Uncategorized

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 11 to 20

Muryan ta da yasoma rawa ne yasaka ta yin shiru, sai da tashare hawayen fuskarta kafin taci gaba

“Shi kuma Alhaji Mubarak tare suke harƙalla da Mr. Jay Pitter, yana kawo masa ƴan mata sosai, duk wani aikin da Mr. Jay yake yi tare suke yi dashi, nasan shi sosai domin yana yawan zuwa nan ɗin, kuma insha Allahu duk wani sirrin su zan iya nemo maka inhar kayi alƙawarin zaka mayar dani ƙasata, ina son nakoma gun iyayena, kataimake ni don Allah, sosai naji zuciyata ta aminta da kai”. Taƙarike maganar tana fashewa da kuka

Brr. Khalil kallon ta kawai yake yi cike da tausayin ta, sosai tabashi tausayi kuma yana ji aran sa insha Allahu sai ya taimaka mata, dama wannan daman yake nema wanda zai kawo ƙarshen masu safaran mata, koda iyakan Alhaji Mubarak da mutanen sa yakawar tabbas yasan ba ƙaramin Jihadi yayi ba, ko ba komi za’a rage yawaitan mugaye irin su, ajiyan zuciya yasauke yana tuno Nazeefa

“Yanzu shikenan da itama nan za’a kawo ta? Yarinya ƙarama, kai amma waɗannan mutanen basu da imani, Allah kaɗai yasan iya adadin yaran da suka kawo waɗanda ma basu kai ta ba”.

Numfashi yaɗan ja yana kallon ta yace

“Kiyi shiru Fadila, insha Allahu zan taimaka miki kibar wannan ƙasan, zaki koma ga iyayen ki in Allah ya yarda nayi miki alƙawari”.

Kallon shi tayi da idanuwanta da sukai jazur tayi masa murmushi tace

“Nagode sosai”.

“Babu godiya tsakani na dake, ke dai ki aiwatar da duk abinda zan saka ki”.

Daga nan yasoma bata bayanai akan abinda yakamata tayi masa, sun daɗe suna tattaunawa kafin tatafi, shi kuma tashi yayi yashige toilet yayo wanka tare da ɗauro alwala yafito, shirya wa yayi cikin farar jallabiya da dogon wandon jeans yashimfiɗa sallaya yayi sallah, sannan yamiƙe yaɗau tellphone ɗin dake ɗakin yakira Receptionist yayi odan abinci, yana zama babu jimawa akayi nocking door ɗin yaje yabuɗe ya’amso yadawo yazauna yasoma ci, abincin yake ci sai dai hankalin sa baya wajen yana nazari, wayan sa dake saman gado tasoma ringing hakan yasaka yaɗan kalli wajen kafin yasauke ajiyan zuciya, yamiƙe yanufi inda wayan take yaɗauka, ganin Bro ɗin sa ne babu ɓata lokaci yayi peacking call ɗin yana zama

“Hello My Bro”.

“Hi ɗan ƙanina ya kake?”

Ɓata fuska Khalil yayi yana shafa goshin sa yace

“Bro bana so”.

Dariya Sameer yayi yace

“Sabida me um ɗan ƙanina?”

Shiru yayi yaƙi magana

Still dariya Sameer yasake yi yace

“I’m sorry dama tsokanan ka nake, ai yanzu kai big boy ne tunda kafara aje yara, kasan fa Hakima ta haihu”.

“Dagaske Bro? Yaushe? Me tahaifa?” Yayi masa tambayoyin ajere yana miƙewa yakoma wajen abincin sa

“Yanzu babu daɗewa, ai nayi tunanin Mom tariga ni sanar maka, namiji tahaifa”.

“A’a tun safe da mukai waya bamu sake ba, Allah yaraya shi Yaya, ina fata ni za’a yi wa takwara ko?”

Sameer yace “tabb kai awa?”

“Ni a Dadyn sa, Please Bro kasan munyi alƙawari dani da kai, duk wanda yahaihu cikin mu zamuyi ma junan mu takwara”.

“A’a to ai bance maka na fari ba, ni Dad zan ma takwara sai dai kabari tasake haihuwa lokacin ma kayi naka auren, kaga sai su tashi tare ko?”

Ajiyan zuciya Khalil yayi yace

“Dama haka zakace ai, kafison Dad dani, shikenan sai kayi ta sakawa”.

Dariya Sameer yasaki jin yanda Khalil ɗin yayi maganan cike da shagwaɓa, cikin dariyan yace

“Haba autan Mom Kar kayi fushi tunda nace zan saka, kuma kasan da cewa ni dama na wurin Dad ne, dole na fifita shi akan ka, amma fa ina son ka sosai fa, daga shi sai kai a zuciyata”.

