Uncategorized

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 11 to 20

“Dan Allah kidena kukan nan karki sa Mama tafahimci wani abu daga gare ki, bansan me zance mata ba”.

Gyaɗa kanta tayi tana saka hannu tasoma share hawayen ta, still kuma wasu na tsiyayowa, Nura yasoma shiga yaleƙa yaji shiru, sai yadawo yariƙo ta suka nufi ɗakinta, a saman katifan ta yazaunar da ita sannan yafita, sai da yataɓa ɗakin Mama yaji shi a kulle, ashe be kula bane labule tasaki takulle ɗakin, koda yatura yaga ƙofan ya buɗe, sai da yaleƙa ko ina yatabbatar babu ita sannan yadawo cikin ɗakin Halwa, tana nan kwance sai kuka take yi, ƙarisowa yayi kusa da ita yakira sunan ta, shiru tayi bata amsa ba

“Kitashi kigyara jikin ki Mama bata nan, Halwa karki sake Mama tafahimci akwai wata matsala atare dake kinji ni ko?”

Kuka tasake fashewa dashi tana ɗaura hannun ta saman fuskarta

“Wai don Allah kukan na menene? Inace duk dan ni kike yi kuma nace zan rufa miki asiri zan aure ki”.

Buɗe idanunta tayi tana kallon shi, sai kuma tarufe idanun taci gaba da kukan ta, sam bazai gane me take ji cikin zuciyarta ba, amma tasan da cewa komi nata ya ƙare, Haris ya gama cutar ta har abada, bazata taɓa yafe mishi ba”.

Miƙewa yayi yana kallon ta yace

“Ni zan fita, kidena kukan nan haka dan Allah, ki saka ma zuciyar ki salama Allah zai saka miki, kinsan baza mu iya faɗa dashi ba ya riga da yafi ƙarfin mu, kibar sa da Allah kinji My Halwa?”

Zuciyarta ne tayi mata sanyi, shiru tayi tana sake lafewa saman katifan sai ajiyan zuciya take yi

“Yauwa my dear dan Allah karki bari Mama tafahimci kinyi kuka bare tasan wani abu na damunki, yanzu bari in fita yanzu zan dawo kinji?”

Gyaɗa masa kai kawai tayi, shi kuma yafice, ahankali taci gaba da kukan ta, tasan da cewa sosai tayi dacen Yaya, wanene zai iya auren ta da wannan tabon cikin rayuwanta? Amma gashi Yayan ta mafi soyuwa cikin ran ta ya amince zai aure ta bayan yasan abun da yasame ta, tabbas yayan ta ya cika masoyin gaskiya, da ko wani namiji zai fahimci cewa ko wace Yarinya da hakan yasame ta ƙaddara ce Allah yarubuto mata, su gane cewa auren ta babban jihadi ne kuma sadaukarwa ne, da mata da yawa da suke kukan baƙin ciki sun dena.

Ji tayi ƙaunar yayan nata na sake ninkuwa cikin ranta

“Allah Sarki Yayana, tabbas kai me ƙaunata ne da bansan ya zanyi ba, wani miji zan aura da zai iya zama dani ahaka? Nagode Yayana ina matuƙar ƙaunar ka, Nagode Nagode sosai da karufa min asiri”.

Tafaɗa maganar afili tana sakin murmushi kamar yayan nata na ganin ta, sai kuma can tafashe da kuka tana cewa

“Allah ya isana mugu azzalumi, bazan taɓa yafe maka ba, insha Allah sai anyi ma yaranka kaima abun da kayi min, mugu azzalumi kawai”.

“Ke da wanene haka kike ta ja mishi Allah ya isa?”

.

_Toooo ???? me zai faru?_

_kuna ganin asirin ta zai rufu kuwa?._

[9/6/2020, 7:14 PM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*

                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*

_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`{{Ɗaya tamkar da Dubu????}}“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuƊahirah*????

         *⚜{{F.W.A????}}*

“`ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH“`

_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._

*SADAUKARWA*

_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*

“`NAFEESAT

LABARIN DEEBIZAH

JARUMAI

RAYUWATA

NUSNIM

BUTULCI

SO MAI ZAFI.“`

.

     *CHAPTER 15*

“Ke da wanene haka kike ta ja mishi Allah ya isa?” Cewar Mama tana bankaɗo labulen

Dasauri taɗaura hannu a saman fuskarta, cikin ruɗewa tace

“Ahm Ma.. Babu kowa”.

“Ya zakice min babu kowa bayan naji da kunnina kina mishi Allah ya’isa, tukunna ma me yayi miki da za’ayi ma yaran shi?”

