BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 11 to 20

“Kana son wani abu ne? Naga tun ɗazu kazo kazauna anan kamar kana neman wani ko?”
Gyaɗa mata kai kawai yayi batare da yasake kallon ta ba
“Ok ko zan iya taimaka maka?” Tafaɗi maganar tana kurɓan Juice ɗin dake hannun ta
Shiru yayi kamar bazai ce komi ba sai kuma yace
“Ina son ganin Mr. Jay pitter ne, me wajen nan, ance min in nazo nan zan same shi”.
Murmushi tayi tana gyara gashinta takalle shi dakyau, sai kuma tagirgiza kan ta tana jawo kujera tazauna taci gaba da shan Juice ɗin ta, shiru ne yagibta a tsakanin su har Khalil yana shirin tashi sai yaji muryan ta ya doki kunnin sa
“Meyasaka kake neman sa?”
Ɗan kallon ta yayi sai yakau da kai be ce komi ba, ƙure shi da ido tayi tana wani irin murmushi tace
“Daga Nigeria kake ko? Nima acan nake ai”.
Taƙarike maganar tana kau da kan ta taci gaba da sipping juice ɗin ta kamar ba itace tayi maganar ba, shi kam kallon ta yake kamar me neman wani abu jikinta, mamaki ne kwance acikin ran sa domin ko kaɗan batayi kama da zubin ƴan Nigeria ba, musamman ma da yaga tana mishi turancin kamar tana wani yare, sam ba wani fahimta yake ba, murmushi tasake yi wannan karon da Hausa tayi maganar tace
“Kana mamaki ko? Uhmmm kadena mamaki sabida ni da kake ganina cikakkiyar Bahaushiya ce ƴar Nigeria, Nigrian ma a Kano, sunana Fadila kuma musulma ce ni, but anan ana kira na da baby Dil”.
Ɗago kai yayi sosai yana kallon ta da tsantsan mamaki a face ɗin sa wannan karon, but yaƙi furta komi
“Kafaɗa min meyasaka kakeson ganin Mr. Jay pitter?”
“Meyasa kikeson nafaɗamiki?” Yayi maganar yana kau da kai kanta
“Sabida zan taimaka maka, bazaka taɓa samun shi anan ba, koda zaka kwana kana sintiri ne, wahala kawai zakayi, but Ni kuma zan iya taimaka maka in kaika inda yake”.
Khalil yace “Please kitaimaka min ina son ganin shine sabida wani bincike da nakeson yi”.
Dariya tasaki tana kallon shi cike da sha’awa tace
“Sau da yawa ina ganin irinka suna zuwa nan don neman sa, kuma tun sanda naganka nagane kai ɗan Nigeria ne kuma nasan abinda yakawo ka har kake neman sa”.
Da mamaki Khalil yakalle ta yace
“Taya kika sani”.
Sai da tashanye sauran Juice ɗin ta’ajiye cup ɗin sannan takalle shi tace
“Idan har kana son taimakona to mubar nan wajen, Ni kuma zan faɗamaka duk abinda kakeso kasani, har da wanda ma bakaso”.
Shiru yayi yana nazari kafin yace
“Ok muje to”.
Tashi tayi takalle sa tana kashe mishi idanu, tamatso kusa dashi kaɗan ahankali tace
“Kabari in nafita sai kabiyo bayana”.
Hakan ko akayi, sai da tafice kafin yabiyo bayan ta, daga can nesa yahango ta tsaye tana ware hannayen ta tana yarfe su, wajen ta yanufa yana kallon ta, bata bari yayi magana ba tace
“Kasamar mana taksi mubar nan”.
Sai kuma tasakar masa murmushi tace
“Ko muje musaukin ka”.
Wani irin kallo yayi mata, sai tawaro idanu still tana murmusawa tace
“nan zai fi sirri, coz za’a iya samun matsala ne”.
Jimm yayi kana yace
“Ok”
Daga nan yatare musu taksi suka shiga suka tafi.
[9/10/2020, 11:42 AM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
“`NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.“`
.
*CHAPTER 16*
Lokacin da suka isa cikin ɗakin sa na Hotel ɗin Baby Dil akan sofa tayi wa kan ta matsuguni, taɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tajingina bayan ta da kujeran tana kallon shi, shi kuma Direct cikin Toilet yashige, be jima ba yafito yanemi wuri kan kujera yazauna kana yace da ita
“Ina jinki, Please ina son nasan komi ga mutumin nan”.
