Uncategorized

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 11 to 20

“Kiduba jaka na kiɗauka nima banyi ba, kije dashi kiyimin don Allah”.

Miƙewa Zainab tayi tana faɗin

“Ok ba damuwa”.

Inda take rataye School bag ɗin tanufa taciro, taduba littafin taɗauko tadawo tazauna tace

“Ni zan tafi gida Umma na can tana jirana zataje anguwa, amma goben zakije school ɗin? Don naga jikinki ya matsanta miki”

“Zani”.

“Tom sai muhaɗe acan kenan, ina Yaya Nura? gashi zan tafi ban mishi Allah yasanya alkhairi ba”.

Halwa tace “ki neme sa a waya mana, ko kin ban ajiyar sa?”.

“To ai naga kece Gimbiyar tasa wataƙil kinsan inda yake, kinga ni ba jan magana zan yi ba na tafi”.

Fita Zainab tayi tayima Mama sallama tatafi.

***** ***** ******

Kwance take saman gadonta ta ɗaura hannayen ta saman fuskarta, babu abinda take tunani sai Khalil, tun sanda yakawo ta gidan nan har tafiyan shi takasa samun sukuni, kullum dashi take kwana kuma dashi take tashi, tarasa meyasaka tunanin sa yake damunta kullum, kuma ta kasa gane takamaiman abinda take ji acikin ranta game dashi, tsananin kewar sa ne yake damunta ako da yaushe, burin ta kawai yanzu tasanya shi a idanunta ko ta sami sauƙin zuciyarta, ahankali tamiƙe zaune tana ƙura ma waje ɗaya idanu, can tasaki ajiyan zuciya tatashi tsaye tasanya room slippers tanufi ƙofa, tafiya take yi ahankali tana saukowa daga upstairs, tun sanda takusa saukowa tahango Mom zaune a parlour tana waya, har takusa isa kuma sai tajuya da ninyan komawa Mom takira ta

“Ina zakije kuma Nazeefa? Zo ga yayan ki kugaisa”.

Jiki a sanyaye tajuyo tazo wajen Mom tana jin zuciyarta cike da farin ciki, amsan wayan tayi bayan da tazauna takara a kunne tana faɗin

“Hello Yaya”.

“Nazeefa”. Yakira sunan ahankali cike da salo

Hakan yasaka Nazeefa lumshe idanuwanta cikin jindaɗin muryan sa da yaratsa mata har cikin kwanya tace

“Ina wuni Yaya”.

“Lafiya lau, ya jikin ki? Dafatan kina shan maganin ki akan ƙa’ida?”.

Gyaɗa masa kai tayi kamar yana kallon ta, sai kuma tace

“Eh ina sha”.

“Ok kici gaba da kulawa”.

Shiru ne yagibta, hakan yasaka Nazeefa taɗan saci kallon Mom taga hankalinta na kan t.v, sai tace

“Yaya yaushe zaka dawo?”

Shi da har yai tunanin ko ta ba Mom ne still yaji muryan ta tana tambayan shi

“Kina so in dawo ne? Yatambaye ta cike da kulawa

“Eh Yaya nayi kewarka ne sosai”.

Tafaɗi maganar ahankali, don ita kanta batasan sanda tafaɗa ba, umarnin zuciyarta kawai tabi

Shi kam Khalil jin maganar yayi wani iri a zuciyar sa, sai kuma yashare tunanin da yakawo mishi rai yace

“Very soon zaki ganni, miƙa ma Mom wayan”.

Ba musu tacire wayan a kunni tamiƙa ma Mom, waya suka ci gaba da yi ita kuma Nazeefa tana zaune tana sauraron su, duk da bata jin muryan Khalil ɗin but sai sakin murmushi take yi kamar an mata bushara, tunanin ta kawai yatafi wajen tuno kyakykyawar fuskar sa ne, tana jin wani iri sosai a game dashi musamman ma duk sanda zasu haɗa idanu sai taji gaban ta ya faɗi, ko kuma da zaran ta gan shi hakan ke faruwa da ita, sai dai ita batasan menene ba bare tace ga matsayin abinda take ji, sai dai tasan shi ɗin wani haske ne a rayuwanta, me haskaka mata duk wani baƙin duhun dake cikin rayuwanta, kuma Mai Taimakon rayuwanta.

_Shin zaku iya faɗamata abinda ke damunta Fan’s? Don nasan kun sani ai._

~Khalil-Billy~

       ~Khalil-Lubna~

~Khalil-Nazeefa~

_Muje zuwa Fan’s_

_karku manta ku suburɓuro comments fa._

[9/15/2020, 11:32 AM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*

                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*

_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuƊahirah*????

