa, yanzu nima nake ji wajen Brr. Kuma”.
Wani irin kallo Khalil yayi masa, be ce komi ba yajanye murfin motan sa yarufe, leƙo da kai Brr. Tahir yayi yace
“Bakace komi ba zaka tafi?”
“Me kake so nace maka Umhm?” Khalil ɗin yafaɗa yana ma Motan keey
“Muje mu gaishe ta mana, kaga daga nan sai kashigar da kanka ka gane ai”. Brr. Tahir yace hakan yana dariya ƙasa-ƙasa
Gajeran tsaki yayi tare da jan motan sa yayi gaba, shima dai Brr. Tahir ɗin motan sa yanufa yashiga yana ci gaba da dariya tare da girgiza kan sa.
[9/18/2020, 9:47 AM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
“`NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.“`
.
*CHAPTER 24*
Lokacin da ya’isa gida yayi parcking motan sa, sai da yayi kusan mintuna 5 kafin yabuɗe motan yafito, ahankali yake takawa har yashiga cikin gidan, akan sofa yazube yana kwantar da kan sa cike da gajiya, dafe goshin sa dake ɗan sara masa yayi yana lumshe kyawawan idanun sa, few minutes ago yacire hannun yana tashi tsaye yanufi ɗaki, koda yashiga wanka yasoma yi sabida yaji ƙarfin jikin sa, don sosai yake jin sa kamar an mishi dukan tsiya, bayan ya shirya cikin brown ɗin jallabiya da Three qweater sai yafito parlour yanufi kichen kai tsaye, shiru yayi yana tunanin abinda zai dafa, don sosai yagaji da cin indome, kuma so yake yaci abu me ɗan nauyi coz yunwan dake ƙwaƙulan sa, tea yafara haɗawa yazauna nan kichen ɗin yashanye cikin ƙanƙanin lokaci, kana yasoma girka makaroni, shi ba wani ma’abocin iya girki bane don be taɓa yi ba in banda indome da yake dafa wa, but haka dai yayi karanbanin sa yasoma ƙoƙarin girka wa, sai da yaɗaura tukunya a wuta sannan yakurma ruwa rabin tukunyan, yana soma zafi yaɗauko makoroni biyu yasake, don yana son yagirka ne har dare yahuta da ɗame-ɗame, bayan ya sake ne sai yaɗauko Maggi yazuba sannan yaɗauko kayan miya, blanda yaɗauko yasoma yunƙurin blanding ɗin sa, lokacin duk zufa ya ishe shi hakan yasaka yatashi yafice, rigan jikin sa yacire yajefa saman sofa, yadawo daga shi sai singlate ajikin sa yasoma blanding kayan miyan, bayan ya gama duk yasake cikin tukunyan, yazauna nan yana jiran yanuna, gaba ɗaya ya manta da cewa ko mai be zuba ba, sai da yabuɗe yaga yana ta zaɓarɓaka yatuna ai be zuba mai ba, ɗauko wa yayi yadiddila yamayar yaci gaba da zama, sai da yabashi good 30min kafin yabuɗe, lokacin tuni ya nuna sai dai ruwa da yayi yawa hakan yasaka yacaɓe, but be damu ba yaɗauko plate yaɗiba yarufe sauran, ɗauka yayi yafito yanufi saman dainnig ya’ajiye, sai yaje yaɗauko Faro water da kwalin Juice yadawo yazauna, spoon yaɗauka yana kallon abincin, kamar baya son ci sai kuma yasaka spoon ɗin yaɗiba yakai bakin sa, taunan farko yadakata yana taɓe baki, ahankali kuma yaci gaba da taunawa har yahaɗiye, kana yasoma tsakalan abincin kaɗan-kaɗan yana ci, ko kaɗan babu daɗi but yakasa dena ci sabida yunwan da yake ji, yayi dana sanin dafa wa, da tun farko yayi indome’n sa da tuni yacinye lafiya lau duk da ba wani iyawa yayi ba, but yafi wannan jagwalgwalon, sai da yaji cikin sa yasoma murɗa masa yana mishi ciwo kafin yamiƙe yaɗau plate ɗin yakai kichen tare da sake sauran cikin tukunya
Parlour yadawo yazauna yana ɗaukan wayan sa dake ajiye yasoma latsawa, ahankali yatsai da abinda yake yi yana nazarin abinda yake son aikata wa, tsawon minti 3 kafin yaci gaba da latsawa sannan yakara a kunne
“Assalamu alaikum”.
Jin muryan ta a cikin kunnen sa yasaka shi lumshe idanun sa yana gyara zaman sa tare da ɗaura kan sa saman kujeran
“Wa’asalaikis Salam”. Ya’amsa mata cikin cool voice ɗin sa me daɗin sauraro
Shiru ne yabiyo bayan amsa sallaman nasa, domin ita a fannin ta mamaki ne yakusa kashe ta, abinda bata taɓa gani ba ko da a mafarki ne wai Brr. Khalil zai kira ta.. katse mata tunanin ta yayi da faɗin
“Baki iya gaisuwa ba?”
Bilkisu da rawan baki tace
“Ina yini?”
“Lafiya, ke fa yakike?”
Tace “lafiya lau”.