Murmushi Khalil yayi yace

“Uhmm naƙi daɗin bakin, ai dama Mom ta sanar dani kuma yanzu na yarda, yanzu ni dai kagaishe min da me jegon da kyau da kyau tare da My Son”.

“Ok zasu ji, ya aikin naka? Dafatan komi yana tafiya normal?”

“Alhamdulillah Yaya, Ina samun duk abinda naje nema”.

“To Allah yataimaka yabaka Sa’a”.

“Ameen Bro, katura min photon Baby ta WhatsApp in ganshi”.

Sameer yace “ok yanzu kuwa”.

Daga nan sallama suka yi, yaci gaba da cin abincin sa yana latsa wayan sa.

[9/12/2020, 1:32 PM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*

                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*

_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuƊahirah*????

         *F.W.A????/*

“`ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH“`

_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._

*SADAUKARWA*

_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*

“`NAFEESAT

LABARIN DEEBIZAH

JARUMAI

RAYUWATA

NUSNIM

BUTULCI

SO MAI ZAFI.“`

.

      *CHAPTER 17*

      *WASHE GARI*

         *NIGERIA*

Da sallaman ta tashigo gidan, Mama dake zaune tana gyaran lagwani ta’amsa mata tare da faɗin

“A’a maraba da Zainaba”

“Mama ina wuni?”

“Lafiya lau, ya Umman taki?”

“Tana lafiya, tace in gaishe ki”.

“Ina amsawa, ya wajen su Zaituna, ina fata kina leƙata?”.

Murmushi Zainab tayi tace

“Eh Mama ina zuwa sosai”.

“To madallah haka akeso, kishiga ƙawar taki na ciki ai, bata jindaɗi ne”.

“Eyya Allah yasawaƙe, ai bani da labari”.

Mama tace “ameen, ai zazzaɓi ne kuma jiya da dare ne ma jikin yamatsanta mata”.

Cike da tausayin ƙawartan tasake cewa

“Mama Allah yasawaƙe bari in shiga wajen ta”.

“Ameen Zainab”.

Zainab na shiga taga Halwa saman gado ta kwanta tajuya ma ƙofa baya, ƙarisawa tayi kusa da ita tazauna a gefen katifan tana faɗin

“Halwa ya jikin naki?”

Halwa da tarufe idanunta batare da tamotsa ba tace

“Dasauƙi”.

“Allah yabaki lafiya, shine kuma baki kiran awaya kin sanar dani ba? Yanzu da ba don naji Umma tana maganan saka ranan ki jiya ba shikenan bazaki faɗa min ba? Abin yaban mamaki ai ince kina cikin wannan farin ciki nasan da tuni kin garzayo kin fesa min”.

Duk wannan surutun da Zainab take yi Halwa taƙi cewa komi illa jinta da take yi, hannu Zainab ɗin tasaka tataɓa wuyan Halwan tana cewa

“Wai jikin yayi tsanani ne haka da bazaki tashi muyi magana ba?”

Ahankali Halwa tabuɗe idanunta tatashi zaune tana kallon Zainab ɗin, cikin kasala tace

“Wani magana zamuyi?”

Zainab kallon yanda duk tayi wani yaushi idanuwanta sukayi luhu-luhu suka yi ja tayi tace

“Ƙawata me ke damunki ne? Kinga yanda kika koma? Ke da ciwo baya hana ki walwalan ki amma yanzu duk kin wani iri kamar kin daɗe kina ciwo?”

Ɗan dafa kan ta Halwa tayi tace

“Zazzaɓi ne kawai”.

“To Allah yasawaƙe”.

“Amin” Halwa tafaɗa tana komawa takwanta

“Banji daɗi ba ƙawata da baki da lafiya, sai da lokacin farin cikin ki yazo sai kuma gashi ciwo na son hanaki walwalan ki”.

“Inji wa yace miki bana farin ciki?” Cewar Halwan tana ƙirkiro murmushi

“Hmm kowa yagan ki yasan da cewa sosai kina jin jiki Halwa, ciwon kwana ɗaya ya maidake haka, nasan da cewa da bakya jin jiki tabbas bazaki kwanta haka ba, ƙafan ki babu inda bazai zagaya wajen sanar da cewa an sanya miki ranan aure ba”.

Halwa hararanta tayi tace

“Tunda an ce miki bani da kunya ko?”

Dariya Zainab tayi tace

“Anan kam ai nasan baki da kunya, zakiyi abinda yafi hakan ma”.

“Ke dai kika sani”. Halwa tace hakan tana ɗaura hannu asaman goshinta

“Yauwa ya maganar Assignment ɗin nan na Malam Isma’il? Kinsan yace “shine Test ɗin mu, kuma wlh na duba nawa bangani ba, ara min naki in kwafe Questions ɗin”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button