         *F.W.A????/*

“`ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH“`

_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._

*SADAUKARWA*

_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*

“`NAFEESAT

LABARIN DEEBIZAH

JARUMAI

RAYUWATA

NUSNIM

BUTULCI

SO MAI ZAFI.“`

~Khalil-Billy~

       ~Khalil-Lubna~

~Khalil-Nazeefa~

.

   *CHAPTER 18*

     *TOMORROW*

         *MONDAY MORNING*

Halwa ce tsaye cikin ɗakin ta tana riƙe da Hijab ahannu, kayan makaranta ne ajikin ta da tagama sakawa, tanufi wajen jakan ta dake rataye taciro tasaƙala shi a kafaɗa sannan tasanya Hijab ɗin tafito waje, leƙa ɗakin Mama tayi dake zaune tana cin tuwo tace

“Mama ni na tafi sai na dawo”.

“To uban wa kika bar ma abin karyawan naki?”

Yamutsa fuska tayi da yazame mata jiki tace

“Mama ni nayi latti banda lokacin cin abinci”.

Harara Mama tawurgo mata tace

“Tunda an faɗi maƙiyin ki ai dole kice kinyi latti, kizo kizauna kici tun kafin in saɓa miki, ayi mutum sam baya son cin abinci? Rayuwan zata yiwun miki ahaka ne? Nura dai zai yi aiki wlh”.

Buga ƙafa Halwa tayi cike da shagwaɓa tace

“Ni wlh Mama bazan iya cin tuwon nan ba, ki ƙyale ni kawai natafi”.

“Wlh kuwa in bakizo kinci ba sai dai kifasa zuwa makarantan nan, shegiyar yarinya me taurin kai”.

Fuska a kumbure Halwa tashiga cikin ɗakin tawafci kwanon tuwon dake ajiye agefe zata fita

“Dan ubanki dawo nan, zauna kici anan don nasan in dai kika fita sai dai kizubar”.

Babu musu takoma tazauna, sai dai gaba ɗaya in kakalli fuskarta zaka gane ranta aɓace yake, haka tatsulma hannu tasoma kai abincin baki tana yamutsa fuska kamar tana cin kashi, Mama kam bata ƙara bi takanta ba taci gaba da cin tuwon ta duk tana ankare da ita, ganin tana yunƙurin yin mata amai a ɗaki ne tace

“Wlh Halwa idan har kikai min amai a ɗaki sai na mugun saɓa miki”.

Gyaran murya Baba dake bakin ƙofa yayi yace

“Wai menene haka kika tasa yarinya gaba kina ta mata faɗa?”

“Kaima kasan halinta tunda an haɗa ta da abokin gaban ta, makaranta zata tafi bataci komi ba”.

Murmushi Baba yayi yace

“Kiriƙa lallaɓa ta mana Hauwa, kinji tashi kije ɗakina akwai raguwan ƙosai da narage kiɗauka kitafi dashi”.

Miƙewa tayi kamar zatayi kuka ta cika bakinta da tuwo amma takasa haɗiye wa

“Ungo nan riƙe wannan kiƙara ki sayi wani abun kici”.

Amsan kuɗin tayi tafice dasauri, ɗakin Baban tashiga taɗauko ƙosan tafito, sai da tazubar da tuwon dake bakin ta tukunna takuskure bakin tafice dasauri, akan hanya suka haɗu da Zainab

“Ai da naji shiru baki biyo min ba nace bari in zo in duba Madam ɗin nan lafiya?” Cewar Zainab kenan

Yamutsa fuska Halwa tayi tace

“Ƙalau, Mama tatare ni dole sai na karya sannan zan fita”.

Dariya Zainab tayi tace

“Ke dai har yanzu bazaki dena wannan halin naki ba sai kace ƙaramar yarinya, kullum sai kin saka Mama ta ɗaga murya akan cin abinci, Allah yakyauta miki, Yaya Nura dai zai yi aiki wlh”.

“Uhm itama haka tagama cewa, ko wani aiki zai yi oho?”

Zainab tace “ai da gaskiyar Mama, kullum wajen cin abinci zai yi fama dake”.

Taɓe baki kawai Halwa tayi bata sake cewa komi ba, ita kuma Zainab sai mata hira take har suka kai bakin titi suka tari abin hawa

Bayan sun kai suka sauka Halwa taciro Hamsin tamiƙa, ita kuma Zainab tajuya da ninyan tafiya Halwa tariƙo ta tana faɗin

“To uwar son banza ai ban bada da naki ba, sai ki biya sa”.

Kuɗin taciro cikin jaka tamiƙa mishi suka juya suka tafi

Zainab tace “wlh ke ƴar wulaƙanci ne Halwa, nima zan rama”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button