Uncategorized

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 11 to 20

*SADAUKARWA*

_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*

“`NAFEESAT

LABARIN DEEBIZAH

JARUMAI

RAYUWATA

NUSNIM

BUTULCI

SO MAI ZAFI.“`

.

     *CHAPTER 25*

      *FEW DAYS*

“My dear kiyi sauri Kar kiyi late kuma?”

Halwa dake cikin ɗaki cikin sanyin murya tace “to Yaya ga ninan”.

Fitowa tayi riƙe da Bairo a hannun ta tana kallon yayan nata, shima kallon ta yake yi cike da tausayin ta, gaba ɗaya duk ta rame sabida zazzaɓin da yasako ta agaba kwana biyu, tayi haske kallo ɗaya zakayi mata kagane sosai take cikin ciwo, itama Mama dake zaune kallon ta tayi tace

“Ni kuwa idan ba yazama dole bane Halwa a fasa zuwa makarantan nan mana, kinga yanda kika yi kuwa? Ba fa sauƙi kika ji ba?”

Kallon Maman tayi kawai tana marairaice fuska kamar zatayi kuka

Nura yace “Mama wannan jarabawan fa tana da muhimmanci tunda na fita ne, haka nan zata lallaɓa tayi har su kammala, kinga jiya ma taje tayi tadawo lafiya, zaki ga sauran ma kamar yanzu ne har an gama”.

“Um um Nura, yau kaduba kagani sosai take jin jiki ko abinci ta kasa ci, ga wahalan da zataje tasha, me zai hana abari wani shekarar sai tarubuta”.

Nura yace “kai Mama har shekara sai tayi ta zama agida? Kema kinsan halinta ba yarda zatayi ba”.

Halwa tace “Mama ki dena maganar nan ma, kuma Ni haka nan zan je in zana jarabawa ta, sai dai in ciwon ya kwantar dani ne amma banga abinda zai hana ni zuwa ba”.

Murmushi Nura yace “to kin ji dai”.

Kaɗa kai Mama kawai tayi tace “ai shikenan Ni dama tausayin ki nake ji, yanzu ku hanzarta kutafi kar lokaci yaƙure”.

Fita suka yi, A mashine ɗin Abokin Nuran yakai ta har cikin makaranta, yasauke ta a bakin ajin su.

Bayan kamar mintuna 20 aka zo raba musu pepper, lokacin ne kuma sosai jikin Halwa yayi tsanani, jikin ta sai kakkarwa yake yi zazzafan zazzaɓi yarufe ta, kasancewar mutum ɗaya-ɗaya ake zama a sit shiyasaka babu wanda ya lura da ita, tana can kusa da baya ajikin bango ta takure waje ɗaya, sai takifa kan ta a table tana hawaye, ita kan ta takasa jure yanayin da take ji, sai da Wani Malami yazo miƙa mata Pepper yakira sunan ta

“Halwa lafiyan ki lau kuwa? Za’a yi jarabawa kina kwance”.

Ahankali taɗago kan ta tana ƙanƙame jikinta, face ɗin ta duk hawaye, kuma sai rawan ɗari take yi

“Subhanallah.. baki da lafiya ne?” Malam ɗin yafaɗa yana kallon ta

Gyaɗa masa kai tayi don takasa magana ma

“To yanzu ya za’a yi kenan? Zaki iya yin jarabawan?”

Shiru tayi bata iya cewa komai ba, su kuma ƴan ajin yawancin su hankalin su na wajen, har da Zainab aciki, duk tausayin Ƙawartan ya kamata, ɗaya daga cikin Malaman dake tsaron su yace

“Ku me kuke kallo ne baza kuyi abinda ke gaban ku ba?”

Sai kowa yamayar da kan sa ƙasa suka soma duba peppern, Malam Isma’il dake can bakin ƙofan yace

“Ai kabar su Malam Kamal, time na cika amsa zamuyi mu wuce”.

Malam Jamilu dake tsaye har yanzu kan Halwa still yace da ita

“Halwa ko dai bazaki iya bane? In ciwon yayi tsanani kije ki amso magani kisha kinji?”.

Cike da ƙarfin hali tace “zan iya Malam”.

“Ok to gashi”.

Aje mata yayi a gaban ta, yaja gefe nan yana kallon ta tare da kula da waɗanda suke wajen, ita kam ahankali tajanyo pepern ta’aza Bairo akai, tayi shiru ta kasa rubuta komi, sai da tayi kusan mintuna 5 kafin tasoma rubuta sunan ta daƙyar, bayan ta gama tasoma amsa Questions ɗin, Number One taɗauka tafara dashi, ahankali tatsayar da hannun ta daga rubutun da take yi tana runtse idanu, wannan karon jikinta sosai yake rawa har da hannun ta, Malam Jamilu dake tsaye yana kallon ta yace

“Gaskiya bazaki iya wannan jarabawan ba, tashi kije kisha magani, inyaso sai asamo wani yarubuta miki”.