“Mama wani ne fa yakusa yabige ni, shine sai ƙunduma min zagi yake yi, shine fa abun yanzu yake damuna”.

Guntun tsaki Mama taja tana sakin labulen tace

“Shine ke kuma tunda baki da haƙuri zakizo kina taja mishi Allah ya isa? Allah yashirya ki Halwa, nima da naji ku shiru ne nafice abuna”.

Ɗaki Maman tashige tana ci gaba da surutun ta, yayinda Halwa kuma gyara kwanciyan ta tayi tana sauke ajiyan zuciya cike da fargaba, rufe idanuwanta tayi tana jin wani kukan na sake zuwan mata tuna abun da yafaru da ita yau, wani irin ƙunci da baƙin ciki ne suka tokare mata wuya, take tafashe da kuka tana toshe bakin ta

“Shikenan yau an raba ta da abu mafi daraja ajikinta, wai yau ita ce wannan ƙaddara yasame ta, abinda ko a mafarki bata taɓa tunanin wannan ɓakin ranan zai zo mata ba, ya zatayi da rayuwan ta? Ji take yi kamar takashe kanta duk sanda tatuna yau wani namiji yasanta a ɗiya mace batare da aure ba

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”. Abinda take ta maimaita wa kenan har tasoma jin zuciyarta na mata sanyi.

.

**** **** **** ****

     *WASHE GARI*

          *EGYPT*

Zaune yake saman Three sitter ya harɗe ƙafafunsa yana danna Lapton ɗin sa, takardu ne birjik agaban sa sai faman aiki yake yi, yana sanye cikin fararen kaya masu taushi sosai, wandon Three qweater ne sai Rigan me kamar singlate

Tun jiya da yasauka a ƙasan yake faman aiki babu ƙauƙautawa, bincike sosai yake akan mutumin da yazo don shi amma har yanzu yagaza samun koda bayani ɗaya akan sa, sosai yake cikin damuwa ko lokacin kansa baya dashi, yanzun ma aikin yake yi but tunanin sa na wani wajen daban, wayan sa da tasoma ringing yayi saurin ɗauka domin dama abinda yake jira kenan

“Hellow Poker..”

“Ok.. ok turo min da address ɗin wajen”.

Cire wayan yayi a kunne yariƙe a hannu yana kallon screan ɗin wayan, 1mint sai yaji Message ya shigo, dasauri yabuɗe yaduba sannan yatashi, cikin sauri yasauya kayan sa cikin farar riga me gajeren hannu da blue jeans, sai yaɗaura jaket saman rigan baƙi ne me belt a wajen cikin sa, jaket ɗin me hula ne sai dai be sanya hulan ba iyakan yasaka Combat a ƙafan sa Black, yaɗau wayoyin sa yazuba a aljihu yafito yarufe ɗakin, kasancewar a Hotel ne ɗakin sa yana hawa na uku ne, cikin sauri_sauri yake taka step ɗin har yasauko ƙasa, yana fita yatari taksi yashige suka tafi, a wani haɗaɗɗen club aka sauke sa yafito yabiya me taksi ɗin kuɗin sa kana yamatsa gefe kaɗan yana ƙare ma wajen kallo, tsawon mintuna 5 yaɗauka awajen kafin yajanyo hulan Jaket ɗin ya’aza akan shi yasoma takawa yashige wurin, sosai ciki yake da duhu, mutane ne birjik ciki kowa na sha’anin gaban sa, ba abinda ke tashi aciki sai daddaɗan cool music da aka sanya wasu sai cashewa suke yi, yana shigowa kallon wajen kawai yake yi har ya’isa wani hill chair yazauna yana kallon mutane, tsawon mintoci yana zaune a wajen yana nazarin inda zai ga mutumin da yazo nema, sai kawai yayanke shawaran nufan wasu matasa maza da mata dake zaune gefe can saman wasu haɗaɗɗun kujeru sai kurɓa alcohol suke yi, wata matashiyar budurwa ce taƙariso kusa dashi hannun ta riƙe da cup, kallo ɗaya zaka yi mata kagane irin waɗannan gogaggun karuwan nan ne, skin ɗin ta baƙi ne but ko kaɗan batayi yanayi da ƴan Nigeria ba coz yanayin shiganta da wayewan ta

“Hi”. Tace dashi lokacin da ta’isa gaban shi

Kallon ta yayi sai yaɗauke kan sa dasauri batare da ya amsa mata ba, murmushi tayi tace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button