Ɗan sakin murmushi tayi still tana kallon shi tace
“Ni kuma zan sanar da kai komi insha Allahu, katambaye ni duk abinda kakeso”.
Gyaɗa mata kai yayi kafin yagyara zaman sa yace
“Akwai wani Alhaji Mubarak da muke Shari’a dashi acan Nigeria, kuma tabbas an tabbatar min da Mr. Jay pitter abokin harƙallan shi ne, don haka nazo bincike kuma ina son nahaɗu dashi”.
Baby Dil tace “tabbas da ka isa wajen shi babu abinda zaka samu, domin Alhaji Mubarak na hannun daman sa ne, kaga kuwa babu abinda zaka samu a wurin sa illa ma kasake jagula abin, kamar yanda nace maka xan sanar da kai komi sabida nasan sirrin su ne, a baya mutane irinka sun zo kamar kai don bincike, wasu ƴan sanda ne wasu kuma lauyoyi ne, but kai bansan menene aikin ka ba?”
“BARRISTER”. Yafaɗa ataƙaice
“Ok Amma tun sanda naganka naji zuciyata ta kwanta da kai sosai shiyasa nazo wajen ka bcoz nima ina buƙatar taimakon ka”.
Shiru tayi tana sauke numfashi, sai kuma tasauke ƙafan ta tahaɗe hannayen ta waje ɗaya tana kallon shi, sannan taci gaba da faɗin
“Zan soma da baka tarihina duk da baka tambaye ni ba but nasan duk abinda kake nema yana da alaƙa da abinda akai min, shekaru 7 kenan da zuwata wannan ƙasan, ko ince aka sai dani a wannan ƙasan, zaka yi mamaki idan nace maka ta sanadiyan maƙocin mu nazo wannan ƙasa, mun kasance mu talakawa ne don haka maƙocin mu yake taimaka mana kasancewar sa me kuɗi, haka kawai watarana yace inxo zai sama mana aiki awani gida, dama abinda muke nema kenan musami aikin da zamu dogara dashi ni da iyayena, kwana biyu da soma zuwana, uban gidan mu yakai ni wani gida, ni dai ban fahimci ko ina ne ba amma akawai ƴan mata irina da yawa don mun kai mu sha biyu, muna ji muna gani akai mana allura wanda bamu fahimci na menene ba, tun daga lokacin hankalin mu yagushe, ashe makocin mu ne yasiyar dani ga mutumin da yasamar min aiki gidan sa, shima kuma yasiyar dani ga wani uban gidan sa”.
Shiru tayi tatsira ma waje ɗaya idanu taci gaba da faɗin
“Wannan alluran da akai mana yagusar mana da hankali, anyi haka ne don su cin ma manifan su akan mu, suna harƙallan sai da coken that’s why suke samun ƴan mata sufarka cikin su azuba musu coken ɗin nan aciki, alluran da ake yi yana da ƙa’ida, yana ɗaukan iya awannin da zai kai mu ƙasan da za’a kai mu ne, don haka lokacin da akai mana hankalin mu gushewa yayi bamu sake sanin inda muke ba sai a wannan ƙasar, sun kawo mu nan an kuma mana aiki an cire mana coken ɗin, sai dai basu bar mu haka ba suka sai damu ga Mr. Jay pitter, mutum ne shi da yake safaran ƴan mata ƙasa-ƙasa wasu kuma yamai dasu karuwan sa don samun kuɗi dasu, acikin waɗanda muka taho tare gaba ɗaya yasiyar dasu a wasu ƙasashe sai ni da wata yabar mu a matsayin karuwan sa, tun sanda natsinci kaina a wannan ƙasa nake kuka ina roƙon su da sumai dani ƙasata, sai dai aikin gama yariga da yagama su mutane ne da basu tsoron Allah, daga farko da sukaga ina musu taurin kai har nayi yunƙurin guduwa haka sukai ta gana min azaba, but duk da haka ban sa ran wataran zan ƙi guduwa ba, sai dai duk wani hanya da yakasance zan bar ƙasar nan sun toshe ta, ataƙaice dai zan faɗa maka babu yanda za’a yi nabar ƙasan nan batare da sanin su ba, haka nahaƙura naci gaba da zama dasu nima har lokacin da nasaba, nima nadawo nagoge azahiri namanta da komawa ta gida, sai dai abaɗini abin na nan araina, aduk sanda natuna da iyayena sai nayi kukan baƙin ciki, ina tunanin awani hali suke na rashina, shiyasaka har yanzu ban fid da raina zan koma ba”.