“Halwa”. Malam Isma’il da yaƙaraso wajen yakira sunan ta

Zuwa lokacin kuka take yi kan ta a ƙasa ta kasa amsawa

Yace “wai meke damunki ne? Ciwon me kike yi sai a amso miki maganin?”

Still shiru babu amsa sai kukan ta dake daɗa ƙaruwa

Malam Jamilu yace “Zainab taso kije da ita tasha magani”.

Dasauri Zainab tataso tataho wajen tariƙo Halwa dake langaɓe wa, ta rufe fuskarta still tana kuka, suna fita tasoma sheƙa amai kamar zata amayo hanjin cikin ta, sabida babu komi a aman kasancewar bataci abinci ba, nan da nan hankalin Malaman yatashi suka fito waje suna mata sannu

Malam Kamal yace “gaskiya wannan ciwon be kamata abarta anan ba, yakamata amaida ita gida”.

Malam Isma’il yace “Eh haka za’a yi kuwa, tunda nasan gidan su bari inje in kai ta”.

Daga haka yajuya dasauri yanufi inda suke parcking yaburgo mashine ɗin sa yataho wajen, da taimakon Zainab aka ɗaura Halwa akan mashine ɗin, zuwa lokacin duk ta galabaita bata ma iya tsayuwa

Malam Jamilu yace “Zainab kihau bayan ta kuje tare, sai ku dawo tare da Malam Isma’il”.

“To Malam”. Cewar Zainab kenan, kana tahau bayan mashine ɗin

Sai da sukaga tafiyar su kafin Malaman suka koma ciki.

Koda suka isa gida bayan sun sauka, Zainab tariƙo ta suka shiga cikin gidan, Mama na ɗaki tana kwance tajiyo sallaman Zainab, amsa mata tayi tana tashi zaune, ahankali suke tafiya har suka isa bakin ƙofar Maman, Zainab taɗaga musu labule suka shige

“Subhanallah.. lafiya Zainab me yafaru da ita?” Mama tafaɗa tana tashi tsaye cike da ruɗewa

 “Mama wlh jikin ta ne yayi tsanani, shine Malaman sukace adawo da ita gida”.

Mama tariƙo ta tana zaunar da ita saman gadon ta, kana tace

“Dama tunda naga jikin nata da tsanani na san bazata iya taɓuwa komi ba, sai dai taurin kanta ya saka taƙi haƙura, gashi an dawo dake ai”.

Zainab tace “Mama bari inje, Allah yaƙara lafiya”.

“Ameen ameen Zainab, mungode kinji?”

Zainab na fita, Mama tazauna gefen gadon tana kallon Halwa da har yanzu take rawan sanyi tana kuka tace

“Yanzu kuma da ina da ina yake miki ciwo inje nasiyo miki magani? Kamar ma amai kika yi ko? Don gashi duk kin ɓata Hijabin ki”.

Tana sauke maganar ta Halwan tasoma kwarara wani aman daga kwance, dasauri Mama tariƙe ta ganin zata faɗo daga kan gadon, sai da tagama aman kafin tasake ta tana faɗin

“Oh Ni Hauwa, gaskiya ban ga tazama ba dole muje asibiti, tashi tashi muje kiwanke jikin ki mutafi asibiti, Allah dai yabaki lafiya ƴar nan, wannan ciwo haka”.

Da taimakon Maman suka fito waje, taje taɗibo ruwa a botiki ta’ajiye a gaban ta, ita da kan ta Maman taɗauraye mata jikin takaita har ɗaki, kana tazaɓo mata wasu riga da wando na Pakistan, rigan Light and Dack Orange ???? colour ne, sai wandon kuma dack orange ne da ɗankwalin

“Gashinan ki saka, bari inzo”. Mama tafaɗa tana ficewa

Ahankali Halwan tatashi tasaka kayan, sannan tasanya ƙaramin Hijab Baƙi tafito, itama Mama lokacin ta sanyo Hijabin ta suka fice.

Lokacin da suka isa asibiti minti goma suka ɗauka kafin sukaga likita, bayan sun shiga office ɗin sun zauna ne Doctor ɗin yasoma mata tambayoyi tana amsa mishi, har sanda yagama sannan yakira Wata Nurse yace “taje da ita tayi mata gwaje-gwaje”. Bayan kamar mintuna 20 sai gashi sun dawo tare da Nurse ɗin, sakamakon Nurse tabashi sannan tafice, bayan ya amsa ya gani yayi rubuce-rubuce sannan yaɗago yana kallon su

“Am Mama.. a binciken da mukayi mata, sakamakon ya ba mu tana ɗauke da ciki har na wata ɗaya da sati, kuma sannan..” 

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un Ci..Cikiii?”.

Mama tafaɗa da ƙarfi tana kallon Likitan da shima yadakata yana zuba mata nashi idanun

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button